Me ya sa muke kyalkyala dariya haka kawai?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wani lokaci mukan kyalkwale da dariya idan muka ga wani abu da ba mu saba gani ba. Kamar yadda masana tunanin dan-adam suke bincike, wannan kyakyalniya na iya kasancewa daya daga cikin muhimman dabi'unmu in ji David Robson.

Mun kusa gama hirarmu da Sophie Scott, sai kawai ta dan juya a kujerarta ta kunna min wani hoton bidiyo na wani mutum dan Jamus da ya je wanka a wani rafi da ya daskare da kankara.

Bayan kusan minti daya da aka nuno mutumin yana shirin durgowa daga saman da ya hau, durowarsa ke da wuya a she bai sani ba ruwan tafkin ya zama kankara.

Da fadawarsa sai abokansa suka zuba ido su ga me zai faru. Bayan dan lokaci kadan sai kawai suka fashe da dariya, da dai ba su ga jini da kasusuwa warwatse ba, kuma suka ga yana ta 'yan noke-noke in ji Scott.

To me ya sa muke kyakyata dariya ne ko da kuwa wani abin tausayi ne ya samu mutum? Kuma mai ya sa sai ka ga kusan idan dariyar ta kama sai ka ga kowa a wuri ya dauka?

A matsayinta na masaniyar aikin jikin dan-adam a Jami'ar Kwaleji ta Landan(University College London), Scott, ta dauki wasu 'yan shekaru da suka gabata tana kokarin amsa wadannan tambayoyi.

Kuma a taron gabatar da jawabai kan fannoni daban-daban na rayuwar dan-adam da aka yi a 'yan watannin a Vancouver, wato TED2015, Scott ta bayyana cewa dariya na daya daga cikin dabi'unmu mafiya muhimmamnci da kuma ba a fahimta ba.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

A ko da yaushe abokan aikin Scott, masu son ganin komai ya tafi a kan tsari, ba sa yarda da aikinta.

Ita ma a ko da yaushe tana son nuni zuwa ga wata 'yar takarda da aka rubuta da hannu, wadda ta taba gani an manna a jikin wasu takardun bincikenta.

A jikin takardar, an rubuta cewa,'' wadannan tarin takardun kamar shara ne (saboda abin da ke cikinsu), kuma za a zubar da su idan ba a kwashe su ba, shin wannan kimiyya ce?''

Domin nuna karfin halinta da jajircewa a kan abin da take yi da kuma karbar sukar da ake yi mata, a yanzu tana sa wata riga ne mai rubutun da ke tambaya, ko mutum a shirye yake domin halattar wasan kwaikwayon da za ta gudanar nan gaba da yamma.

Ta dai fara binciken nata ne, da nazarin muryoyi baki daya, da kuma bayanan da murya ke dauke da su.

Ta ce, ''za ka iya samun kyakkyawan bayani, daga jinsina da shekaruna da matsayina da garina na asali da yanayina da lafiyata har ma abubuwan da suka shafi mu'amullata.''

Daya daga cikin hanyoyin bincikenta, ta hada da, binciken kwakwaf da na'ura da ta yi kan kwararren mai wasan shigar burtun nan da ke kwaikwayon mutane, Duncan Wisbey, domin ta ga yadda ya kware wajen kwaikwayon maganar mutane.

Abin mamakin da ta gano shi ne, yanayin aikin kwakwalwarsa na da alaka da motsin jikinsa da kuma bangaren kallonsa, domin kokarin da yake yi a lokacin ya ke kwaikwayon, yana son kamar ya shiga fatar wanda yake kwaikwayo ne(ta yadda zai zamarwa mutane kamar wancan mutumin)

Haka kuma bincike a kan wannan fanni na shigar burtu, ya sa ta gano cewa bangarorin kwakwalwa da ke aiki kan abin da ya shafi yanayin harshen mutum, wato salon yarensa da kuma iya maganarsa, wanda wadannan abubuwa ne da ke fayyace inda mutum ya fito.

