Anya za mu iya kawar da kudin cizo?

A cikin shekara sama da goma da ta wuce an samu karuwar kudin cizo; dan karamin kwaron da ke addabar mutum ta zukar jininsa a kasashe da dama.

Brooke Borel ya duba abin da ake bukata domin fuskantar wannan barazana da ke kara tasowa.

Ba abin da ke sa tsigar jikinmu tashi, fatar jiki ta motsa kamar jin cewa da alamun kudin cizo a dakinmu.

Duk da kankantarsa, kudin cizo yana iya shan jinin da ya linka nauyinsa sau bakwai a lokaci daya, ya tsere ya buya inda ba za ka gan shi ba wata da watanni, ya bar ka da soshe-soshe da jiki rudu-rudu.

Tun kusan karshen 1990 kudin cizo ya kara zama alakakai a kusan ko ina a birane a gidajen jama'a da otal-otal a fadin duniya.

Wani bincike da ka yi a 2010 daga Jami'ar Kentucy da hukumar yaki da kwari ta Amurka an gano cewa kashi 95 na kamfanonin Amurka da ke yaki da kwari sun yi aikin maganin kashe kwari a shekarar 2009, kari daga kashi 25 cikin a shekaru goma baya kuma kashi 11 cikin dari kafin wannan.

Hatta a wani bangare na ginin hukumar kula da lafiya da tsafta da ke New York, wadda ke kula da jama'ar da ke fama da kudin cizon, sai da aka yi feshin maganin kwaron a watan Satumba na 2012.

Kamar yadda rahoton ya ce masu aikin yaki da kwari a Turai da Afrika da Australiya da Arewacin Amurka, sun ce kudin cizo shi ne kwaron da ya fi wahalar kawar wa.

Saboda ya fi tururuwa da kiyashi da gara har kyankyaso ma ya fi.

Hakkin mallakar hoto science photo library

Wani binciken ma ya nuna cewa a Landan kadai aikin yaki da kudin cizo yana karuwa da kashi daya bisa hudu tsakanin 2000 da 2006.

Abin takaicin game da wannan lamari shi ne mun sakankance cewa mun yi maganin wannan kwaro.

Clive Boase kwararre a kan yaki da kwari da ke Suffolk, wanda kuma ya rubata binciken na Landan, ya ce tun daga shekarun 1930 ne aka fara samun raguwar kudin cizo a Birtaniya.

An samu hakan ne a lokacin saboda sauyin da aka kawo kan tsarin gina gidaje da kula da lafiyar jama'a, inda aka rurrushe tsofaffin gidajen gwamnati na jama'a, sannan duba-gari suke shiga har cikin gidaje don tabbatar da tsafta.

Bulla da sabbin nau'in maganin kwari da suka hada da DDT a shekarun 1940 shi ma ya taimaka wajen rage bazuwar kwaron, inda zuwa 1950 da wuya ma ka ga an samu inda ake da kudin cizon.

A Amurka ma an samu irin wannan gagarumar raguwa ta bazuwar kwaron daga kusan karshen shekarun 1940 zuwa gaba, can ma dai sakamakon samar da wannan hoda ta DDT da sauran magunguna.

To a yanzu kuma ina magungunan wannan yaki?

Magugunan kwarin da ake da su yanzu in ji Dini Millner, kwararriya a kan kwari daga Virginia, ta ce, ''ba kowa ne zai iya amfani da su ba saboda tsada.''

Ta kara da cewa samar da sababbin magungunan kwari abu ne mai tsada da cin lokaci.

Saboda kudin cizo yawanci a dakin kwana yake bazuwa, a kan haka sai kamfanonin yin magani sun bayar da cikakken bayani na tabbatar da cewa magani ba shi da hadari, saboda zai iya taba mutane da dabbobin cikin gida.

Kuma a tabbatar da wannan sai kamfani ya kashe kusan dala $256 a cikin shekaru takwas kuma a kan duk sinadarin hada maganin daya kamar yadda bayanin hukumomin Amurka da Turai ya nuna a 2010.

Wannan ya sa ba lalle a sami kamfanin da zai zuba jarinsa ba a wannan aiki.

Saboda a Amurka ake amfani da kashi daya bisa biyar na maganin da ake amfani da shi a duniya baki daya, amma yawancinsa ana amfani da shi ne a gona sai kuma na kashe ciyawa sannan kuma na kwari.

