Yaushe ne ganiyar rayuwarka?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ko shekaru gargarar tsufa ne da ba su da makawa ko kuma akwai wasu hanyoyin daban na nishadi da moriya na kaiwa ga tsufa? David Robson ya duba mana.

Ko ka taba damuwa cewa ganiyar rayuwarka ta wuce ka ba tare da ka ankara ba ko sani ma a lokacin da ta wuce?

Ana cewa rayuwa na farawa ne daga shekara 40, ko kuma wai shekara 60 ita ce sabuwar 50 ta yanzu, to amma menene gaskiyar lamarin? Wace shekara ce ganiyar mutum?

BBC ta bincika litattafai da rubuce-rubucen masana kimiyya a fannin lafiya, domin duba yadda lafiya da rayuwarka ke sauyawa kama daga karfin haddarka zuwa sha'awa da karfinka na jima'i. Kuma mun yi mamakin abubuwan da muka gano.

Mu duba lafiyar jiki

Hakkin mallakar hoto NIgel Hawtin

Abubuwan da ke bukatar kuzari cikin gaggawa kamar wasan tseren mita dari ko jifan dalma ko mashi shekara 20 da wani abu ne farkon ganiya, tun da bayan wannan lokaci mutum ya ke saurin dusashewa ko ja da baya a irin wadannan wasanni.

Su kuwa masu wasan kwallon kafa suna fara cin moriyar ganiyarsu ne tun kafin shekara 20 din ne.

Duk da haka kuma akwai wasannin motsa jikin da suka fi dacewa da wadanda ke da yawan shekaru, wasannin da suka fi bukatar juriya kamar na gasar gudun yada-kanin-wani ta nisan kilomita 100 ko kilomita 1000 da makamantansu.

A irin wadannan wasannin ko da mutum ya kai sama da shekara 30 ko 40, a hankali yake ja da baya ba lokaci daya kwatsam ba.

Misali 'yar gasar tseren keke ta Amurka Sunny McKee, ta yi bikin cika shekararta 61 ta hanyar shiga gasar kashi uku ta tseren kilomita 180 a keke da gudu da kafa, da kuma gasar ninkaya ta kilomita hudu.

'Yan wasa da dama sukan yi sha'awar wadannan wasanni masu wahalar gaske har a lokacin da suka wuce shekara 70.

Hakkin mallakar hoto NIgel Hawtin

Idan ka wuce shekara 20 da wani abu to ta karfin haddarka ya wuce. A gaskiya ma za a iya cewa ta fara dusashewa tun a lokacin da ka gama makaranta.

Kokarinmu na haddace abubuwa su dade a kanmu yakan dan fara raguwa a lokacin da muka kai sheakar 40 da wani abu.

Haka kuma ma za ka iya wuce lokacin da ka fi kaifin basira a wannan lokaci, domin yawancin abubuwan basira da mutane suke samun kyautar lambar bajinta ta Nobel, suna yin su ne a kusan lokacin da suke shekara 40.

Kuma a lokacin da muka wuce shekara 40,a wannan lokacin ne hatta halittar da ke kwakwalwarmu wadda ke sa kwakwalwar sauri wajen tunawa da sarrafa bayanai ta ke fara rauni, wanda hakan ke sa ta rage sauri gaba daya.

Duk da haka akwai kyakkyawan fata

Hakkin mallakar hoto NIgel Hawtin

Basirarmu na hawa da sauka ne

Duk da cewa mutum ya kai wannan matsayi da yake samun koma baya a basirarsa idan ya kai wannan lokaci, to amma kuma wasu abubuwan nasa sukan bunkasa a lokacin bayan sun ja baya.

Misali lissafi da karatu domin fahimta, duk suna kara habaka har lokacin da mutum ya kai munzalin shekarunsa na 40 zuwa 60. Hatta tunaninmu kan mu'amulla da da jama'a ya kan bunkasa a gaba. A takaice dai tunaninmu da basira ya kan ragu kuma ya karu ta fannin bunkasa a wannan lokaci.

''Babu wani lokaci a shekarunmu da za a ce mun kai ganiyarmu a wani abu ko kuma a yawancin abubuwa,'' in ji Josh Hartshorne na Jami'ar Harvard wanda ya gudanar da yawancin binciken.

