Na yi na'urar gano tunanin mutum

Hakkin mallakar hoto Getty

Me kake kallo? Masanin kimiyya Jack Gallant zai iya ganowa ta hanyar bude tunaninka kamar yadda Rose Eveleth ta gano.

Jack Gallant zai iya sanin abin da ke zuciyarka. Ko kuma akalla zai iya gano abin da kake kallo idan kana cikin na'urarsa kana kallon fim din da ya kunna maka.

Gallant, wanda mai bincike ne a Jami'ar California, da ke birnin Berkeley yana da na'urar da ke sanin aikin kwakwalwa.

Wannan na'ura ce da ke nazarin hoton aikin kwakwalwa ta shiga zuciyar (tunani) mutum ta sarrafa abin da take gani ta yadda za a gane abin da mutum yake sakawa a ransa.

Idan irin wannan fasaha ta sanin tunanin mutum ta zama ruwan-dare, za mu damu? Ka yi wa Gallant wannan tambaya, ba za ka yi tsammanin amsar da zai ba ka.

A aikin da Gallant ya yi na bincike,an sanya wa mutane fim ne suna kallo yayin da shi da abokan bincikensa suke auna yanayin aikin kwakwalwarsu.

Daga nan ne kuma sai aka sarrafa bayanai ko hoton aikin kwakwalwar aka samar da hoton bidiyo na Youtube na abin da aikin kwakwalwar ya nuna.

A takaice abin da ake nufi a nan, masu binciken sun dauki hoton aikin kwakwalwar suka mayar da shi hotunan bidiyo, wanda hakan ke nuna abin da mutum ke kallo.

A wurin Gallant da abokan aikinsa, wannan wani fanni ne kawai na aikin fasaharsu.

Duk da yadda wannan na'ura ta shi ta dauki hankalin duniya, shi a wurinsa ba wai ya tsara yin na'urar da za ta rika gano abin da ke zuciyar mutane ba ne.

Ya ce,''wannan daya ne daga cikin abubuwa da suka fi ban sha'awa da daukar hankali da muka taba yi, amma da ba kimiyya ba ce.''

Ainahin abin da Gallant yake son ganowa a binciken nasa, shi ne yadda jikin mutum yake gudanar da aikin sarrafa hoto ko abin da mutum yake gani.

Wanda a kan hakan ne ya samar da samfurin yadda kwakwalwa ta ke sarrafa bayanan hoto ko abin da mutum yake kallo.

Gano na'urar nazarin tunani ko abin da mutum yake tunanin, ribar kafa ce kawai, wato karin wata sa'a ce a aikin da suke yi, amma ba ita ce ainahin binciken kimiyyar da suka sa a gaba ba.

Ya ce, ''abin ya dai ya kasance ne cewa idan ka kirkiri kyakkyawan samfurin kwakwalwa, wannan na'urar za ta zama mabudin abin da kwakwalwa ke sakawa.''

Maganar dai ita ce, kimiyya ko ba kimiyya ba, wannan na'ura ta taso da fargabar da wasu mutane ke yi cewa, wata rana gwamnati za ta iya satar abin da ke zuciyarmu.

Watakila ka ga hakan kamar wata fargaba ce kawai ta sakarci, to amma Gallant ya ce ba sakarci ba ne.

Ya kara da cewa,'' a gaskiya na yarda da wannan fargaba, amma ka da ka tayar da hankalinka nan da shekara 50.''

Za a dauki tsawon wannan lokaci, ba a iya gano biyu daga cikin matsalolin da suka shafi fasahar nazarin kwakwalwar mutum ba, wato, samun karamar na'ura da kuma kyawun bayanin zanen aikin kwakwalwar da na'urar za ta fitar.

A yanzu idan Gallant zai yi nazarin tunaninka, sai ka shiga wata katuwar na'ura kuma mai tsadar gaske, wadda za ta auna inda jininka yake bi a kwakwalwa.

