Wayar Salula ce madogarar ilimi a Afrika

Hakkin mallakar hoto z

Kwararre a kan hanyar koyar da ilimi ta waya na Majalisar dinkin duniya, Steve Voslo, yana ganin wayar salula ce za ta iya zama madogarar ilimi a Afrika:

''Tsarin ilimi na cikin wani mawuyacin hali. Wannan matsala ce da ake fama da ita a sassan duniya da dama, amma ta fi kamari a Afrika.

A kasashen Afrika da ke kudu da hamadar Sahara, yara miliyan goma ne suke ficewa daga makarantar framare a duk shekara.

Su kansu wadanda ma suka samu damar tsayawa har su gama makarantar ingancin ilimin nasu kasa yake sosai fiye da yadda ake tsammani.

Bugu da kari akwai kuma babbar matsala ta karancin kwararrun malamai masu kishin aikin koyarwar.

An yi kiyasin cewa idan har ana son kowane yaro ya samu ingantaccen ilimi a kasashen Afrika na kudu da hamadar Sahara zuwa wannan shekara ta 2015 da muke ciki, Afrika na bukatar daukar sabbin malamai 350,000 a kowace shekara, wanda wannan abu ne mai wuya.

Ka duba inda aka fi yawan manyan da ba su da ilimi a duniya, daga nan za ka fara fahimtar girman matsalar.

Sakamakon wadannan matsaloli, a shekaru goma da suka wuce kasashen Afrika da yawa sun yunkuro har suka samu dan cigaba wajen bunkasa ilimin.

Amma fa tafiyar kamar ba a fara ba, domin matsalar ba karama ba ce, kalubalen na da girma sosai.

Tsarin da aka saba bi na jarraba hanyoyin farfado da ilimin bai isa ba.

Duk da haka akwai mafita:

Yayin da ilimi yake fadi tashin farfadowa, hanyar sadarwa ta wayar salula ta bunkasa fiye da yadda ake tsammani.

A yau Afrika ita ce kasuwar salula da ta fi bunkasa kuma ta biyu a duniya.

Yayin da kuma yawan layukan wayoyin salula a wasu kasashen da suka hada da Botswana da Gabon da kuma Namibia, suka fi yawan mutanen kasar. Afrikan kuma ita ce koma-baya wurin shiga duk wata kasuwar wayar salula ta duniya.

Akwai karin cigaba da dama da zai zo. Layukan wayar salula sama da miliyan 620 da ake da su a Afrikan na nufin a karon farko a tarihin nahiyar, mutanenta sun shigo dandalin cigaba.

Wannan dandali da suka hau na duniya na matattarar wayar salula inda kowanne daga cikinsu zai iya saduwa da kowa da kuma wasu na sassan duniya, dama ce ta samun ilimi.

Hakkin mallakar hoto

Tuni har mun fara ganin sauyi. Sabbin abubuwa da hanyoyi, wasu manya wasu kanana suna amfani da fasahar sadarwa ta zamani ta waya wajen rarraba kayan karatu da taimaka wa wajen farfado da al'adar karatu tare kuma da samar da damar koyo tsakanin abokan karatu da kuma koyon karatu daga wajen makaranta ta waya.

Wadannan hanyoyi na sadarwar waya suna kawo sauki a harkar gudanar da ilimi da inganta sadarwa tsakanin makarantu da malamai da kuma iyaye.

Amfanin ba shi da iyaka. Koyo ta hanyar salula, ko mutum shi kadai ne, ko ta hanyoyin da aka saba yana taimakawa da kuma fadada ilimi da ciyar da shi gaba ta hanyoyin da ba za ta yuwu ba kafin yanzu.

A yau miliyoyin 'yan Afrika suna yawancin karatu da rubutunsu ne na yau da kullum ta wayarsu ta salula ta hanyar rubutun tes(sms) ko sakon kar-ta-kwana (IM).

Ana kuma kara samun cigaba wajen amfani da waya, a samu damar karanta littattafai da jaridu da kasidu da makamatansu ba wai dan rubutun da bai wuce haruffa 160 ba.

Ba karanta littattafan da kasidu ba kadai ta wannan hanya, su kansu masu karatun suna da damar bayyana ra'ayinsu.

Wata daga cikin hanyoyin da matasa suke samun wannan dama ta karanta littattafai na labarai ta waya ita ce Yoza, wadda ta samu karbuwa a wurin matasan Afrika.

A watanni 18 na samuwar wannan kafa, an karance littattafanta da sauran labarai da wakoki har 470,000 da kuma samun ra'ayin jama'a 47,000.

Haka ita makungiyar bunkasa harkokin karatu ta Worldreader, tun kafuwarta a 2010, ta samar wa yara 'yan makaranta a kasashe masu tasowa da dama hanyoyin karanta littattafai ta intanet.

A kwanan nan kuma ta fara wallafa littattafai ta hanyoyin wayar salula da ake kira e-reader. Manhajar kungiyar ta Worldreader da kuma dakinta na karatun labarai tuni suna kan wayoyi miliyan uku da dubu 900, inda take da masu amfani da ita daga Najeriya da Ethiopia da Ghana da sauransu.

A kasashe da dama, intanet ko wayar salula ita ce hanya daya tilo ta rarraba littattafai da mujallau da sauran abubuwan karatu ba tare da wata matsala ba, idan aka yi la'akari da tsadar littattafai da kuma raba su, musamman a yankuna na karkara.

Karatu a kan waya yana da bambanci da karatu da littafi:

Hanyoyin zamani suna ba wa mutum dama ta musayar ra'ayi, inda masu karatu za su iya bayyana ra'ayinsu a kan abin da suka karanta, sannan suna bayar da damar muhawara da sauran masu karatu da yin tambaya da kuma samun tallafi ko taimako a kan karatun, ko da wani abu ya shige wa mai karatu duhu.

