Kana son koyo da sauri? Yi amfani da jikinka

Hakkin mallakar hoto science photo library

Daga hannunka ko motsi da yatsunka da kuma kai kawo a cikin daki ka iya sa ka koyi abu da sauri, in ji Colin Barras. Ko ya hakan ke yuwuwa?

Ka taba samun kanka a yanayi na neman shawo kan wata matsala? Ko ka koyi wani abu? Ka fahimci wani bayani mai wuya?

Hanyar koyo tana cike da misalai da za a yi da sassan jikin mutum, ba sai da kwakwalwa ba kadai. Watakila saboda wadannan tambayoyi suna nuna alamun wani abu mai zurfi.

Masu bincike suna ganowa cewa koyon abu ya fi sauki da sauri da kuma karko idan darasin koyarwar ya kunshi amfani da jiki da kuma kwakwalwa; ko ta hanyar nuni ko ishara ko kwatance da hannu ko tafiya a cikin daki.

Ko wannan abu zai iya bunkasa yadda ake koyo da koyarwa a nan gaba? Kuma ko hakan zai nuna yadda za a yi amfani da fasaha a aji a nan gaba?

Ta wasu hanyoyin, maganar cewa jiki zai iya taimakawa wajen koyarwa ba abin mamaki ba ne.

Idan ka duba za ka ga da yawa daga cikinmu mun fara koyon lissafi ne ta hanyar kirge da 'yan yatsunmu kafin mu rika yi da kwakwalwa.

Andrew Manches wani malami da ya juye ya zama masanin tunanin dan-adam a Jami'ar Edinburgh ta Birtaniya, ya ce, '' a da mutane sun ce yayin da muke koyo muna zama wadanda suke iya tunani da ka.'' wato ba sai an baje mana abubuwa a zahiri ba, misali za mu iya lissafa su.

Ya ce,'' Kananan yara sun dogara ne ga abubuwa na zahiri da suke taimaka musu,amma idan a wurin taro aka ba ni wani lissafi na yi, sai na debo wasu abubuwa kamar tsakuwa ko lemo da za su taimaka mini a lissafin, ba shakka za a dauke ni wawa.''

A haka za mu yi tunanin cewa malamai za su yaye yara, su daina koya musu ilimi da abubuwa na zahiri da kuma amfani da jiki domin sun fara kama hanyar zama manya, da ba sa bukatar irin wannan koyarwa.

To amma a gaskiya duniya ta zahiri (wato wadda ke amfani da abubuwa da ake gani) ba ta rabuwa da tunaninmu, duk da cewa malamanmu sun yaye mu wajen koyar da mu ta hanya irin ta kananan yara tun muna kanana.

Misali idan muna maganar kalmomin aiki kamar na Ingilishi ''lick'' da ''kick'' da kuma ''pick'', na'urorin daukar hoton cikin jikin mutum na asibiti suna nuna yadda bangaren kwakwalwarmu da ke tafiyar da jijiyoyin fuskarmu da kafafuwa da hannaye dukkansu suna yin wani aiki.

Jiki da zuciya

Wannan nazari ya shafi jiki ne da zuciya, kuma yana nuna cewa abin da zuciyarmu ke tunani yana samun asali ne daga ayyukanmu da mu'amullarmu da abubuwan da ke kewaye da mu.

Hakan na nufin idan muka sa yara su koyi abu kamar yadda manya ke koyo ba tare da nuna musu abu na zahiri ba, wato ta hanyar amfani da tunani kawai, za su yi wahalar fahimtar abin da ake koya musu da kuma tuna shi.

Kimiyya ta fara tabbatar da maganar nan da ake cewa, ''gani ya kori ji'' a aji.

Spencer Kelly, masanin tunanin dan-adam a Jami'ar Colgate da ke Hamilton a New York, ya gano cewa, mutane sukan yi amfani da lokacinsu linki uku suna sadarwa ta hanyar amfani da wani sashe na jikinsu (wato ishara kamar da hannu), idan suna ganin hakan zai isar musu da sakon da suke son gabatarwa.

Wannan ke nan yana nuna cewa ko da a can cikin tunaninmu ma, mun yarda da amfanin isharar (amfani da jikinmu a zance kamar yadda kurame ke yi) da mukan yi wajen mu'amulla.

Kelly ya kuma gano shedar da ke nuna cewa mutane sun fi son malamin da yake koyarwa yana amfani da hannunsa wajen jaddada abu ko bayani.

Muhimmancin amfani da jiki wajen koyarwa ba ya tsaya wajen sa malami ya yi fice a wurin dalibai ne kadai ba, abin ya wuce haka.

Bincike da yawa da aka yi ya nuna yara sun fi gane karatu idan malaminsu yana amfani da jikinsa wajen yi musu bayani.

Haka kuma Susan Wagner, masaniyar tunanin dan-adam a Jami'ar Iowa da ke birnin Iowa, ta gano cewa yara sun fi gane wani sabon darasi sosai idan aka bukace su su duba yadda malaminsu ya siffanta abin da jikinsa, su ma su yi.

