Yadda waya ke dauke hankalin mutane

Hakkin mallakar hoto lencap alamy

Wayoyin komai-da-ruwanka 'yan kananan kwamfutoci na hannu (tablets) suna dauke hankalin masu hawa motoci da jirage a zamanin nan. To amma hakan na nufin ba sa

sanin abin da ke gudana ke nan, su kuma fasinjojin da ba sa rike da komai me suke yi ke nan? Chris Baraniuk ya bincika

Ka hau duk wata motar bas ko jirgin kasa a yau za ka ga fasinjoji kowa sanye da kwat ba abin da yake yi sau kallon 'yar na'urar wayar da ke hannunsa.

Watakila ba inda fasaha take da mabiya sau-da-kafa kamar cikin irin wadannan ababan hawa.

Amma kuma duk da haka wasunmu na ganin yadda wannan na'ura ke dauke wa mutane hankali abin na da illa.

Hakan ne ma ya sa fasahar bidiyon Look Up, wadda ke nuna cewa za mu fi jin dadi idan muka tsinke layinmu na sadarwa na waya ta ja hanakalin mutane sosai.

Hakan ne kuma ya sa lokacin da aka sa hoton mutumin da ba shi da waya a shafin Twitter da maudu'in #guywithoutaphone ya zama abin dariya a wurin mutane.

Saboda da wuya a ce yau ga wani mutum a jirgin kasa ko a motar bas ba shi da waya rike a hannunsa.

A shekarar 2009 Stephen Dowling na BBC ya samu fasinjojin da ba wayar Ipod ko jarida a hannunsu yake tambayarsu, su kuma me suke yi, tun da ba komai a hannunsu a lokacin.

Abin da suke gaya mishi ya kama daga cewa, ''ina tunanin 'yar uwata ne da ke kwance a asibiti'' da kuma ''ina numfashi ne irin na wasan motsa jiki ( na inganta lafiya wato Yoga)''.

To a yau fa ya lamarin yake, bayan shekara biyar? Ko akwai irin wadannan mutanen? Idan kuma akwai su tunanin me suke yi?

Da safiyar wata ranar Alhamis mai hadari, fasinjojin jirgin kasa na karkashin kasa na Landan suna ta tururuwa sun kama hanyarsu ta zuwa wuraren aikinsu duk da cewa dai a lokacin yawan masu zuwa aikin ya ragu.

Tafiyar ta kama ne daga tashar Wembley Park, wadda tana da tsawo, saboda haka yawancin fasinjoji kowa ba abin da za ka ga yana yi sai kawai zuba idonsa a kan wayarsa yana wani abu da ita.

Mutum daya ya fita zakka daga ciki. Rahul Giri mai shekara 38, shi yana zaune ne shi kadai, ba abin da yake yi sai kallon sararin duniya ta tagar wannan jirgin kasa.

''Ni ma'aikacin fasahar sadarwa ne. Sa'a tara nake yi a gaban kwamfuta,'' ya ce. ''Wannan ya ishe ni!''

Wani lokacin Giri yana duba wasikunsa na email a wayarsa ta BlackBerry, in ban da wannan shi kam ya fi so ya huta idan yana tafiya a jirgin.

Shi ma Mark Deerman mai sheakara 66 haka yake. Ya ce, ''ina jiran a kirawo ni ne ta waya'' Yana taba aljihun rigarsa inda wayar take.

Mr Deerman, wanda ma'aikacin gidan waya ne, shi yana ganin ba amfanin ya debe wa kansa kewar wannan zama ta hanyar dukufa wasu abubuwan da wayar tasa kamar yadda sauran

fasinjoji suke yi, tun da dai ya san za a iya kiransa ta wayar, duk da dai cewa, wayar ta kan katse a wasu lokutan tun da hanyar karkashin kasa ce suke ciki.

Haka su ma fasinjojin da suka toshe kunnuwansu da wayar suna jin kida ko wani abu da ita, Mista Deer ba ya cikin masu wannan dabi'a kuma haushinsu ma yake ji.

'' ina jin takaicin wannan abu da suke yi, ko littafi ba za su karanta ba, ba sa kokarin sanin labaran abubuwan da ke faruwa na yau da kullum, kidansu kawai suke saurara ko wani abu.'' Ya koka.

Hakkin mallakar hoto hemis alamy
Image caption Fasinja na jiran jirgin kasa a tashar Baker Street

A titin Baker Street, a nan layin dogon ya hadu da hanyar jirgin ta karkashin kasa wadda tafi dadewa., domin tuna shekarar 1863 jiragen kasa suke bin hanyar.

Jonathan Ham mai shekara 54 yana bin wannan hanya kusan kullum.

Ya ce, '' wani lokaci ina sauraren kida. Amma dai na fi son na yi tunani idan ina wannan tafiya ko kuma dai in rika kallon yadda mutane suke.''

A matsayinsa na masanin kimiyyar halittu, a wani lokacin Ham, ya kan karanta mujallar kimiyya a jirgin, amma a wannan lokacin ya ce, '' ba na jin sukuni yau!''

Sai dai mutanen da yake kallo, su kuma ra'ayinsu ya sha bamban, domin su a wurinsu, jirgin wuri ne da kowa zai fito da wayarsa da sauran 'yan na'urorinsu na hannu su dukufa a kansu.

Ya ce, ''mutane sun dukufa kacokan a kan wayoyinsu da 'yan kananan kwamfutocinsu na hannu.

Bana jin dadin yin hakan gaskiya, ko don ni ba dan zamani ba ne kila. Ba ruwana da wannan tsarin samsam.

