Yabo abu ne mai kyau ko maras kyau ga yara?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Mun dauka cewa gaya wa yara kalmomi masu karfafa zuciya na sa su kara kwazo. Amma idan ka bincika za ka ga cewa wannan ba abu ba ne na sha-yanzu-magani-yanzu. Abu ne da ya dogara ga irin kalmomin da ka yi amfani da su in ji Claudia Hammond.

Danka ne ya kawo maka wani zane na mutum da dogayen kafafu sirara, amma ba gangar jiki ga kai da gashi duguzunzun. Can a gefe daya kuma ga wani abu mai launin rawaya wanda ya ce ma rana ce. Zanen dai ga shi nan kawai. Dan naka yana sauraron ya ji abin da za ka ce masa game da wannan zane, me za ka ce?

''Kai wannan ya yi kyau sosai. Zane ne da ban taba ganin mai kyawunsa ba. Komai ya yi daidai.''

Dan naka yana cike da farin ciki yayin da ya manna zanen a wani wuri a daki yana jiran sauran 'yan gidan su gani su ma.

Matsalar ita ce ba wai yabon ba ne bai dace ba, a'a, abin da ake gudu shi ne amfani da kalmomin da suka wuce kima ko na karin gishiri da za ka kambama yaro.

Iyaye na iya kambama kwazon dansu, musamman idan dan ba shi da karfin hali da zummar cewa hakan zai sa ya samu kwarin gwiwa.

To amma abin tsoron shi ne, hakan na iya haifar da abin da ba a so. Domin an san cewa, idan aka ziga ganga sai ta fashe.

Kamar mutum ne a yi ta zuga shi ana cewa wane ya koshi, sai yake ta hura cikinsa, ka san cewa a karshe sai yunwa ta kai shi kasa.

Babbar matsalar da ke tattare da koda kwazon yaro, ita ce, kamar yadda bincike ya nuna za ka iya sa yaron ya kauce wa wani kalubale da zai fuskanta a gaba, domin gudun ka da ya yi abin da bai kai wancan da ya yi ka zuzuta kwazonsa ba, wanda idan hakan ta kasance yana ganin abin kunya ne a wurinsa, saboda haka sai ya yi kokarin kauce masa.

To amma idan ba ka zake ba wurin yabon kwazon dan naka, misali, lokacin da ya nuna maka wannan zane da ya yi, sai kawai kace masa, ''wannan ya yi kyau.'' Kalma daya kawai za ta iya sa bambanci, wato ba ka ce, 'sosai' ba.

A nan masana na ganin idan ka yaba masa sosai da sosai, to kamar kana tsammanin idan zai yi wani abu makamancin wannan a nan gaba ya yi wanda ya fi wannan na yanzu. Ko da yake dai babu wata jarrabawa da aka yi wa wannan bincike.

To yanzu yaya ya kamata ka yaba wa danka idan ya yi wani abu?

Jagoran marubuta wannan kasida kuma masani kan tunanin dan-adam, Eddie Brummelman, ya shawarce ka da ka dan ja baya , ka da ka zake, ka yi tunanin irin yabon da za ka yi wa yaro wanda ba zai sa ya yi fargabar ka sa kaiwa kamarsa a can gaba ba.

Abubuwan da ka yi amfani da su wajen yabon za su iya yin tasiri;

Bayan shekaru 20 da ta yi tana bincike Farfesa Carole Dweck ta Jami'ar Stanford, ta gano babban bambanci tsakanin yaba wa yara a kan kokarinsu (misali ka gaya musu yadda suke da basira) da kuma yaba musu saboda irin jajircewar da suka nuna (misali ka ce musu sun yi aiki tukuru lalle).

A wani binciken gwaji da aka yi an gano cewa, idan aka yaba wa yara a kan aikin da suka yi tukuru ko kuma a kan dabarar da suka nuna a abin da suka yi, yaran masu 'dabara'(wadanda aka yaba wa saboda dabararsu) sun fi taka tsantsan, domin a gaba sai suka zabi abin da suka san za su iya yi kuma sun fi damuwa idan suka kasa yi.

Amma yaba wa yaro a kan basirarsa abu ne da zai iya sa ya tsaya a inda ka san shi, wato abu ne da zai sa yaron ya rika kaffa-kaffa da yin duk wani abu da zai sa ka ga kamar bai kai matsayin da ka san shi ba.

A saboda haka Farfesa Dweck, ta bayar da shawarar mayar da hankali kan yabon hanyar da yaron ya bi ya yi wannan abu maimakon jinjina masa a kan basirarsa.

Misali ka ce masa,'' gaskiya na ji dadin yadda ka mayar da hankali a kan haka,''

Idan ya kuskure a wurin yin abin, sai a ba shi kwarin gwiwa wajen gyara masa, ta yadda zai koyi yadda zai gyara matsalar.