Kuma darasin da aka koya wa yaro ta hanyar magana da ishara (jiki) ya fi zama a kwakwalwar dalibi fiye da na magana kawai.

Dabarar fasaha

Duk wannan abu da muke magana fasaha tana da gurbinta a ciki, musamman a yanzu yadda ake samar da na'urori masu nuna ko kwatanta wani abu da jikin mutum zai yi, kamar Nintendo Wii da Kinect na Microsoft da kwamfutocin hannu na komai-da-ruwanka da makamantansu.

A yanzu ana amfani da fasahar Kinect wajen taimaka wa yara koyon inda ya dace sosai su sa lambobi a wani wuri misali layi a wani fili, wanda wannan abu ne mai sauki amma kuma mai muhimmanci wajen fahimtar lissafi.

Masu bincike a Jami'ar Eberhard Karls a Tuebingen da ke Jamus, sun gano cewa, yaro dan shekara bakwai zai iya sa lambobi a kan wannan layi da aka shata dai dai inda ya kamata lambar

ta kasance a kan layin, idan yaron ya yi tafiya a kusa da layin idan fasahar ta Kinect tana dauka tare da sarrafa bayanin tafiyar da yake yi, fiye da a ce yaron ya yi amfani da kwamfuta ne

kawai wadda ke ba shi bayanin layin a cikin kwamfutar.

Manches ya fara duba yadda ko za a iya amfani da fasahar ta Kinect wajen sake tsarin wasan yara na gina daki ko gida da 'yan robobin nan masu kama da bulo.

Wannan fasaha tana bai wa yara damar sarrafa robobin (a kwamfuta maimakon na zahiri) kamar yadda suke yi da robobin na gaske.

To amma a nan su wadannan robobi na cikin kwamfuta za su iya yin wani abu da na zahirin ba sa yi, kamar su sauya launi idan yaro ya raba su , wanda hakan zai sa yaro ya samu wata sabuwar fahimta ta yadda za a iya raba lambobi a lissafi.

A dangane da muhimmanci da amfanin wannan salo na koyarwa ba abu ne da kusan a ce ba zai dace ba a ce malamai da dalibansu su rika tsalle da daga hannayensu da juyawa kamar fanka a lokacin darasi.

Sai dai Manches ya kawo hanzari, inda ya ce matsalar ita ce kimiyya ba ta fayyace takamaimai yadda tasirin dangantakar jiki da zuciya za ta yi aiki ba.

''Ba za ka iya hanzarin yin hasashe kan yadda wannan hadaka za ta kasance da wuri haka ba'' in ji Manches.

Sai dai Cook ita kuma cewa ta yi, ''wannan ba yana nufin ba wani nazari na tabbatar da abin da yake faruwa ba, musamman idan ana maganar fahimtar abin da ya sa bayani da hannu ko jiki yake taimakawa wajen sa ilimi ya fi zama a kwakwalwa ba.

Ta ce darasin da muke koyo a makaranta abu ne da yawanci ya kunshi bayani ko magana da za mu iya tunawa ko mu ayyana a wata rana a gaba.

To amma wasu daga cikin abubuwan da ke kwakwalwarmu ba irin wadannan ba ne, da za mu iya ayyanawa a duk lokacin da muka so, saboda abubuwa ne da za mu fada ba tare da mun iya bayanin yadda aka yi, ba mu manta su ba, misali kamar tuka keke.

Wannan abu ne da ba za mu iya cewa ga dalilin da ya sa ba mu mance shi ba. Saboda haka motsi shi zai fi dacewa da koyan abubuwan da ba za ka iya ayyana dalili na rashin manta su ba.

Don haka ta hanyar magana da kuma motsi da jiki za mu iya karfafa kwakwalwarmu ta yi hadda biyu daban daban, wanda hakan zai kara mana damar tuna wannan abu a nan gaba.

Duk da cewa masu bincike irin su Manches da Cook ba su fitar da wani tsari ko ka'ida da malamai za su bi ba, gargadinsu kan wannan tsari ko hanya ya fara samun rauni.

Cook ta ce, ''shekaru biyar da suka wuce da zan iya cewa akwai yuwuwar hadari sosai wajen bai wa malamai umarni daga wannan bincike.''

A yau wannan masaniya ba ta damu ba da wannan hadari da ta nuna fargabarsa ba,saboda a bangare guda ba wani daga cikin binciken da ta yi zuwa yau da ya gano wata illa ta tattare da wannan dabara ta koyarwa.

Ga abin da ta ce kuma,'' a duk nazarin da muka yi na jarraba amfanin ishara ko yin alama da jiki wajen koyarwa, mun ga tsarin yana aiki, hatta ma a gwajin da muka yi inda muke ganin isharar ba za ta yi aiki ba.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Want to learn quicker? Use your body