Ba ni da ma ko email a gida. Amma ina da kwamfuta a gida amma ba ta da intanet. A wurin aiki kawai nake wannan.

Idan ina son na yi email zan iya yi da wayata, amma a hakan ma na dan jirkita wayar saboda haka da 'yar wuya in yi.''

Al'adar dauke hankali kacokan

Wadanda suke kokaw da yadda wayar komai-da-ruwanka ke dauke wa mutane hankali har suke ba da shawara mutane su katse layin waya sun sami mabiya a kwanan nan.

Daya daga cikin irin wadannan mutane shi ne, wani marubuci kuma farfesan Ingilishi, Tom Montgomery Fate na Kwalejin DuPage ta Chicago.

Ya ce,'' ina ganin raguwa a yadda dalibaina suke karatu da mayar da hankali, wanda ina ganin hakan ya kasance kishiyar fasahar da aka samu.

Ina jin takaicin cewa sadarwa ba za ta iya zama gaba da gaba ba. Ba za ka iya ganin duniyar ba idan kana kallon kasa a ko da yaushe; idan wani abu ya dauke maka hankali.''

Hakkin mallakar hoto Getty graham
Image caption Jama'a na amfani da sabbin wayoyin tarho da aka sa a tashar jirgin kasa ta Oxford Circus a 1968

Farfesa Fate, ya tsani abin da ya kira '' ko da yaushe sabuwar al'adar dauke hankali.''

Sai dai a kwanan nan shi kansa ya ba da kai, inda ya sayi wayarsa ta komai-da-ruwanka ta farko domin ya rika yin kiran da ke nuna hoton bidiyo da 'yarsa wadda ke karatu a Madrid.

Mutane sun yarda kuma akwai shedar da ke tabbatar da cewa, idan muka tsayar da hankalinmu a kan abin da ke faruwa kusa da mu, maimakon zuba wa waya ido, za mu fi jin dadin rayuwarmu.

Amma kamar yadda da yawa daga cikin mutanen cikin jirgin nan na kasa suka nuna za ka iya amfani da wayarka ka cimma hakan.

Hakkin mallakar hoto fine art alamy
Image caption Wani lokaci ba abin da yake da dadi kamar ka zauna ba ka komai

Yayin da jirgin ya nufi barbican, Katie Walker mai shekara 29, sai ta ce, ''ina bukatar wani abu da zan yi gaskiya, kamr kallo a iPlayer di na ko kuma sauraren kida wanda ya fi dadin hutawa.''

Wata ma da ke tafiya a jirgin na karkashin kasa na Landan, ta bayyana cewa da a lokacinma tana amfani da wayarta don dai an kasa ta ne a wasan Candy Crush da take yi, kuma tana son ta dan huta.

Wani lokaci fasaha tana tilasta mana mu mayar da hanakali wajen sanin muhallinmu.

Sinead Dennig, mai shekara 24 barkewa ta yi da dariya lokacin da take bayanin abin da ya sa take zaune ba ta komai.

''Wayata ta mutu!'' Ta ce, yayin da jirgin ya nufi titin Liverpool Street tasharsa ta kusa da ta karshe.

''Ina tunanin yadda zan samo chajar wayar ne. Sai na je gida dole na dauki chajar na chaja ta sanna na dawo. Zan je wajen wata kawata ce wadda da mun hadu yanzu, idan da ba sai na koma gida na chaja wayar tawa ba.''

Wannan yanayi na rashin waya da Dennig ta samu kanta a ciki ba tsammani, ya tilasta mata kallon muhallinta.

Ta ce, ''hakan ma da na zauna ina jin dadi. Da zan dauko littafi na ne na karanta, amma sai na ji na gaji. Kawai ina son na zauna na huta ba na komai!''

Pic doing nothing..................................

Jenny Davis mataimakiyar Farfesa a fannin nazarin halayyar dan-adam a Jami'ar James Madison ta Virginia, ita tana ganin maganar cewa akwai bambanci tsakanin mutanen da suke amfani

da waya da wasu abubuwa a jirgin kasa da wadanda ba sa yi ba haka abin yake ba.

Ta ce a wuraren da suke a birane a ko da yaushe akwai abin da zai daukar maka hankali, ko waya ce ko wata na'ura ce ko jarida ko ma tunaninmu ko dai wani abu.

Wadannan kalamai sun dace da hoton fasinjojin jirgin kasan da ya yi kama da na shekarun 1940 ko 1950, inda kowanne ya dukufa karanta jarida.

'' Duk wannan fasaha tana sa mu zama marassa son mu'amulla da junanmu'' kamar yadda rubutun da ke biye da hoton ya nuna.

''Sam babu maganar cewa muna cikin natsuwa, wai ba abin da ya dauke mana hankali, idan muna cikin irin wannan yanayi na dube-dube, a ko da yaushe muna tunowa da wasu abubuwa

na tarihinmu da abubuwan da suka faru da mu da kuma tunanin abin da ke a gaba'' In ji Davis

To dai watakila a nan sai a ce babu wani darasi da za a koya. Gaskiya ne fasinjojin cikin jirgin kasa na Landan, dukkanninsu suna da dalilin duk wani abu da suke yi.

Ninu Arghard mai shekara 23, wata mata ce da take rike da wayarta a hannu, duk da cewa fuskar wayar ta yi baki, kuma ba ta amfani da ita a lokacin, da aka tambaye ta, sai ta ce, ''ina

son kawai na dan yi kalle-kalle ne, ba zai yuwu ka yi ta amfani da waya ba a ko da yaushe, abin da gundura wani lokaci''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan On your commute? Maybe you shouldn't read this