Bunkasa koyo ta jan hankali

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wasu makarantu suna amfani da kade-kade da hayaniya da kanshi a aji domin ganin ko hakan zai sa dalibai su kara kokari a jarrabawa- hakan zai yuwu kuwa? Catherine de Lange ta bincika.

Kanshin me makarantarku take yi? Tana da hayaniya ko shiru take?

Za ka ga kamar wannan ba wani abu ne mai muhimmanci ko amfani ba, amma binciken da ke ta yi na nuna cewa kanshi da kara za su iya yin tasiri wajen koyo da kokari da tunani.

Hakkin mallakar hoto Getty

Hasalima wasu shugabannin makarantun yanzu sun fara sanya hayaniya da fesa turare a harabar makarantunsu domin ganin ko hakan zai iya bunkasa sakamakon da dalibai ke samu a jarrabawa. Ko hakan na da wani amfani?

Idan da akwai, to menene hadarin yadda muke aiki da kuma karatu?

Akwai tabbatattun shaidun da ke nuna cewa wasu surutan na kawo nakasu ga koyo.

Bincike da yawa da aka yi sun nuna cewa yaran da suke koyon karatu a wurin da hanyar jirgi ta bi kusa da manyan filayen jirgin sama ba sa kokari sosai a jarrabawa.

Ba wannan kadai ba hayaniya gaba daya ma ana ganin tana tasiri wajen koyo.

Farfesa Bridget Shield ta Jami'ar London South Bank, da Julie Dockrell ta Makarantar horon malamai (Institute of Education), suna gudanar da bincike tare da shawartar 'yan siyasa a kantasirin duk wata hayaniya kamar ta ababan hawa da jiniya da kuma shi kansa surutun da 'yan makaranta suke yi.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

A lokacin da suka sanyawa dalibai irin wadannan surutai da hayaniya a lokacin da suke yin jarrabawa, sun ga 'yan makarantar ba su kokari sosai ba.

Malaman biyu sun gano cewa lamarin ya fi shafar yaran da suke nakasassu ko kuma wata larura da suke bukatar kulawa sosai.

Farfesa Shield ta ce, surutun sauran 'yan makaranta ma ya fi daukar hankali a aji.

Wannan abu ne da masu tsara ko zayyana ginin budaddun ajujuwa(babban daki da babu bango da ya raba wannan ajin da wancan) za su yi la'akari da shi a aikinsu.

Malamar ta kara da cewa,'' surutu yana dauke hankalin mutane sosai idan wanda ake fahimta ne, wanda kuma ba da kai ake yi ba, tana mai kari da cewa, ''abu ne da ya zama ruwan darehatta a manyan wuraren aiki da ma'aikata suke cikin babban gini ko daki daya.''

A kan cewa ko surutun bayan fage yana da muhimmanci ko babu, wannan ya danganta ne da irin surutun da kuma yawa ko karfinsa.

A jerin binciken da aka yi a 2014, Ravi Mehta na Kwalejin koyon harkokin kasuwanci ta Illinois (College of Business) a Amurka, da abokan aikinsa, sun jarraba hazakar mutane yayin da suka

sa musu hayaniyar bayan fage kamar surutun kantin shan gahawa da wurin gini inda suka rika bude karan tun daga kadan har ya yi yawa.

A karshe sun gano cewa mutane sun fi hazaka da tunani idan karan bai yi kadan ba, yana tsakiya.

Idan kuma ya yi yawa sai ya rikita musu lissafi gaba daya su kasa wani kokari.

Wannan yana da alaka ne da wasu dalilai in ji Dakta Nick Perham, na Jami'ar Cardiff (Cardiff Metropolitan University) a Biritaniya, wanda ya yi nazari a kan tasirin kara a kan koyo, amma kuma ba ya daga cikin wadanda suka yi binciken.

Ya ce, da farko, kara ko hayaniyar da ta fi daukar hankali ita ce wadda ta fi kara.

Hayaniyar mutane da yawa a bayan fage wadda ba ta da kara sosai kuma ba ta yi kadan sosai ba ta na dan tsuma mutum, domin ita ba ta yi karan da za ta dauke maka hankali ma kuma

ba ta yi kasa ba yadda hankalinka zai rika kokarin ya ji menene.

A don haka Perham ya ke ganin, sanya dan kida ko sauti na waka a ajin adabi ko wanda ba na kimiyya ba ko kuma wani wuri makamancin hakan inda ake bukatar basira, yana da kyau zai

kara kwazon mutane ko.

Malamai da yawa a sassan duniya daban daban tuni suka fara sanya wa dalibansu kida ko waka a aji.