Duk da cewa littattafai suna da nasu muhimmancin, kamar rashin batir, wato ba ruwanka da maganar wani batir da sai ka yi masa caji.

Yana da kyau a gano hanyoyin da kowane tsari yake da muhimmanci ko ya fi karfi tsakanin littafin na waya da kuma na takarda domin kara karfafa cigaban koyon ilimi.

Shafukan sada zumunta da muhawara da yawancin 'yan Afrika suke samu ta waya da dangin wayar, suna ci gaba da karuwa kuma suna kara samar da damar bunkasa ilimi.

Tuni malamai da dalibai suke amfani da su ta hanyar musayar bayanai, tare kuma da samar da tallafi ta hanyar tattaunawa ta intanet ko ta waya.

Ga al'ummomin da suke warwatse, ba sa iya saduwa da juna gaba da gaba, amfanin irin wadannan hanyoyi na zamani ba zai misaltu ba.

Mxit shi ne babban dandalin sada zumunta da muhawara na Afrika, inda yake da masu mu'amulla da shi sama da miliyan 50. Shafin wanda aka samar a Afrika ta Kudu, ba kawai yana sada zumunta tsakanin masu mu'amulla da shi ba ne wadanda yawancinsu matasa ne, yana kuma taimaka wa wajen koyar da darasin lissafi.

Dr Maths, da ke shafin na Mxit ya taimaka wa 'yan makaranta 30,000 a ayyukansu na lissafi wajen hada su da malaman lissafi ta intanet din su taimaka musu kan wani aiki.

Tsarin yana da kyau saboda abubuwa biyu, na farko yana da sauki, domin ainahin abin da yake yi kyauta ne amma masu shigar suna biyan dan kudin da ba shi da yawa, ga kamfanin wayar da suke amfani da shi wajen samun layin intanet din.

Haka kuma yana aiki da yamma a lokacin da 'yan makaranta ke bukatar taimako a aikin da aka ba su a makaranta su yi a gida.

Ba shakka, babu ta yadda za a samu tsari daya da zai wadatar da kowa. Tsarin intanet ko sadarwar wayar salula a Afrika ya warwatsu ne daban daban a fadin kasashe 56, inda wasu suke da sadarwa mai kyau wasu kuwa ba ta da karfi.

Idan ana son ganin wannan hanya ta zamani ta yi tasiri sosai, dole ne a tashi tsaye a inganta fasahar sadarwar.

Misali kamar Nokia Life, wanda tsari ne da yake da masu mu'amulla da shi sama da miliyan 70 a India da China da Indonesia da kuma Najeriya.

Fitattun kafofin yada bayanai a Najeriya na intanet, suna bai wa 'yan makaranta darasi ko sanar da su hanyoyin yadda za su yi jarrabawa da bayani kan ilimin da ya shafi lafiya domin iyali da kuma koyar da Turanci.

Tsarin yana amfani da sakon tes(text ko sms ) ne, wanda ba sai da intanet ba.

To amma fa ba wai wanzuwar irin wadannan hanyoyi ba ne kawai, idan har ana son ganin tasirinsu muna bukatar sake tunani a kan me muke nufi da ilimi, da makaranta da kuma wana irin ilimi ko kwarewa suke samarwa.

Kwanannan wani kwamiti na Majalisar dinkin duniya da hukumar ilimi da kimiyya da kuma al'adu ta majalisar ,UNESCO, ya samar da wani rahoto a kan ilimi da kwarewa a kan wata sana'a bayan shekara ta 2015.

Rahoton ya nuna yadda za a samu sauyi bayan wannan shekara, inda alamu suka nuna za a kauce wa tsarin koyarwa a aji, a mayar da hankali wajen hanyoyin koyo da ake yi na rayuwar jama'a ta yau ta kullum.

A nan ake ganin amfanin sadarwar waya zai yi tasiri , domin sadarwa ce da ke bayar da dama ko taimaka wa koyo a ko ina a ko wane lokaci, saboda mutum ya mallaki wayar, kuma ko da yaushe wayar na nan na kusa da shi.

Rahoton ya kuma yi hasashen cewa za a sami raguwar tarnaki ko iyaka tsakanin koyo da aiki da kuma tafiyar da rayuwa(wato kusan za ka iya tafiyar da duka wadannan abubuwa a lokaci daya)

Daman tuni wayar salula ke taimakawa wajen koyawa mutane sana'o'i a fannoni da dama da suka hada da aikin gona da lafiya da sauransu.

Bayan bunkasa hanyoyin ilimi na al'ada da aka saba na koyar da karatu da rubutu da lissafi, rahoton ya kuma ce, akwai bukatar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta zamani ta yadda mutane za su sami kwarewa a fannin mua'mulla da sauran fannonin ilimi da ake yi ta intanet.

Ta hanyar jagorancin malamai, sadarwar waya za ta bayar da damar koya wa miliyoyin 'yan Afrika wadanda suke mu'amulla da intanet ko waya.

A nahiyar da ilimi yake sauyawa, me za a rika koyarwa, kuma ta yaya za a koyar da shi da kuma yadda za a rika nazarin cigaban da aka samu daga wannan ilimi da ake koyarwa.

Kuma a wannan nahiya da koyo ya zama dole ga waya tana da sauki tana kuma hada mutane su koyar da juna da kuma yada bayanai fiye da yadda abin yake a da, idan aka duba wannan duka, za a ga, ba karamin cigaba za a samu a nahiyar ba a nan gaba.

Wayar salula ta sami gindin zama a nahiyar Afrika kuma za ta ci gaba da tasiri da habaka ilimi.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The future of education in Africa is mobile