Fasahar da ake sanyawa a jiki: Wa ya fi ka sanin sirrin jikinka?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Sabbin kayan fasaha na yau ka iya bin diddigin bayanai a kanka game da abin da ya shafi harkar jima'inka da rashin lafiyarka da sauran abubuwa da ka bar wa birnin zuciyarka (sirri), amma bisa rashin saninka za ka iya bayyana wa irin wadannan kayayyaki sirrin naka fiye da yadda ka ke tsammani, in ji Jacob Ward.

Jeff ya fara jima'i da karfe biyu na rana, inda ya kai 'yan sa'oi yana yi, kuma a sanadiyyar hakan nauyin jikinsa ya ragu ma'ana maikon jikinsa ya ragu( 347 calories).

Mun san cewa saboda wannan bayani ko kididdiga na nan a intanet ga kowa amma ba mu san ko shi Jeff ya san hakan ba.

Hakkin mallakar hoto Getty

Jeff yana sanye da wani awarwaron roba a wuyan hannunsa da ake kira Fitbit, wanda ke aiki da intanet, kuma yake kididdigar yawan motsa jikin mutum ta yadda za ka iya sanin nauyinsa da ya ragu.

A shekara ta 2011 an sanya wadannan alkaluma a rumbunan bayanai na intanet, wanda hakan ya sa duk wanda ke daura wannan abu a hannunsa kuma ya dauki jima'in da yake yi a matsayin motsa jiki, to a takaice yana yada wa duniya wannan bayani ne.

Duk da cewa kamfanin wannan awarwaron roba na Fitbit ya yi saurin cire wadannan bayanai na sirri daga intanet, lamarin ya zama misali na gargadin mutane su san cewa duk wani bayani na aikin jikinsu da suke sanyawa a intanet zai iya haifar musu da matsala da ba su yi tsammani ba.

Da yawa daga cikin kayan sanyawa ko wadanda ake daurawa a jiki masu dauke da fasaha a yau, suna daukar bayanai kan misali, nauyinka da abin da kake ci da bayanin irin damar jikinka ta samar da 'ya'ya.

Kuma abin takaicin shi ne yawancin wadannan bayanai za a iya yada su a shafukan sada zumunta da muhawara na intanet da kake mu'amulla da su da likitoci da kamfanoni ko ma mutanen da ba ka san su ba samsam.

Duk da cewa akwai alfanu da dama da ake nunawa a tattare da sanya muhimman bayananka a intanet, tambayar ita ce nawa daga cikin yawan sirrin jikinka kake so a sani?

Hakkin mallakar hoto Getty

Daya daga cikin mutanen da suka fara sanya bayanan duk abubuwan da suke yi a kullum a intanet shi ne Steve Mann.

Mann wanda ake dauka a matsayin wanda ya fara kirkiro 'yan na'urorin kwamfuta da ake daurawa a jiki, ya samar da kwamfutoci da ake goyawa a baya a shekarun 1980, wadanda suka hada da na'urar daukan hoton bidiyo da dan gilashi mai kamar fuskar talabijin da yake daurawa a gefen idonsa daya yana ganin hotunan, wanda ake ganin kamar masomin tabaran Google ke nan.

Zuwa tsakiyar shekarun 1990, Mann ya kirkiro 'yar karamar na'urar daukar hoto wadda yake daurawa a jikinsa a ko da yaushe ba tare da ya cire ta ba.

Da wannan na'ura yake watsa duk abubuwan da yake yi a kullum kuma a kowane lokaci ta intanet.

An ga amfanin wannan na'ura tasa ne bayan da ya dauki hoton bidiyon yadda wani mai mota ya kade mutum kuma ya gude, inda aka yi amfani da wannan hoto aka gano mai motar.

Kirkire-kirkiren Mann, sun mayar da hankali ne a kan yadda zai yi mu'amulla da duniya, amma kuma ainahin manufar daura kayyakin fasaha a jiki tare da yada su a intanet ya bude hanyar samar da na'urorin da ke bin diddigin ayyukan jikinka kafin bayyana su a duniya.

Misali abubuwan daurawa a hannu masu na'ura kamar Fitbit da FuelBand na kamfanin Nike suna nadar motsin mutum ne sannan kuma su aika da bayanan zuwa shafin intanet ta yadda mutum zai san yawan nauyin da yake ragewa da sauransu.

Wasu mutanen sukan sanya wadannan bayanai nasu a shafin Facebook ko kuma wasu shafukan na intanet.

Wasu da dama sukan ce wai hakan na taimaka musu wajen inganta lafiyarsu da kuzarinsu.

Abubuwan da ake daurawa a jiki na fasaha za su iya taimaka mana wajen sani halin da jikimu ke ciki ta wasu hanyoyin daban.

