Hanyar da aka fi gane mai karya

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Manta da maganar kallon idon mutum ko fuskarsa ko yanayin takunsa akwai hanyoyin gane mayaudari da suka fi wadannan.

David Robinson zai yi mana bayani:

Ayarin Thomas Ormerod da jami'an tsaro sun gamu da aiki mai dan karen wuya da za a iya cewa ma ba zai yuwu ba.

An dai ba su aikin ganawa da matafiya ne a fadin filayen jiragen sama na kasashen Turai, inda za su tambayi matafiyi tarihinsa da kuma inda za shi da abin da zai yi a inda za shi.

Ormerod ya cakuda matafiyan da wasu na bogi, kuma aikin ayarin mutanen nasa ne ya gano wadannan matafiya na karya.

Yadda ya yi shi ne kusan mutum daya daga cikin matafiya 1000 karya zai gaya musu.

Idan ka duba wannan za ka ga ai gano wannan matafiyi na bogi kamar neman allura ne a teku.

To ya suka tunkari wannan jan aiki? Wata hanya ta yin wannan gagarumin aiki ita ce ta nazarin takun mutum ko idonsa ko? To lalle kam, idan kana ganin hakan ya dace sai in ce ka kama kafar wala.

Saboda tarin binciken da aka yi na amfani da wadannann hanyoyi na gano makaryata, ba sosai ake samun nasara ba.

Hatta wandanda kwararrun 'yan sanda suka yi ma, kawai kamar sa'a ce kawai.

Wani binciken ma ya nuna masu irin wannan bincike 50 ne kawai daga cikin 20,000 suka yi nasara. Su ma kuma nasarar kashi 80 ne cikin dari wato ba dari bisa dari ba. Wasu ma canke ne kawai suke yi.

Wadannan masu bincike na ayarin Omerod sun jarraba wata hanya ce daban, kuma sun yi nasarar gano yawancin matafiyan na karya.

Kana son sanin wannan sirri nasu? Hanyar ita ce ka yi watsi da yawancin dabaru da hanyoyin da ake amfani da su na gano yaudara a maimakonsu ka kama wasu hanyoyin da kusan na kaitsaye ne kawai.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption idan ana maganar gane makaryaci ne ka da ma ka yi maganar kallon idon mutum

A cikin shekarun da suka gabata, bincike ya nuna hanyoyin da ake bi wajen gano mayaudara, ba sa bayar da sakamakon da ake bukata.

Yawancin hanyoyin da ake amfani da su, wadanda suka danganci nazarin yanayin takun mutum ne da yanayin fuskarsa, kamar yanayin motsin kumatunsa da kiftawar idanuwansa da kuma dariyarsa.

Babban misali a nan shi ne, yadda Bill Clinton ya ke yawan taba hancinsa, a lokacin da yake musanta badalarsa da Monica Lewinsky.

A wannan lokacin an dauka a duk lokacin da yake hakan wata alama ce ta cewa karya yake yi.

Timothy Levine na Jami'ar Alabama da ke Birmingham ya ce, a duk lokacin da mutum zai yi karya idan aka sa shi a gaba, hakan na sa mutun wani yanayi mai karfi sosai da zai yi wuya ya iya hana kansa yi.

Kamar sanyin jiki ko fargaba ko kuma ma annashuwa da farin ciki, duk a kokarin yaudarar nuna cewa shi mai gaskiya ne.

Ko da mutum ya iya daure fuskarsa, wato bai yi wani abu da zai sa a iya gane cewa karya yake yi ba, zai iya aikata wani abin da daban da zai iya sa a gane shi.

Amma fa duk da haka babu wata alama takamaimai da za a iya dogaro da ita cewa tana tabbatar da mutum karya yake yi, saboda tarin yawan dabi'un dan-adam.

Sanayya ka iya sa ka san lokacin da mutum yake fadin gaskiya.

Amma kuma wasu mutanen sa iya yin sabanin hakan, domin babu wata fassara ta gaba daya da duniya ta yarda da ita a kan wata dabi'ar mutum.

Ormerod wanda ke Jami'ar Sussex, ya ce, ''babu wata dabi'a ko taku na mutum da za ka iya tabbatarwa cewa da zarar mutum ya aikata shi to alama ce ta karya.''

Ya kara dacewa '' Na kan kyalkyala dariya, wasu kuma sukan murtuke fuska, wasu suna yarda ku hada ido, wasu kuma ba sa yarda''

Levine ma ya amince da wannan magana inda ya ce: ''Sheda a bayyane take karara babu wata alama da ta bambanta wata dabi'a tsakanin gaskiya da karya''

Misali a ce idan mutum ya yi abu kaza to gaskiya yake amma idan ya yi kaza kuma karya yake.

