Ko aikin dare hadari ne a wurinka?

Wace irin illa aiki da daddare yake yi wa jiki da kwakwalwa? Claudia Hammond ta bincika.

A tsarin wasu ayyukan ba ta yadda mutum zai kauce wa zuwa aiki da daddare.

Akwai aikin asibiti da tukin jirgin sama ga kuma kantina da ke sayar da kayayyaki duk tsawon dare yayin da harkokin mutane ke sauyawa zuwa wani yanayi na ba dare ba rana.

Ida aka yi kyakkyawan tsari da kuma dan hutu da rana za a iya aikin dare a kuma samu damar barcin sa'a takwas bayan aikin ba tare da wata matsala ba.

Wasu mutanen ma za su gaya maka cewa ba su damu ba, sun saba aiki a irin wannan yanayi da tsari.

To amma anya jikinsu zai iya sabawa da yanayin da za a ce an sauya lokacin barci ya koma na iki, kuma na aiki ya koma na barci? Kuma ma, wani abin ji shi ne, ko aikin dare yana yi wa lafiyarka illa?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Bincike ya nuna ba jikin kowa ba ne zai iya juyawa ya saba da aikin dare

Akwai abubuwa biyu a kan wadannan tambayoyi. Daya ita ce kan yadda kwakwalwarmu za ta ji. MUtane za su iya cewa sun saba da aikin karba-karba da ake yi a lokacin dare da kuma rana. Akwai shedar da ke nuna cewa muna sabawa da aikin dare idan muka yi nisa da shi fiye da a lokacin da muka fara yinsa, amma kuma wasu mutanen ba sa jin dadinsa kamar wasu.

Wani bincike da aka yi a kasar Canada, ya yi nazari kan lokacin kwanciya da kuma yawan kwayoyin halittar da ke sa barci da jiki yake fitarwa a kan wasu 'yan sanda a lokacin da suka shiga makonsu na aikin dare.

Yawanci jikinmu yana fitar da kwayoyin halittar da ke sa barci ne can da almuru lokacin muka fara jin gajiya muna son barci.

Idan ka saba sosai da aikin dare, lokacin fitar da sinadarin da ke sa barcin sai shi ma ya sauya zuwa safe maimakon da al'muru ko dare.

A wannan binciken an gano cewa wadanda jikinsu ya yi wannan sauyi sun fi farin ciki da kuma kuzari. Sai dai kashi 40 cikin dari ne kawai jikinsu ya iya yin wannann sauyi.

A wani binciken da aka yi babba, wanda ya kunshi 'yan sanda sama da 3,000 da suke aikin daren a Canada da Amurka, an ga illar da ta samu wadanda jikinsu ya kasa sauyawa, inda kashi 40 cikin dari daga cikinsu suka gamu da wata matsalar da ta shafi barci.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Idan dare ya yi mutum ya kan rasa abinci sai dai ya nemi na ko-ta-kwana

Ko da ba ka jin wata matsala, harwayau akwai maganar cewa ko jikinka zai iya gamuwa da wata matsala a can gaba.

Idan ana maganar duba illar zahiri a jikin mutum, daya daga cikin matsalolin ita ce, yadda za ka iya bambanta tsakanin tasirin da aikin karba-karbar zai iya yi wa yanayin tafiyar da rayuwarka (life style) da ainahin tasirin da aikin daren yake yi maka.

Abu ne mai wuya ka iya cin abinci yadda ya kamat ko ka rika motsa jikinka a kai a akai idan kana aikin dare.

Bayan wahalar samun nau'in abinci kamar salad da daddare, ba kuma lalle ba ne cewa shi kake so domin ka iya zama ba ka yi barci ba.

Wannan shi ke sa mutane sayen 'yan kayan abinci na kwalama ko na gaggawa.

Za ka iya cin su Pizza da Shawarma ka koshi, to amma cinsu yau da gobe ba abu ne mai kyau ba sosai ga lafiyarka. Kuma ga shi ba ka da dama sosai ta zuwa motsa jiki.

Idan aikin rana kake za ka iya kukutawa bayan ka taso daga aikin ka je ka motsa jiki, to amma idan na dare kake, baza ka iya zuwa ba domin a lokacin gyangadi ma ya fara daukarka.

Bincike ya nuna cewa matukan jiragen sama sun fi farin ciki a ranakun da suke hutu idan aka kwatanta da ranakun da suke aikin dare.

