Ko farin wata na sa mutane hauka?

Akwai maganganu masu kama da camfi da almara da yawa da suka danganci farin wata inda har wasu mutanen ma ke ganin cikakken wata yana iya jawo wa wasu hauka.

Claudia Hammond ta duba yadda kimiyya ke kallon wasu daga cikin wadannan maganganu.

A wasu al'adun ana daukar lokacin da wata cikakke ya bayyana da cewa lokaci ne na bayyanar dodanni da fatalwa da kuma wasu matsaloli.

Kuma a wasu wuraren mutane sun yi amanna a wannan lokaci watan yana sa wasu hauka.

Ka tambayi wasu 'yan sanda ko ma'aikatan sashen bayar da kulawar gaggawa na asibiti, wasunsu za su kafe maka cewa an fi samun hatsari da rikici mai tsanani da ke kai ga raunata mutane da kuma yawan masu tabin hankali idan aka ce cikakken wata ya bayyana a sama.

A shekara ta 2007 hukumar 'yan sandan Biritaniya a yankin shakatwa na Brighton, sai da ta kara daukar 'yan sanda aiki a lokacin fitar cikakken wata.

Hakkin mallakar hoto AP

Tasirin wata a dabi'unmu ba shakka abu ne da mutane da yawa suka yarda da shi.

Ba maganar tatsuniya ko wata sheda ta al'ada ko almara ba, wannan magana ce da aka mayar da hankali wajen gudanar da daruruwan bincike a kanta.

A bazarar 2013 an gudanar da wani sabon bincike, wanda ya gano cewa mutanen da suke kwana a dakin bincike sun ce barcinsu ya ragu da kashi 15 cikin dari a lokacin cikakken wata.

Wannan kuma duk da cewa ba sa ganin watan a fili ko ma wani haske na watan a dakin da suke, kuma suka ce suna daukar akalla minti biyar kafin barci ya dauke su akan yadda suka saba.

Wannan nazarin ya dauki hankalin mutane da dama duk da cewa mutane 33 ne kawai aka gudanar da binciken da su, kuma hatta su kansu wadanda suka gudanar da shi suna kaffa-kaffa wurin dogaro da sakamakon.

Hada sakamakon bincike daban-daban wuri guda a yi nazari a kansu, wata hanya ce ta kokarin sanin ainahin gaskiyar lamari.

Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu masana tunanin dan-adam na Amurka James Rotton da Ivan Kelly sun dauki wannan tsari a 1985, suka hada sakamakon bincike har 37 na tasirin cikakken farin watan.

A karshe suka ayyana cewa babu wata alaka tsakanin farin watan da yawan tabin hankali da kisan kai da hadarin mota da miyagun abubuwa da sauran laifuka da ake yi a lokacinsa.

Da masanan suka gudanar da nazarinsu a kan wadannan bincike-binciken da suka danganta farin watan da wadannan abubuwa sai suka gano cewa lokacin watan ya yi daidai ne da lokacin wani hutu ko karshen mako wadanda daman lokuta ne da abubuwa marassa dadi ke aukuwa.

Duk binciken da suka ga ya nuna cewa an samu matsaloli da yawa a lokacin da farin watan ya fito cikakke, sai wani binciken kuma ya nuna an samu matsaloli kadan.

Roton da Kelly sun ga ce idan ka yi kokarin amfani da wadannan alkaluma domin hasashen halayyar mutane sai su ga alakar tana da raunin madogara.

Tun daga wannan lokaci an gudanar da tarin karin bincike daban-daban wadanda ke nuna sakamakon da ke karo da juna.

Wani nazari da aka yi a 1992 na wasu tarin bincike har guda 20 a kan dangantakar bayyanar cikakken farin watan da yawan mutanen da ke tunanin kashe kansu, ya ayyana cewa babu wata shedar alaka tsakaninsu.

Haka kuma a wannan karon ma, masu nazarin da suke cewa akwai alaka tsakaninsu sun kasa yin la'akari da cewa hakan na kasancewa ne a wani lokaci na hutu a mako.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu sayar da furanni a lokacin shirye-shiryen bikin ibadar cikakken wata ta addinin Buddha a Sri Lanka

Wata matsala da ke kara karfafa wa masu yarda da tasirin farin watan, ita ce ta yadda mujallu za su fi karbar binciken da aka yi aka ga alakar domin wallafawa fiye da na wadanda ba a samu alakar ba.