Hatta karfin sha'awarka ta jima'i ma za ta iya karuwa

Hakkin mallakar hoto nigel hawtin
Image caption Kashi 30 cikin dari na masu shekara 65 zuwa74 na jima'i akalla sau daya a mako.

Idan za mu yarda da fina-finan da muke kallo a gidajenmu za mu yi amanna cewa shekarunmu na tsakanin sama da 20 zuwa sama da 30 wani lokaci ne na karfin jima'i ga mutum.

A gaskiya ma babu wani abu walau karfi ko sha'awar jima'in mutum da ke raguwa har sai ya zarce shekaru hamsin sosai.

Hatta a wannan lokacin ma, raguwar ba tana kasancewa ba ne gaba daya a lokaci guda.

Kamar yadda aka gabatar da wata kasida da ke magana a kan wa'adin lokacin karfin jima'in mutum, hatta mazan da suka kai shekara 55 a yau za su iya sa ran wasu shekaru 15 ko kusa da haka na iya yin jima'i a kai a kai.

Su kuma mata da wannan munzalin shekaru za su iya sa ran karin wasu shekaru sama da goma da iya jima'in su ma.

Ko da ike dai jima'in ba lalle ya kasance da armashi da kuma kuzari kamar yadda aka saba yi ba a da, amma kamar yadda wannan bincike ya nuna kashi 30 cikin dari na mutanen da suke da lafiya masu shekara 65 zuwa 74 suna jin dadin jima'i akalla sau daya a mako.

Kuma ma wani abu shi ne, yayin da mutum yake rasa sha'awa da kuzarin jima'insa sai kuma ya rika jin dadin rayuwarsa a lokacin yana karuwa.

Wannan wani abin mamaki ne ganin yadda tsufa ke tattare da laulayi na ciwon jiki da wasu matsaloli nan da can.

Amma ana ganin hakan na kasancewa ne saboda a lokacin mutum ya san yadda zai iya tunkarar duk wani tunani na damuwa bayan fadi-tashi da gwagwarmayar shekara da shekarun baya.

To me za mu iya cewa wannan bayanin gaba daya ya nuna mana?

A takaice za ka iya cewa ganiyarka ta jima'i ita ce shekara 20 da wani abu, yayin da kake bakin munzalin karfinka a shekara 30 da dori, zurfin tunaninka ya kai karshe a tsakanin shekara 40 zuwa sama da 50, shi kuma lokacinka na ganiyar farin ciki yake a shekara 60 da wani abu.

Sai dai wannan duka kididdiga ce da ta shafi yawancin mutane, saboda ba lalle hakan ya kasance a gare ka ba.

Wani abu mafi muhimmanci ma shi ne yadda muka san cewa kowane mutum da yadda shekaru suke zuwa masa wato daidai wuya daidai dadi, babu wani lokaci takamaimai da za a ce ka cimma ganiyar rayuwarka.

Sirrin farfadowa? Dabarar na bukatar kwazo;

Dadin labarin dai shi ne wasu daga cikin matsalolin da ke tattare da tsufa ba wai abubuwa ne da suka zamma lalle ba za a iya kauce musu ba kamar yadda wataki ka dauka.

Motsa jiki abu ne da ke kara karfafa jiki da yaki da cutuka daban daban da suka hada da cutar sukari da ta daji.Haka kuma yana taimakawa wajen kara karfin kwakwalwar da ta yi rauni. Mutanen da suke da lafiya kuma suna samun karin kusan shekaru biyar na jin dadin jima'i a karshen rayuwarsu.

Masana tunanin dan-adam ma sun gano cewa halayya da tunaninmu za su iya taka muhimmiyar rawa fiye da yadda za mu yi tsammani.

Wasu mutane sukan ce suna jin yarinya kamar ba su kai shekarunsu ba, wanda hakan ka iya sa su rika jin kuriciya a zuciyarsu kuma hakan ya sa su kara tsawon rai. A takaice dai wasu abubuwan na tsufa mutum ne ke dora wa kansa amma ba jikinsa ne ke yinsu ba.

Ba abin da zai taimaka mana mu dawo da kanmu matasa bayan mun tsufa to amma sanin yadda girma kan kasance da kuma yadda da kalubale da dadin da ke tattare da shi akalla zai sa mu ji dadin gangarar. Watakila a gaba mu gamu da wani tudun da za mu kara hawa na cin moriyar tafiyar.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi to latsa nan What's the prime of your life?