Ko da yake za ka iya jin cewa wasunmu na cewa suna iya ganewa da wasu alamomin idan mutum yana karya, wasu masana na musanta wannan.

Duk da wannan sakamakon, har yanzu wadannan alamomi da ake ganin suna bayyana makaryaci abubuwan dogaro ne a wurinmu.

Mu duba tsarin da aka sa na tantance matafiya a filayen jirgin sama, tsarin da aka sa Oremond ya yi bincike a kai kafin wasan Olimfiks(Olympics) na 2012.

Ya ce a bisa ka'ida jami'an tsaro za su yi amfani da takarda mai tambayoyi da ke dauke da zabin e ko a'a akan niyyar matafiyi, kuma an horar da su, kan yadda za su kura da yanayi ko take-taken mutum a wannan lokaci.

Ta yadda za su gano wani yanayi nasa na nuna ko karya yake yi in ji Ormerod.

Y ce to amma ko shi wannan tsari na tattare da matsalar nuna san rai ko bambanci.

Domin jami'an tsaron za su iya nuna wariya a kan wasu kabilu ko jinsi.

Wanda wannan zai hana a gano mutumin da yake karya. In ji Ormerod.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba llalle ba ne jiki ya iya nuna cewa mutum karya yake yi

Wannan ya nuna cewa lallai akwai bukatar samun wani tsari na daban domin gano makaryaci.

To amma idan aka yi la'akari da 'yan nasarorin da aka samu a gwajin da aka yi na tsarin a dakunan bincike, wane tsari ke nan za a yi amfani da shi?

A nan amsar da Ormerod ya bayar mai sauki ce: a daina mayar da hankali kan yanayin mutum a lokacin da ake bincikensa, maimakon haka a rika nazari a kan kalmomi da maganganun da mutum ke furtawa.

Ormerod da abokin aikinsa Coral Dando na Jami'ar Wolverhampton sun zayyana wasu ka'idojin tattaunawa da za a iya amfani da su wadanda za su iya sa a gane makaryaci.

A rika amfani da tambaya mai bukatar bayani, inda ta hakan mutum zai yi ta yin magana har sai ya kama kansa ko ya jefa kansa inda za a kama shi.

A rika amfani da tsari na shammata, inda mai bincike zai tambayi mutum tambayar da bai yi tsammani ba, wadda za ta dan iya rudar da shi.

Misali ka mayar da shi baya ta hanyar nemansa ya yi maka bayanin wani abu da ya riga ya yi maganarsa a can baya, wanda hakan zai iya sa ya manta abin da ya gaya maka a can baya.

Ka rika lura da 'yan kananan bayanai da za a iya tabbatarwa ba tare da wata matsala ba.

Idan mutum ya ce maka ya yi karatu a Jami'ar Oxford, sai ka nemi ya ba ka bayani game da yadda ya fara aiki bayan ya gama karatu.

Idan ka gano wani abu na alamun karya a maganarsa, ka da ka nuna masa cewa ka gano hakan.

Yana da kyau ka bar shi ya ci gaba da samun kwarin gwiwa cewa ba a gano shi ba, ta yadda zai ci gaba da yi maka wasu karerayin.

Ka lura da sauyin karfin halinsa. Ka duba cikin natsuwa yadda jikin mai karya yake yin sanyi idan an jefa masa wata tambaya da ta kalubalance shi bayan bayanan da ya yi ta yi a baya idan ya fahimci an kama hanyar gano shi.

Manufar wannan tsari ita ce, tattaunawa tsakaninka da wanda kake gudanar da binciken a kansa, ba wai ka saka shi gaba kana ta yi masa tambayoyin ba.

Ta wadannan bayanan da yake ba ka ne cikin matsin da kake masa cikin ruwan sanyi zai kama kansa.

Inda zai fadi wata maganar da za ta saba da wata da ya fada a baya ko kuma ya rika yin kuskure a bayanan da yake yi na amsoshin.

Makaryaci da makaryaci Makaryaci ya fi saurin kama makaryaci. Wani abin mamaki shi ne mutumin da yake makaryaci ya fi iya kama makaryaci (mugu shi ya san makwantar mugu). Geoffrey Bird na Kwalejin Jami'ar Landan da abokan aikinsa sun gudanar da wani tsari na bincike, inda suka hada mutane da su ba da amsar e ko a'a a game da halayyar su kansu mutanen.

