Gaskiyar babbar almarar fasaha

Mutane da ma da suke da kwarin gwiwa a kan al'amura sun yi imanin cewa fasaha za ta kawo sauyi a cikin al'umma ta intanet ce ko kuma ta wayar salula.

Sai dai kamar yadda Tom Chatfield yake gani, gaskiyar dangantakarmu da fasaha nesa ba kusa ba ta fi ban sha'awa.

Da yake gabatar da wata lacca a karshen 1968,masanin halayyar dan-adam dan Amurka Harvey Sacks, ya yi bayani a kan gazawar burin fasaha.

Masanin ya ce, ''a ko da yaushe muna fatan cewa idan muka kirkiro wata na'urar sadarwa duniya za ta sauya.''

''Maimakon haka hatta na'urorinmu da suka fi sauran na'urori fice da fasaha sai dilmiye cikin tsarin da daman ake da shi a duniyar da daman tuni ta mallaki duk wani tsari take da shi.'' In ji masanin.

A matsayin misali Sacks, ya dauki wayar tarho, wadda aka samar da ita a gidajen Amurkawa a watanni uku na karshe nakarni na 19.

A dalilin wannan fasaha sadarwa ta kai tsaye ta nisan duniya ta zama kamar abin al'ajabi.

A wurin Ba-Amurke masanin kimiyya da yake bayyana ra'ayinsa a 1880 wannan mafari ne na'' wata sabuwar al'umma, inda za a samu yanayin da kowane mutum,duk yadda yake nesa da

sauran jama'a zai iya yin waya da kowane mutum a cikin al'ummarba tare da wata matsala ta zamantakewa ko kasuwanci ba...''

To amma abin da ya biyo bayan bullar tarhon ba wani sabon tsarin al'umma ba ne, kamar yadda aka yi hasashe a baya, domin turuwar dabi'un al'umma cikin tsarin ta yi tasiri a cikin fasahar.

Sabuwar fasahar ba ta kawo sauyi na rana daya ba,a maimakon hakan sai ka samu fafutukar cusa wani sabon abu cikin al'adun da aka saba da su.

Misali muhawar farko da ta biyo bayan bullo da fasahar ta wayar tarho ba ta danganci sauyin da za a samu ba ne a zamantakewar jama'a illa bin da ya shafi kamala da karya ko yaudara.

Ma'ana me wannan dama ta tattaunawa da wani wanda ba ka ganinsa kai ke nufi ga sirrin gida ko kuma ga mutanen da suke da rauni ko saukin yaudara a gidan kamar mata da ma'aikatan gidan?

Shin abin kunya ne ka yi tarho ba tare da ka sa cikakkiyar sutura ba?

Irin wadannan na daga cikin damuwa da mutane suke nunawa a karni na 19 lokacin da aka bullo da fasahar wayar tarho, abin da kuma ya gamu da kokarin kamfanonin tarho na tabbatarwa da jama'a kare mutuncinsu.

Kamar yadda Harvey Sacks shi ma ya nuna, ''duk wata sabuwar na'ura ko fasaha da aka kawo wata dama ce kawai ta sake ganin abin da za mu iya gani a ko ina''

Kuma manufar duk wani rubutu a kan fasaha shi ne ganin an dauki fasahar a matsayin wata hanya ko dama ta mu sake nazarin= ko bincikar kanmu.

Tun shekara ta 2012 nake rubutu a wannan shafi, kuma a shekaru biyun da suka gabata na ga sabbin na'urori da ayyuka da aka kirkiro wadanda wani fanni ne na wannan yarjejeniya da muke magana a kai.

Ta kowane fanni ka duba, za ka ga cewa wannan lokaci namu, zamani ne da kirkirar sabbin abubuwa ta kankane.

A yawancin lokaci kirkirar ba tana samar da hanyar sanin menene a cikinta ba sai dai ta yi jagora zuwa ga wani gagarumin rashin sani ko makanta a kan ainahin al'aadunmu da kuma tunaninmu''

Ka duba yawan bayanan da ake yi a kan wata fasaha ta zamani.

An yi kiyasin cewa a shekara ta 2014 wayoyin salula za su fi mutane yawa a duniya.

A shekara ta 2014 kashi 90 cikin dari na bayanan duniya an kirkire shi ne a shekaru biyun da suka wuce.

Wayoyin salula na yau sun fi manyan kwamfutocin da aka yi jiya, haka kuma manhajar da aka yi yau ta fi mu a komai da sauransu.

Almarar kadaita:

Wannan labari ne da na'urori da ayyukansu ke karuwa har abada, inda suke tafiya ko jan mu a wannan tafiya.

Watakila almarar da za a iya cewa na tattare da wanna tafiya ta yau, ita ce sa rai da zuwan wani lokaci da basirar na'urorin za ta iya fin tamu.

Duk da cewa yawancin mutane ba su damu da wannan hasashen ba amma barazanar hakan kusan a zahiri take.

Ba shakka magana ce ta lokaci kawai ko dai wannan hasashe ya tabbata ko kuma mu tsira daga hasashen mu shiga wani sabon babi na tarihin dan-adam.

Ko idan hakan ba ta tabbata ba, domin shi cigaban kimiyya da fasaha wani abu ne mai ban mamaki, wanda dangantakarsa da cigaban dan-adam ta fi kasancewa da buri fiye da abin da yake a zahiri.

Ko muna so ko ba ma so ba za a cigaba da tafiya gaba ba har abada.

Za mu so mu tsira da gangar jikinmu da tarihi amma abin da muke so mu mayar da kanmu abu ne da zai zo da tsohon kyawunmu da kuma gazawar dan-adam.

Zuwa wani lokaci burinmu na fasaha zai kauce wa abin da yake iya tabbata a zahiri, ya yaudare mu.

Wannan shi ne dalilin da a shekaru biyun da suka gabata na dukufa wajen rubuta kasidu a kan dambarwar da ke tsakanin labaran da muke bayarwa na fasaha da kuma yadda suke shafar rayuwarmu.

Me kake gani ya cancanci fasaha ta mayar da hankali a kansa yau?

Wace dabi'a kake gani ta mutanen da za su zo a nan gaba wadda za ta yi daidai da matakin da za mu iya kaiwa da dan karamin lakataye mai kama da malam-buda-mana-littafi zai zama wayar tarho.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The truth about technology's greatest myth