Ka'idojin barci mai dadi.

Wasu abubuwan da mutum ya gamu da su ko yanayi da ya taba shiga abubuwa ne na tayar da hankali kamar rashin barci.

A zahiri barci shi ne aiki a duniyar nan da mutum zai yi ba tare da wata wahala ba, to amma duk da haka wasunmu suna fama da matsalar kasa barci (rashin barci).

Wani abin kara ta da hankalin kuma shi ne a yanzu, lokaci ko sa'o'in da kake yi kana barci suna da muhimmanci ga lafiyar jiki da kwakwalwarka kamar lokacin da kake tafiya da magana da kuma cin abinci.

Barci mai kyau zai iya taimakawa wajen kyautata yanayinka, da sa maka natsuwa da karfafa tunaninka, yayin da larurori irin su cutar sukari ake danganta su da mutanen da suke fadi tashin samun isasshen barci.

Tunanin yadda za ka iya samun barci mai dadi shi kadai zai iya sa, ka kasa more hutu ko dadin barcin, wanda hakan ke sa mu nemi wasu hanyoyi na samun barcin mai dadi.

To amma maganar ita ce, me yake aiki kuma menene ba ya aiki wajen biya mana wannan bukata?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ka da ka sha kofi ko gahawa da daddare

Barin shan gahawa shawara ce mai kyau, to amma ba wai sai ka takura kanka ka yi hakan ba a lokaci daya idan ta zama jiki a wurinka.

Idan tun da rana ka sha gahawarka ta karshe, to watakila zuwa karfe 11 na dare yawancinta ta riga ta fice daga jikinka.

Ko da ike yana da kyau ka kauce wa shan gahawa ko shayi sa'a shida kafin ka kwanta, domin ka samu damar yin barci cikin sauki, abin da ba mu sani zuwa yanzu, shi ne ko akwai wani amfani da barin shansu a bayan wannan lokaci.

Kuma wani abin da yakamata a sani shi ne, ba kowa ba ne kofi ko gahawa suke tasiri a jikinsa.

A nan ke nan ya danganta da abin da yake tasiri a jikin mutum wajen hana shi barci.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ka rika rubuta abubuwan da kake yi kafin lokacin barci

Rage yawan shan barasa (ga wanda yake sha) da motsa jiki a kai a kai da kauce wa barcin rana da kuma kiyayewa da tsayayyen lokacin kwanciya za su iya inganta barcinka ya zama mai dadi da gamsarwa.

Kuma wani abu mai muhimmancin gaske shi ne, ka guji yin duk wani abu da zai wahalar da jikinka sa'o'i kadan kafin lokacin barcinka ya yi.

Saboda wadannan dalilan ne ma wasu suke ganin yana da kyau mutum ya samu dan littafi na rubutu abubuwan da yake yi kafin barcinsa ya yi, domin ta haka zai iya kaucewa duk wani da ke hana shi barci.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ka da ka kwanta da na'urar da ka saba karatu da ita (waya ko karamar kwamfutar hannu da sauransu)

Ko da ike dai karatu ba abu ne da yake da wani tabbataccen lokaci ba, muna yi a lokuta daban-daban, amma, duk da haka sauya lokacin da kake karatu zai iya rikita lissafin tsarin aikin jikinka.

Yawancin masu karatu ta wayar salula ko ta kwamfuta, idonsu ya saba da shudin haske, saboda haka, idan suka dauko waya ko 'yar kwamfutarsu ta hannu suna karatu a lokacin da suka kwanta, wannan sabo da kwakwalwarsu

ta yi, na abin da idonsu ya saba gani da rana zai sa ta dauka cewa yanzu ma rana ce, sai jikin ya ki tura sinadarin da yake sa mutum barci (melatonin) saboda haka sai ya kasa barci da wuri.Saboda haka amfani da littafi a lokacin ya fi.

Haka kuma abin yake ga wadanda suka saba da sauraren kida da wani abu ta na'urar MP3 da ire-irensu.

Idan kana so ka samu barci mai dadi da gamsarwa, to lokacin kwanciyarka lokaci da za ka iya waiwayen da, wato ka koma amfani da abubuwan da aka yi watsi da su bayan zuwan fasaha, kamar su littafi.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ka jarraba cin kayan abincin da ke taimaka wa barci

Irin abincin da mutum ya ci da rana ko kafin dare na taimaka wa barcinsa ko kuma akasin haka.

Abincin da yake da sinadarai masu sa karfi da kuma masu gina jiki (carbohydrate da protein) amma kuma wadanda ba su da maiko sosai sun fi taimaka wa barcin mutum, idan dai an ci su akalla sa'a daya kafin kwanciya.

Yawanci abin da ke jawo mutum ya kasa jin dadin kwanciya ko barcinsa, yana da alaka da minshari. Mutane da dama ba sa iya sanin abin da yake sa su farka daga barci duk kuwa da cewa sukan farka sau da dama a dare daya.

Akwai abubuwa da dama da ke sa hakan amma wasu za a iya magance su ta hanyar sauya yadda mutum yake kwance.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Idan kana kwance a rigingine sai ka juya ka yi rub-da-ciki, ko ka kwanta da kwibi.

Wasu masanan kuma sun ce yana da kyau mutum ya koyi busa wani abu kamar algaita(didgeridoo a harshen Ingilishi) ko domin tana karfafa jijiyoyin numfashin mutum.

Wani karamin bincike da aka yi wanda aka rubuta shi a mujullar harkokin lafiya ta Birtaniya(British Medical Journal), ya nuna hakan yana taimakawa masu fama da wannan matsala ta minshari, har su rika samun barci mai kyau, in

banda 'yar farkawar da za su dan rika samu a 'yan lokuta amma ba kamar da ba.

Amma dai wannan ba hanya ce da ta dace da wasu ba, musamman wadanda suke da makwabta, wadanda su kansu suna bukatar su yi barcin.

Kamar yadda ka sani babu wata hanya takamaimai da za a ce lalle ba makawa tana maganin matsalar rashin barci. To amma idan ka jarraba wasu daga cikin wadanda aka sanar da kai ko ka koya, sai ka rika jarrabawa daya

bayan daya har ka samu wadda ta fi dacewa da kai.

Ba shakka hakan ya fi kirga tumakai (kamar yadda wasu ke yi a al'adarsu idan mutum yana son ya yi barci).