An kuma tambayi su mutanen da suka amsa jarrabawar ko aka yi gwajin a kansu, da su ba da amsa a kan gaskiyar abokan jarrabawarsu.

Daga nan sai aka gano cewa wadanda suka fi iya karya su ma za su iya karyar wasu, watakila saboda sun san hanyar da ake bi ayi.

Ormerond ya bayyana a fili cewa dabararsa ko tsarinsa na binciken kamar ya fi tasiri, domin an ga sakamakonsa a zahiri.

Wadanda suka yi gwajin dabarar ta Ormerond da Dando, inda aka cakuda matafiya na bogi cikin na gaskiya a filayen jiragen sama na kasashen Turai, wadanda suka yi amfani da tsarin tambaya sun fi yin nasara sama da kashi 20 cikin dari wajen iya gano matafiyan na bogi.

Fiye da wadanda suke amfani da tsarin lura da yanayi ko alamun fuska da ido da sauran yanayi na mutum.

Wannan nazari ya kayatar da Levine, wanda ba ya ma cikinsa, domin yana ganin yadda aka yi shi a yanayi na gaske a filayen jirgin sama hakan ya kara masa inganci.

''Wannan shi ne nazari mafi inganci da ake da shi ya zuwa yanzu'' in ji shi.

Ita ma hanyar gwaji ta gano makaryaci ta Levine ta bayar da gagarumin sakamako.

Kamar dabarar Ormerod, shi ma Levine yana ganin yin tambayoyi na dabara da aka tsara domin gano kura-kurai a maganar makaryaci nesa ba kusa ba ya fi dabarar lura da yanayin fuska da ido sauran halaye na mutum.

Wani gwaji da aka yi na dabarar ta Levine masu bincike sun yi nasara kashi 90 bisa dari wajen kano makaryata.

Wani mai binciken ma har nasara kashi 100 bisa 100 ya samu.

Hatta wadanda ba kwararrun masu bincike ba da aka sa su yin amfani da dabarar sun yi nasara kashi 80 bisa dari wajen gano masu karya.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ko 'yan sanda sun fi kowa iya gano makaryacin da ake zargi?

Sirrin wannan dabarar shi ne abu mai sauki da kwararrun masu bincike ke amfani da shi.

Za su fara tattaunawar ne da tambayar yadda kake da gaskiya, inda wannan shi zai sa mutum ya dage wajen nuna gaskiyarsa can gaba a tattaunawar.

Mutane na son a dauke masu gaskiya, a kan haka sai su yi ta bayar da hadin kai a binciken da ake yi musu, in ji Levine

Ya ce hatta wadanda ba su da gaskiya sai ka ga suna cikin tsaka mai wuya wajen kokarin nuna cewa suna bayar da hadin kai a binciken.

Daga nan ne za ka ga a can gaba kana ta gane wanda yake karya.

Tuni ake ganin wasu kwararrun masu bincike suke amfani da wadannan dabaru wajen aikinsu.

To amma idan muka yi la'akari da yadda aka yi imani da dabarar gane makaryaci daga yanayin fuskarsa da ido da sauran jikinsa akwai bukatar kara bayani kan muhimmanci da ingancin wadannan dabaru na yanzu.

Duk da nasarar da dabarun nasu suka samu Ormerod da Levine na fatan ganin wasu masanan sun kara bincike a kai ta yadda za a iya ganin tasirinsu a wani yanayin.

Ko da ike dai wadannan dabaru za su iya taimaka wa jami'an tsaro, kai ma kanka za ka iya amfani da su wajen gano makaryaci a harkokinka.

''Na kan jarraba dabarar a kan yara a lokuta da dama,'' in ji Ormerod.

Abin dai da za ka lura da shi, shi ne, ka da ka yi saurin yanke hukunci, saboda kawai ka ga mutum na tsoro-tsoro ko yana kokarin tuna wani muhimmin bayani da ya yi a baya, hakan ba yana nufin shi makaryaci ba ne.

A maimakon haka za ka fi sanya ido ne wajen gano alamun inda maganganunsa suke sabani ko karo da juna sosai.

Amma fa ka sani babu wata dabara da za a iya cewa dari bisa dari ana gane makaryaci ta hanyarta.

Sai dai ta hanyar amfani da 'yan dabaru da basira da kuma shawo kan mutum, ka iya sa ran cewa a karshe gaskiya za ta yi halinta.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The best (and worst) ways to spot a liar