Da dama sun yarda da cewa jin sauti(kida ko waka) zai iya bunkasa basirar dalibai, wato abin da ake kira da Ingilishi Mozart effect.

Kari a kan wannan shi ne yadda masu bincike suke ganin cewa idan mutum ya saurari sautin da yake jin dadinsa kafin wata jarrabawa ko wani aiki, hakan ya kan sa mutum ya ji dadin

aikin, ya yi shi da kyau. In ji Perham, wanda shi ma ya yi nasa binciken a kai.

To amma fa a sani cewa ba a ko da yaushe ba ne sauraren sauti ko kida mai dadi yake da amfani idan za ka yi aiki ba.

Misali idan kana wani aiki da yake bukatar ka rika tuna abu daki-daki ko daya bayan daya misali lissafi, a irin wannan hali, sauti ko wani kara zai iya takura ma ko ma ya sa ka rika bata wanda wannan ya kunshi yawancin sauti.

Wakoki ko sautin da ke dauke da magana a daya bangaren su kuam za su yi damun mutumin da ke yin wata jarrabawa ko aikin da ya shafi ma'anar kalmomi, kamar karatun wani littafi.

To a nan da alama makarantun da suka zabi sauti mai dadi, za su iya bunkasa yanayin koyon dalibansu in dai sun yi zabe a tsanaki.

Wannan ba ita kadai ba ce hanya ta daban ta bunkasa koyon dalibai.

Ana sa yaran da suke da nakasa a makarantar Sydenham da ke Landan su rika nazarin darussan da ake koya musu a wurin da ke da kanshi daban-daban.

Misali, Lissafi a wurin da ke da kanshin lemon zaki, harshen Faransanci a inda yake da kanshin na'ana, yayin da shi kuma darasin tarihi ake so su rika nazarinsa a wurin da yake da kanshin wata shuka mai kanshin kamar cingam ko man goge hakora.

Babu bincike masu yawa da aka yi a kan cewa ko kanshi zai iya taimakawa wajen bunkasa kwazon mutum a kan abin da ya shafi tunani ko kwakwalwa, ko da yake dai, a kwai bayanai da aka samu masu sarkakiya.

A 2003,wani masani kan tunanin dan adam,a Jami'ar Northumbria da ke Landan, Mark Moss, ya gudanar da jarrabawa daban-daban a kan wasu dalibai da aka sa su a wurin da ke da

kanshin wata shuka mai kamar kanshin na'ana (lavender) ko wata mai fure launin ruwan shanshanbale da koron ganye, wadda ake turare da magani da kuma abinci da ita(rosemary).

Masanin ya ce, ita nau'in shuka ko furen na biyu(rosemary) ya dauki hankalinsa ne saboda yadda ta ke dadi kuma ake danganta kanshin da kaifin hadda ko tunani.

Shi kuwa kanshin daya furen mai kama da na'ana ana danganta shi ne da sanya mutum barci in ji Moss.

Mai binciken ya gano cewa, wadanda suke shakar kanshin furen farko(lavender) ba su tabuka komai ba a jarrabawar da ta shafi tunani da kuma natsuwa ba kamar yadda suka yi a wadda

ta danganci sarrafa wani abu ba.

Su kuma 'yan daya rukunin da suke shakar kanshin fure na biyu(rosemary), sun fi kokari a jarrabawar da ta shafi tunani duk da cewa ba su kasance da sauri ba.

Ko menene dalilin duka wannan sakamako ?

Watakila hakan ba zai rasa danganta da cewa kanshi yana shafar tunani ba, domin akwai alaka tsakanin sashen kwakwalwa da ya shafi kanshi da kuma na koyo.

Amma kuma duk da haka Moss yana ganin akwai karin wasu dalilai.

Domin gano tasirin kanshen furen na biyu (rosemary) a jiki, Moss, ya debi jinin wadanda suka yi jarrabawa a dakin da ke da kanshin furen jim kadan da kammala jarrabawar.

Sai ya ga cewa an samu karin wani sinadari da ake kira 1,8-cineole, a cikin jinin nasu, wanda kuma wani bincike da aka yi ya baya ya nuna wannan sinadari yana kara sadarwa tsakanin

kwayoyin halitta na cikin kwakwalwa.

Saboda haka yake ganin wannan zai iya sa aikin kwakwalwar ya inganta, har daliban suka fi kokari a wannan fanni.

Saboda haka a yayin da ka gama karanta wannan bayani, samu lokaci ka nutsa cikin hankalinka, ka rufe idanuwanka ka shaki numfashinka da kyau.

Kanshin me ka ji da kuma karan me?

Watakila amsar za ta iya shafar yawan abubuwan da ka koya a 'yan mintinan da suka gabata.