Ko matsa 'yan yatsu na sa maka ciwon gaba?

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Za ka ga wasu mutane na matsawa ko kuma su sa a ja musu 'yan yatsunsu har su yi kara domin su ji dadi.

Claudia Hammond ta duba abin da ke sa wannan kara har ka ji ka gamsu tare da sanin ko hakan na lalata maka gabobi.

Wasu mutanen sukan sa yatsun nasu wannan kara ne ta hanyar jan bakin yatsun daya bayan daya har sai sun ji wannan kara.

Wasu kuma sukan dunkule yatsun ne ko kuma su lankwasa su baya inda yawancinsu za su yi karan a lokaci daya.

Idan kana daga cikin mutanen da ke yin wannan abu ina jin ba za ka kasa haduwa da wani da ya yi maka gargadi cewa hakan na jawo ciwon gabobi ba.

A wurin wasu dabi'a ce mai ta da hankali, amma wasu kuwa su a wurinsu sabo ne mai dadi.

Ya danganta da nazarin da ka karanta, tsakanin kashi 25 zuwa 50 cikin dari na mutane yana yinta, kuma maza sun fi yi a kan mata.

Kowane tsari ko hanya ka bi wajen yinsa karan dai ta hanya iri daya yake samuwa.

Idan ka matsa ko ka ja yatsun sai filin da ke tsakanin gabobin ya karu, sai iskar cikin ruwan maikon (giris) da ke wurin ya yi kumfa (kwayaye kamar na ruwan sabulu).

Wadannan kwayayen kumfa sai su hadu su kara girma, inda daga nan sai wannan ruwa mai maiko da ya ke aiki a tsakanin gabobin kashi kamar man giris na karfe ya kwararo domin maye gurbin wanda ya tafi, sai ya fasa wadannan kwayaye na kumfa.

Da zarar gabobin sun yi wannan kara to fa ba za su kara yin wani ba sai bayan kusan minti 15.

Wannan ne zai ba wa mahadar gabobin dama ta sake dawowa yadda take tun farkko kuma hakan dai shi zai ba sauran iska da ke wurin ta narke a cikin ruwan maikon, ta yadda za ta iya sake yin kumfar da za ta faffashe idan an sake matsa yatsun.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

To idan muka duba bayanan fasahar kere-kere za mu ga cewa yawan matsa yatsu suna yin wannan kara har zuwa wasu gomman shekaru ka iya lalata wata fata mai kauri da guntsi (cartilage) da ta rufe mahadar.

A zahiri ma wasu sun kwatanta wannan da yadda karfen farfela ko fankar injin jirgin ruwa yake gogewa yau da gobe idan ya dade.

Sai dai shedar kwatanta abin da ke faruwa da karfen jirgin ruwan da hannun mutum kadan ce.

A gaskiya ma nazarce-nazarcen da aka yi a kan wannan ba su da yawa.

Watakila daya daga cikin binciken da aka yi wanda aka fi sani shi ne wanda wani likita a California, Donald Unger, ya jarraba a kansa a 2009.

Shi dai likitan sama da shekaru 60 kullum sai ya matsa yatsun hannunsa na hagu akalla sau biyu su yi wannan kara, amma ban da na hannunsa na dama.

Sakamakon da ya samu? Ina kallon yatsuna kuma ba wanda ya nuna wata alama ta ciwon gaba a dukkanin hannuwan biyu,'' in ji likitan.

Watakila ba za a rasa wadansu gwaje-gwajen da wasu suka yi ba na sosai da suka fi wannan.

A shekara ta 1975 an tambayi wasu masu jiyya 28 da ke wani gidan kula da marassa lafiya ko tsofaffi na Yahudawa a Los Angeles, ko sun taba yin wannan dabi'a ta matsa yatsu.

Sakamakon ya nuna wadanda suka yi da wuya su gamu da wannan larura ta ciwon gaba a hannuwansu a nan gaba.

A wani babban nazari ko bincike da aka yi a Detroit a 1990, masu bincike sun duba hannuwan mutane 300 da suka wuce shekara 45.

A cikinsu wadanda suke wannan dabi'a an gano ba sa iya rike abu da karfi sosai kamar wadanda ba sa yi, kuma kashi 84 cikin dari da alamun kumburi a hannuwansu.

Masu wannan bincike sai suka ce wannan na nufin kamata ya yi mutane su daina wannan dabi'a.

Ko wannan zai iya nuna cewa alama ce mutum zai gamu da wasu matsaloli a can gaba maimakon a ce sanadi ne na larura ?

Yana da muhimmanci a nuna cewa idan dai ana maganar ko masu matsa yatsu sun fi samun kansu cikin hadarin cutar ciwon gaba, a ce a'a.

Bincike na baya-bayan nan da aka yi wanda aka wallafa a shekara ta 2011, shi ne ya fi duk sauran da aka yi a baya, saboda a cikinsa ba ya tabo ko mutum ya taba matsa yatsun ba kadai har ma da maganar sau nawa yake yi idan yana yi.

Na san cewa za ka dauka mutumin da yake matsa yatsunsa duk minti 15 zai fi samun kansa cikin hadarin ciwon gaba fiye da wanda yake matsa yatsun sau daya a rana.

To amma a nan ma lamarin ba haka yake ba, domin babu wani bambanci a tsakaninsu.

A gaskiya ma dai babu bambancin yawan yuwuwar kamuwa da cutar ciwon gaba tsakanin masu matsa yatsun da mutanen da ba sa yi ma samsam.

Cigaba da matsa 'yan yatsunka su yi kara?

To yanzu sai mu duba yadda wannan magana ta danganta matsa yatsu da ciwon gaba ta samo asali. Ta ina ta bullo?

Shin gaskiya ne mutanen da suka riga suka kamu da ciwon gabobi a wasu lokutan gabobinsu na kara sabo da fata mai guntsi da ta lillebe mahadar ta baci.

A gaskiya da wuya a ce wannan wata alama ce ta farkon kamuwa da cutar ana ganin sai dai ta kasance sakamakon cutar amma ba sanadin haifar da cutar ba.

Abubuwan da aka lissafa da za su iya jawo wa mutum cutar ta gabobi su ne, shekaru da gado daga iyaye ko kakanni ko hadari a hannun a can baya ko aikin karfi na hannu tsawon rayuwar mutum.

Tun da mun ji haka, to komatsa yatsun ka iya haifar da wata illar?

Akwai dan abin da ba a rasa ban wasu 'yan rahotannin da ke nuna ko wani mutum ya ji wa kansa rauni cikin kashi ko tsokar dan yatsa ta hanyar matsa yatsun amma ba kasafai ake samun hakan ba.

To yanzu dai idan kana da sha'awar matsawa ko jan yatsunka har ka ji sun yi kara, kawai ka ci gaba ba, amma dai ka kwana da sanin matsayar likitocin nan da suka gudanar da bincike a gidan kula da marassa lafiyar nan da tsofaffi na Yahudawa da ke LA. Abin da suka ce?

''Babbar illar matsa yatsu su yi kara ita ce damuwar wanda ya sanya ido kan wanda yake yi.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Does cracking your knuckles cause arthritis?