Masu binciken sun kuma gano cewa idan matuka jirgin suka yi aikin na dare jikinsu yana samun sinadarin da ya shafi gajiya idan ba su yi barci ba kuma jikin zai yi ta samar da wannan sinadari tsawon wannan rana.

Idan tafiya ta yi tafiya kuma ana ganin yawan sinadarin zai iya kara hadarin matsalar zuciya da kuma hawan jini.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Akwai kuma wasu matsalolin da ke tattare da ikin dare.Wani nazarin kuma ya nuna cewa aikin dare na rana daya zai iya kara bugun jininka.

Idan ka hada duka wadannan da kuma binciken da aka yi a Jami'ar Surrey, wanda aka wallafa a farkon shekara ta 2014, wanda ya nuna cewa bayan aikin dare na kwana uku, an rikita

tsarin aikin kwayoyin halittar mutum,abin da ke nufin lokacin aikinsu zai koma wani lokaci da bai dace ba na rana, za ka ga matsayin lamarin.

Wani binciken na daban kuma ya gano cewa, bayan mako biyar mutanen da ba su yi barci ba da daddare kuma suka yi barci da rana, ana ganin matsala a yawan sukarin jikinsu da kuma

sauyi a tsarin aikin jikin, wanda hakan zai iya kara musu hadarin kamuwa da cutar sukari (nau'in ta biyu wato type 2 diabetes) da kuma kiba a can gaba.

Ba shakka duka wadannan bincike ne na gajeren lokaci, wanda hakan ke sa yuwuwar cewa watakila, jikin mutum ya sauya, ya komo daidai, a can gaba bayan wani dogon lokaci, amma

duk da haka nazarin da aka yi kan annoba a shekaru da dama ba abu ne mai karfafa gwiwa ba akan lamarin.

Akwai muhawara da yawa da aka yi a kan tasirin aikin dare a kan cutar bugun zuciya, inda bincike da dama ya nuna yana kara hadarin cutar, wasu kadan kuma suka ce a'a.

Ko da mutum ya sauya yadda yake tafiyar da rayuwarsa, idan dai yana ikin dare to yana tattare da hadari sosai.

Bincike da dama ya nuna ba ko wane mutum ba ne jikinsa yake iya sauyawa idan ya koma ikin dare.

Idan na maganar aikin jiki ne, tsarin tafiyar da rayuwar mutum na yau da kullum yana iya sa mutum ya kaucewa wannan hadari ko akalla ya rage.

Ko da mutum yana aikin dare,muddin yana samu ya motsa jikinsa yadda ya kamata yana cin abinci mai kyau kuma yadda ya dace sannan ba ya shan taba, ko da ba ya samun lokaci na

shakatawa ta walwala da jama'a, shedar gamuwarsa da wadannan matsaloli kadan ce.

Hakkin mallakar hoto Tom Lord

Akwai kuma hadarin kamuwa da cutar sankarar nono ga wadanda suke aikin dare musamman a kan wadanda suke tashi daga barci da sassafe amma kuma su kai tsawon

dare ba su yi barci ba(wato masu barci dan kadan).

Abin da duk wanna bincike zai iya gaya man shi ne wadanna mutane ne wannan matsala za ta iya shafa.

Ko kuma abin nan ne kamar yadda binciken na gajeren lokaci ya nuna, wanda ya ce wasu mutanen jikinsu zai iya juyawa ya dace da duk lokacin da aikinsu ya koma, wadnda ba za su

gamu da wata matsala ta tsawon lokaci ba? Ko kuma akwai hadari ne ga duk wanda yake aikin dare?

Yawan ire-iren aikin daren da mutane suke yi ya rikita binciken da masana ke yi. Tasirin yawan aikin dare a kai a kai a jikin mutum, daban yake da wanda mutum yana aikin safe kwatsam

ya koma aikin dare a lokaci daya kuma ya yi kwanaki da yawa a sati yana yi.

Duk da haka dai , sai mun kara samun ilimi a kan ainahin wanda yake tattare da hadari, masu aikin dare za su iya taimaka wa kansu idan ba su yi sake da duk wata dama ta cin abinci mai

kyau da lafiya ba yadda ya dace da motsa jiki da kuma lura da alamar wadannan cutuka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Is working at night bad for you?