Amma fa wannan ya dogara ga shekarun yaron. Kamar yaran da ba su fara zuwa makaranta ba duk irin yabon da ka yi musu ba matsala, yana karfafa musu gwiwa, amma idan suka kara shekaru to sai an kiyaye da irin yabon da za a yi musu.

Masaniyar tunanin dan-adam, Jennifer Henderlong Corpus, ta ba wa yara 'yan shekara tara zuwa 11 wata jarrabawa.

A sakamakon da suka samu, ko dai ta yaba musu kan halinsu (character), ko ta yadda suka bullo wa aikin ko kuma ma ta ki yaba musu gaba daya wato ta yi shiru.

Daga nan kuma sai ta tsara wata jarrabawar ta yadda za su fadi, kafin ta duba abin da za su yi a gaba kuma.

Sai ta ga cewa wadanda ta yaba musu kan halinsu ba su ji dadin yadda suka fadi ba, abin ya sa gwiwarsu ta yi sanyi wato bai ba su kwarin gwiwa ba.

Amma wadanda aka yaba wa kan yadda suka bullo wa aikin, sun yi ta kokari da jajircewa sai sun yi shi.

Gogayya:

Ya kuma maganar nuna wa yaran cewa sun yi kokari fiye da sauran takwarorinsu?

Za ka dauka cewa ba abin da muke so mu ji kamar cewa mun fi kowa kokari, to amma, a nan ma nazarin ya nuna abin ba haka yake da sauki ba.

Nazari irin wannan da aka yi a tsakanin manya a shekarun 1970 zuwa 1980 sun nuna cewa wannan yabo yana karfafa jin dadi da farin cikin da mutane suke samu daga yin aikin shi kansa wanda kuma kwarin gwiwa ne sosai.

Amma kuma kusan lamarin ba haka yake ba a wurin yara. Domin an bai wa yara masu shekara tara zuwa 11 wata jarrabawa, wadda bayan da suka kammala, an yi musu yabo iri daban daban.

Wasu an ce musu, ''Wannan aiki ne mai kyau! Kamar kun fi sauran yara da yawa kokari!''

Wasu an yaba musu a irin cigaban da suka yi da cewa misali, ''Aiki mai kyau! Lalle kam kun koyi yadda ake wannan aiki!''

Daga nan ne kuma sai aka ba su wata jarrabawar ta daban, a wannan karon ta yin zane, amma kuma babu wani sakamako da aka ba su na yabo bayan sun kammala, saboda haka ba su da tabbaci kan kokari ko akasin hakan da suka yi kafin su zabi wani aikin tsakanin mai sauki da mai wahala wanda kuma za a tambaye su ko abu ne mai dadi ka yi aiki tukuru.

Sun gano cewa yabon da ya kunshi cewa ka fi wani kokari gara ma a ce ba a yi maka shi ba ma gaba daya, saboda illar da yake sa ka ciki.

Domin yana rage maka karfin hali na tunkarar wani aiki mai wuya domin ka da ka kasa yi a ga cewa ka dawo baya, a don haka ko da yaushe sai ka yi kokarin kaucewa aikin da yake cike da kalubale.

Amma wannan yana kasancewa ne idan ba su san yadda suka yi kokari ko matsayinsu a aikin da aka ba su a baya ba ne.

A lokacin da aka riga aka ba su sakamakonsu maza da matan sun ji daban wato sai yanayinsu ya sauya.

Mazan sun amfana da yabon da aka yi musu, cewa kun fi takwarorinku kokari, amma kuma su matan ba su amfana ba.

Wannan yabo ya sa mazan sun kara dagewa a jarrabawa ta gaba, yayin da su kuma matan sai suka dauka cewa, fin takwarorinsu abu ne da shi kadai ya isa, maimakon ya zamar musu wani kwarin gwiwa don cimma wani matakin ko wata gamsuwar daga aikin da aka sake ba su, hakan ya sa kwarin gwiwarsu ya ragu.

Amma fa ka sani cewa wannan nazarin da aka yi, abu ne da ya shafi yadda yabo yake shafar yara a gajeren lokaci amma ba a lokaci mai tsawo ba.

Shi tasirin yabon da zai shafi dogon lokaci zai kasance ya fi wahala a gudanar, domin dole ne ka samu tabbacin cewa duk wani uba ko babba ga yabon da yake yi wa dan nasa ko yaro wanda ya dace ne na tsawon shekaru.

Duk da haka shawarar da muke bayarwa ita ce yaba wa yara a kan kwazonsu da kuma yadda suka tunkari yin aiki na ba su kwarin gwiwa.

Kuma idan kana yaba musu ne saboda sakamakon da suka samu, to sai a ce yabo ne da za a iya cewa ba zai taba yawa ba. Amma ka kwana da sanin cewa yabo idan ya yi yawa zai iya haifar da koma baya.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Is praising a child good or bad for them?