Duk da kasancewar wannan na'ura daya daga cikin hanyoyin da suka fi aiki wajen auna ko nazarin aikin kwakwalwa a yanzu, ba ta da tabbas dari bisa dari kuma ta yi girma.

Mutane ba sa iya motsawa a cikinta sannan ga ta da tsada.

Haka kuma hoton bidiyon da Gallant ya ke samarwa daga bayanan da ya tattara na na'urarsa ba ya kasancewa dari bisa dari daidai da wanda ake gani a fim din da ya sa mutum yake kallo.

Yanzu dai sai wani ya kirkiro wata hanyar ta auna aikin kwakwalwa wadda ta wuce yadda ake yi yau, idan ba haka ba, ba za a samu kananan na'urorin sanin tunanin da mutum yake

sakawa ba da yawa, wadanda za a iya amfani da su a ko ina, in ji Gallant.

Na'urar sanin mafarki

Duk da cewa Gallant ba ya wani aiki na kokarin kirkiro wata na'urar ta gano sirrin wani abu, wasu suna yi. Akwai ayarin wasu masana a Japan da a yanzu suka dukufa wajen kirkiro wata

na'ura ta sanin sirrin da ke cikin mafarki ko ma'anarsa ta hanyar amfani da fasaha irin ta Gallant (fMRI).

To sai dai ba kamar yadda aka yi amfani da hoton bidiyo na fim ba, a wancan aikin na Gallant, inda masu binciken sun san hoton da mutum yake kallo kuma su tabbatar da hakan daga

nazarin kwakwalwar da suka yi, shi mafarki ya fi haka sarkakiya nesa ba kusa ba.

A jarrabawar da masu binciken na Japan suke yi, suna sa mutum ne a cikin na'urar sai su sa shi yanayi na barci da mafarki, daga nan sai su tashe shi, su tambaye shi abin da ya gani,

sannan su kwatanta shi da abin da suka gano a nazarin kwakwalwar da suka yi.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Masu bincike na kokarin gano sirrin mafarki ta hanyar nazarin aikin kwakwalwa

Ta hanyar amfani da bayanan da suke tattarawa masanan na Japan sun iya gano kashi 60 cikin dari na irin abubuwan da masu mafarkin suka gani.

Sai dai akwai wata babbar matsala a nan domin tsakanin wannan gwajin da ake yi da kuma wata na'ura da za ta yi aiki a duniya baki daya, kowane mai mafarki bayanan da kwakwalwarsa

za ta fitar da za a nazarta a fassara mafarkin sun bambanta.

A yanzu ita wannan na'ura da ake gwaji da ita, sai an tsara ta yadda za ta saba da kowane mutum.

Saboda haka, ko da ka shiga wannan na'ura an yi gwajin da kai, babu wata ta duniya baki daya da za ta iya bayyana mafarkinka.

Duk da cewa ba ya aikin yin wata na'urar yanzu, amma Gallant ya san irin na'urar da ya kamata ya kera idan zai yi.

Ga abin da ya ce,''Ra'ayina shi ne, idan kana son ka kera wadda ta fi dacewa, sai ka yi wadda za ta fassara maganar cikin zuciyar mutum ta fito fili, daga nan za ka iya amfani da wannan

na'ura wurin tuka mota.Wannan za ta iya zama wadda za a iya amfani da ita a duniya.''

Ko ba komai, wannan na'ura ta neman sanin abin da kwakwalwar mutum ke sakawa ta jawo sha'awa sosai a kan aikin Gallant, wanda ya ce, ''idan na tari mutum a titi na gaya masa yadda

kwakwalwarsa take aiki sai ka ga ya kawar da idonsa.''

Idan kuma ya nuna masa hoton bidiyon yadda kwakwalwarsa take aiki daga nan sai ya tsaya ya natsu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Neuroscience: I built a brain decorder