To sai dai wani bincike da ta yi a Namibia ne ya sa Scott , ta fara gano cewa dariya na daya daga cikin muhimman dabi'unmu na baki.

Binciken baya ya nuna cewa dukkanmu za mu iya gane dukkanin dabi'u shida da mutane ko ina a duniya suke da su ta fuska.

Dabi'un su ne tsoro da bacin rai da mamaki da farin ciki da kyama da kuma damuwa.

Duk da haka Scott, tana son ta gano cewa ko muryarmu na tattare da wasu bayanan na wasu dabi'unmu a cikinta, bayan shidan.

A kan hakan ne ta sa 'yan kasar Namibian da kuma Turawa da su saurari maganganun junansu da aka nada, su gano abubuwa, ko dabi'un da za su iya ganowa a ciki wadanda suka hada da wadancan guda shidan da aka sani a duniya, kari kuma da jin dai ko sauki da samun nasara ko biyan bukata.

Dariya ita ce abar da kowane bangare ya fi saurin ganowa. Scott ta ce ba tare da wani bata lokaci ba, kai tsaye ta bambanta daga sauran dabi'un.

A ko da yaushe ta yi bincike sai ta gano karin wasu abubuwa masu sarkakita tattare da wannan dabi'a ta dariya.

Misali mai binciken ba da jimawa ba ta gano cewa yawancin dariyar da mutane ke yi ba ta da alaka da wani abin dariya.

Ta ce, ''mutane suna dauka cewa yawanci suna dariya ne domin abin dariyar da wasu mutanen suka fada, amma kuma a tattaunawar da muke yi, mutumin da ya fi yin dariya shi ne wanda yake magana.''

A don haka take ganin dariya wata dabi'a ce ta zamantakewa da take sa mu kara kusantar junanmu da kulla zumunci ko da abin da ya jawo ta mai ban dariya ne ko a'a.

Ta kara da cewa, ''idan kana dariya da mutane kana nuna musu cewa kana kaunarsu, ko kuma kana rukuni daya da su. Wato dai dariya alama ce ta karfin mu'amulla.''

Wannan ana ganin shi yake sa mata da miji ko saurayi da budurwa da suke tare suke yi wa juna dariya idan dayansu ya yi wani abu na kasawa, yayin da mutanen da ke kallonsu ko kusa da su ba sa dariyar.

Hakkin mallakar hoto Thinstock

''Za ka ji wani ko wata ta ce, ' yana da ban dariya, saboda haka nake son shi'. Abin da kike nufi shi ne 'ina son shi kuma na nuna mishi hakan ta hanyar yin dariya idan ina wurin da yake.''

Ba shakka dariya na iya kasancewa wata hanya ta tabbatar da mu'amulla tsakanin abokan soyayya; Scott ta yi nuni da wani bincike da ke nuna cewa mata da miji ko saurayi da budurwa ko kuma ma'abotan soyayyar da suke dariya da junansu sun fi samun daidaito bayan wani abu da ya tayar musu da hankali ko ya shiga tsakaninsu, kuma za su fi dadewa tare.

Wadansu bincike binciken da aka yi a baya bayan nan sun nuna cewa , mutanen da suke dariya tare idan suna kallon wani bidiyo na ban dariya za su fi bayyana wa junansu wasu abubuwa da sirrinsu, wanda hakan zai iya kara kusanci tsakaninsu.

Hatta abin dariyar nan da Bajamushen nan da ya fada tafki mai kankara da ya yi da sunan zai yi wanka hakan na iya kara dankon zumuntar da ke tsakanin abokanan nan nasa da shi.

''Abin ban sha'awa ne yadda abokan nasa suka barke da dariya a baki daya .Ina ganin sun yi hakan ne domin su sa ya ji sauki'' In ji Scott.