A dangane da wannan ba wanda zai iya cewa ya san yawan binciken da aka yi wanda ba a ga wata dangantaka tsakanin matsalolin ba, wanda kuma mujallu ba su karba sun wallafa sakamakon ba.

Akwai kuma maganar yadda farin watan zai iya tasiri a dabi'armu. Wani nazari shi ne na yadda watan yake shafar igiyar ruwa, haka yake yi a kan ruwan cikin jikinmu.

To amma a nan kuma ai wata bai kai girman duniyarmu ba. Saboda haka karfin maganadisunsa na ja ko danna abu (gravitational force) bai kai na duniya ba.

Kuma ma ai idan har hakan na da tasiri ai wannan karfi nasa zai kasance ba wani bambanci ko watan yana cikakke ne ko kuma sabo ne.

Wasu kuma suka ce, a'a ai hasken farin watan ne yake tasiri a kan mutane. Amma su kuma ba su ga cewa haskensa kusan daya bisa uku ne kawai na kyandir ba a kusa da mutum.

Cizon dabbobi

To amma ina kuma maganar yawan samun matsalar da dabbobi ke cizon mutane a lokacin bayyanar cikakken farin watan?

A wani lokaci da likitoci suka tattara bayanai na shekara biyu a asibitin Bradford da ke arewacin Ingila, sai suka ga an samu karin mutanen da kare ko bera ko kyanwa ko kuma doki ya ciza linki biyu a lokacin da farin wata ya bayyana gaba daya fiye da a lokacin da yake sabo.

Abin da ba mu sani ba shi ne mai ya sa hakan? Kuma ma shin wannan cizon na faruwa da daddare ma?

Ana ganin cikakken farin watan ba lalle ba ne shi yake tasiri a kan dabi'ar dabbobin kai tsaye ba, sai dai kwarin da ke shan jinin dabbobin ne suke sa su haka.

Haka kuma a mujallar da aka wallafa bayanin asibitin Bradford din, masu binciken da suka yi nazarin bayanan marassa lafiyar da aka kai asibitocin Australiya saboda cizon kare a cikin watanni 12 sun gano cewa idan an kiyaye da ranar makon da dabbar ta ciji mutum sai a ga ba lalle ma ranar an samu cikakken farin watan ya fito ba.

Hakkin mallakar hoto Fedor Bystrov

To idan shedar da ake da ita da danganta duk wani abu maras kyau da farin watan cikakke ba ta da wani karfi, me ya sa ke nan mutane da yawa suka yarda cewa abu ne na gaskiya?

Hakan zai iya zama misali na yadda mutane ke yarda tare da tuna duk wani abu da ya zo daidai da abin da suka riga suka yi imani da shi.

A wani dare sai kawai 'yan sanda ko ma'aikatan asibiti suka duba suka ga gari ya yi haske sosai, sai suka ga cikakken farin wata.

Daga nan sai kawai su danganta yawan abubuwan da suke gani na faruwa na aikinsu da wannan dare.

Amma kuma fa ba lalle ba ne idan watan yana sabo su lura da cewa sabo ne ko su danganta abubuwan da ke faruwa da watan.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alamar nuna muhimmancin cikakken farin wata

To yaya wannan al'ada ta kaka da kakanni ta samo asali ne ma tun da farko?

Wani bayani mai ban sha'awa da ake yi a nan shi ne, can a lokacin da, da babu wutar lantarki ko fitulun da ake sanya wa waje, daga nan ne abin ya samo asali, saboda mutanen da ba su da gidaje, suke kwana a waje wadanda kuma suke iya kamuwa da larurar tabin hankali ko farfadiya larurar na iya taso musu idan hasken watan ya hana su barci a lokacin da yake cikakke.

Wasu kuma na ganin tasirin cikakken watan na kasancewa ne a kan wasu mutanen, saboda haka ba abin mamaki ba ne, binciken da ake gudanarwa kan jama'a baki daya yawanci ba ya tasiri.

Suka ce hanyar da ta fi dacewa ita ce a gudanar da binciken a kan daidaikun mutanen da ke cewa abin na faruwa a kansu.

Wa ya sani ko watakila ma wannan dabara ta nuna cikakken farin wata ya iya bayyana wata mummunar dabi'ar wasunmu ta boye.

Amma dai a halin yanzu ga wadanda suke da sha'awar nazari mai sauki kan shedun da ake da su kan wadannan abubuwa masu kama da almara sai a ce tunani ne da ke da wuyar tabbatar da wani abin dogaro.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Does a full moon make people mad?