Irin wadannan na'urori sun kara tsuke duniya, sun rage girmanta ga mutanen da suke da rashin lafiya mai tsanani.

Misali mutanen da ke da cutar sukari, wannan na'ura tana taimaka musu ta yadda likitansu ke sanin yanayin da sukarin nasu yake a duk lokaci.

Akwai kuma wata na'ura da ake kira Duofertility, wadda idan mace tana daura ta, likitanta zai iya sanin ranar da take da dama sosai ta daukar ciki, da haka kuma zai ba ta shawara kan lokacin da ya fi dacewa ta samu juna biyun.

Kamfanin da ya yi wannan 'yar na'ura ya ce a jarraba ta da aka yi an samu nasara daya da makamanciyarta ta IVF, wadda za ta iya fin ta su tsada.

Wasu suna ganin nan gaba ma bayananmu da muke yadawa ta intanet sai sun fi na yanzu yawa.

Wasu masu bincike sun wallafa a mujallar harkokin lafiya ta Journal of Medical Internet Research cewa suna ganin nan gaba mutane za su rika amfani da wadannan na'urori su rika tattara bayanai da kuma gane irin larurar da ke tare da su.

Daman tuni an rigaya an samu irin wadannan shafuka ma kamar su PatientsLikeMe da CrowdMed, wadanda suke ba mutane dama su yi musayar bayanai game da larurarsu.

Shafin PatientsLikeMe tuni ma har ya fara tattara bayanai daga irin wadannan 'yan na'urori da mutane ke daurawa a jikinsu da makamantansu.

Nan gaba ta hanyar tattara bayanan ayyukan jikinmu a intanet za mu iya samun ilimi daga tarin jama'a domin gano cutuka masu wuyar sha'ani ko fahimta.

Amma kuma akwai hadarin da ke tattare da wannan cigaba, musamman idan mutun ya bayyana fiye da abin da ya yi niyyar bayyanawa.

Wanene ya kamata ya samu bayanan jikinka?

Misali ya kake ganin irin dadin da kamfanin inshorar lafiya zai ji, idan ya gano bayanan mutumin da yake amfani da inshorarsa kan zirga-zirgarsa da yanayin jima'insa da na cin abinci ko kuma yanayin shan magani ko miyagun kwayoyi da yake ta'ammali da su?

Ko kuma ma kana wani wasan motsa jiki mai hadarin gaske? Ya yawan jan naman (naman shanu ko tumaki ko awaki da sauransu) da ka ci a makon da ya gabata yake? Abokan jima'i nawa kake da ko kike da.

Kamfanin inshorar da yake da irin wannan tarin bayani a kanka zai iya karbar kudi da yawa a wurinka ko ma ya ki karbarka.

Wannan shi ya sa ma wasu mutanen suke nuna damuwa cewa kamfanonin inshorarsu suna sakaci da bayanansu na lafiya.

Wannan ne ya sa tsarin kula da lafiya na tarayya na Birtaniya ya jinkirta shirin bayar da takaitattun bayanan maras lafiya a wani rumbun bayanai na intanet.

Wani abu kuma da ake taka tsantsan game da amfani da wadannan na'urori kanana na daurawa a jiki shi ne. Ba mutumin da yake rayuwa shi kadai. Ma'ana kwayoyin halittarka iri daya ne da na 'ya'yanka da iyayenka.

To za ka ga wasu mutanen a yanzu suna bayyana yanayin kwayoyin halittarsu da wasu ta shafukan intanet na 'yan uwa da kuma a wasu taruka.

To kuma za ta iya kasancewa hakan ba zai yi wa wani danginsu dadi ba domin watakila shi ba ya son a san wannan yanayi na kwayar halittarsa.

Kamar yadda marubuciya a kan harkokin kimiyya Virginia Hughes ta rubuta: ''Lalubo yanayin kwayar halittar gadonku na iya kasancewa abin bansha'awa.

...Amma kuma fasahar yin hakan za ta iya tono wasu abubuwa na sirri kamar kwartanci da bayar da gudummawar mani da wadanda suke ba danginka ba wato 'ya'yan riko ne (allura ta tono garma). Ba a taba samun lokacin da sirrin iyali ya zama cikin rauni ba kamar yanzu.''

Watsa bayanan aikin jikinka a shafin intanet shakka babu zai iya kasance dayan biyu ko dai alheri ko kuma hadari.

Amfani da kuma ribar wannan fasaha ka iya inganta lafiyarmu sosai da kuma sa mu farin ciki, amma kuma dole ne mu yarda cewa sirrin jikinmu ya bayyana yadda bai taba bayyan ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Wearable technology: Who knows your body's secrets?