A dangane da hakan ne Robin Dunbar na Jami'ar Oxford ya ke ganin cewa dariya na da alaka da karin tsananin ciwo, watakila ta hanyar kara sa jiki ya fitar da karin sanidarin da ke kara kauna tsakanin mutane(endorphins).

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Yanzu Scott na kokarin gano bambancin dariyar da muke yi a lokacin da muke hira da abokanmu da kuma dariyar da muke kyakyatawa ba tare da shiri ba ma.

Misali mai binciken tana ganin dariyar da muke tilasta wa kanmu a lokacin da muke hira domin kara armashin hirar tamu, mun fi yin ta da hanci, yayin da dariyarmu ta sosai kuma ba ta hanci take zuwa ba.

Hotunan da ta dauka na aikin kwakwalwa sun nuna yadda kwakwalwar take aiki kan kowace irin dariya.

Dukkanin dariya iri biyun da mutum yake yi, na motsa bangaren kwakwalwar da ke sa takwaransa na wani mutumin shi ma ya motsa.

Wannan ne bangaren da ke motsawa da aiki idan na gan ka ka buga kwallon kafa ko kuma idan ni na buga. Kuma ana ganin bangaren ne yake sa kowa da kowa ya barke da dariya a lokaci daya idan wani abu ya faru.

Mai binciken ta ce akwai dama sau linki 30 cewa za ka yi dariya idan kana tare da wani fiye da ace kai kadai kake a wuri.

Za ka iya dauka cewa za a iya bambancewa tsakanin dariya ta gaskiya da wadda ba ta gaskiya ba, amma Scott tana ganin hakan ba abu ne mai sauki ba domin abin yakan dauki lokaci har zuwa kusan lokacin da mutum zai kai shekara talatin zuwa sama kafin ya iya ganewa.

Ko da yake za mu iya tsanar dariyar karya da wasu kan yi idan muna tare da su, amma Scott ta ce hakan zai kara fitowa fili ne da yadda mu muke ko halinmu yake maimakon abin ki game da dariyar da mutumin yake yi wadda ke bamu haushi.

Scott ta ba ni labarin wata kawarta wadda take ba ta haushi yadda take yawan dariya.

Ta ce, '' a ko da yaushe ina ganin tana dariyar da ba ta kamata ba, amma da na tsaya na lura sai na gane cewa, ashe saboda ba na taya ta dariyar ne shi ya sa nake ganin dariyar tata ba ta kamata ba kawai.

Idan da ba ta kaunar mutum to da za ta yi 'yar dariyarta ne kawai ba tare da mutumin ma ya sani ba kawai.

Bayan gano dankon zumuntar da ke tsakaninmu, nazarin Scott, ya kai ta har wurin masu wasn ban dariya.

Ta ce, ''abin ban sha'awa game da dariya a irin wadannan wurare na wasan barkwanci shi ne, ita ma dai hanya ce ta mu'amulla, domin masu kallon suna mu'amulla ne da mai barkwancin ta wata siga.

Ta kara da cewa, ''masu wannan wasan barkwanci sun fi jin dadi da sauki idan suna da jama'a masu yawa a wuri, watakila saboda yadda dariya take yaduwa daga wannan mutum zuwa

wancan, wato ke nan idan da mutane da dama za a fi saurin dariy.

A wurinta, ''wannan kimiyya ce?'' Rigar da take sa waza ta tuna mana. Ko da yake abokan aikinta masu tsattsauran ra'ayi ba lalle su amince da tsarinta ba na ganin abin da take yi ba wani

mai muhimmanci ba ne a wurinsu, amma duk da haka , ita a wurinta ta fahimci muhimmancin da dariya take da shi da irin tasirinta wajen yadda za mu bayyana kanmu kuma mu jawo hankalin mutane su saurare mu.

Ta ce, ''wani zai iya daukar dariya a matsayin wata aba maras muhimmanci da rashin ma'ana wadda kuma ba ta da wani tasiri. To amma, ba haka kawai take ba a ko da yaushe tana da ma'ana.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why do we laugh inappropriately?