Millner ta ce, ''to idan ka duba yawan gonaki da lambun da ake da su sun fi yawan gidaje da sauran gine-gine na duniya baki daya. Kuma harkar gidaje ba kudi take samarwa ba sosai kamar ta gona.

Kuma hakkin mallakar fasahar maganin wa'adinsa shekara 20 ne da zarar ya wuce sai ka fara fuskantar gogayya daga wasu kamfanonin, kuma a lokacin ba lalle ka mayar da kudin ka a ce har ka ci riba ba.

Har yanzu dai, ko da yin sabon maganin kashe kudin cizo na da riba akwai sauran kalubale.

Akwai matsalar yadda za ka tabbatar ga yadda za a yi amfani da maganinka ya yi tasiri sosai wajen kashe kwaron a saukake kuma ba tare da wani hadari ba, wanda wannan kuma na bukatar sanin halittar kudin zicon.

To amma saboda shekara da shekaru babu kudin cizon da yawa a duniya, sai ya kasance babu sha'awa sosai ta nazari a kansa.

Daga farkon shekarun 2000 da aka fara ganin alamun sake bayyanarsa sosai a ko ina, sai masana kimiyya suka dawo neman sanin yadda kwaron yake tun daga tushe, inda suka fara daga yadda ma za a yi kiwonsa a dakin kimiyya.

Sai kuma maganar zuba jari wajen binciken. Duk da cewa dakunan kimiyya a kasashen duniya sun dukufa wajen nazarin kwaron, to amma babu wadataccen jari, ta wani fannin saboda ana ganin kwaron ba ya yada cuta.

Baya ga wannan akwai kuma batun bijire wa magani, domin hatta ita kanta hodar DDT da ake ganin tana maganin kwaron sosai ba ta da gariya ga wannan.

Shekaru biyar da bullo da wannan magani ya kuma gama duniya, sai aka samu bullar wani nau'i na kudin cizon wanda hodar ba ta yi masa komai a Hawaii.

A shekarun 1950 da 1960 an samu bullar wannan nau'i mai bijire wa maganin a Amurka da Japan da Koriya da Iran da Giyana (french Guiana) da wasu da dama.

Babu wani maganin kwari na guba da shi kansa ya fi karfin kwaro ya bijire masa musamman idan an dade ana amfani da shi.

A yau kusan kashi 90 cikin dari na nau'in kudin cizo yana iya bijire wa wani maganin na daban (pyrethroids) da ke aiki kamar DDT.

Hana yaduwarsa

Maganin kwari na guba ba zai iya magani ba shi kadai kuma ba wata hanya da ita kadai za ta kasance ta ganin bayan wannan kwaro a yanzu kamar yadda Micheal Potter masani kan kwari daga Jami'ar Kentucky ya ce.

Abin yi shi ne za a iya hada maganin guba da sauran dabaru, misali yadda ake sanya wasu abubuwan da ke yada zafi a wuri domin shi kudin cizo yana mutuwa ne a yanayin zafi da ya kai maki 45 a ma'aunin Selshiyas (celcius).

Akwai kuma hanyar amafani da fasahar halitta wajen hana yaduwar,inda za a yi amfani da maganin da ke takaita girman kwari ta yadda maganin zai hana kudin kaiwa cikakkiyar halittarsa wato ya tsumbure ta yadda ba zai iya yin kwai ba har ya yadu.

To sai dai matsalar wannan dabara ita ce, duk ha hana kudin girma ko haihuwa zai iya cizon mutum.

Wata hanyar kuma ita ce, za a iya amfani da kwayar halittar bakteriya wadda ke cikin kudin shi kansa(Wolbachia), ko kuma amfani da kwayar halittar kudin cizon wadda ke gaya masa inda zai je da kuma wadda zai sadu(barbara) da ita, za a iya sake yanayin halittar kwayar a sa ta rika illata shi.

Amma dai a halin yanzu za a iya daukar matakan wayar da kan mutane domin yin abubuwan da za su hana yaduwarsa a tsafta da sauransu.

Matakan da suka hada da, kula da gadon otal sosai kafin ka baza kayanka da lura sosai da kayanka kamar tufafi a inda za ka rataye ko ajiye su da wanke tufafi da ruwan zafi da kade akwatinka sosai bayan ka yi tafiya, sannan kuma ka kuji dauko kujero ku tebur ko wani gado da aka jefar ka kawo gidanka.

Wasu ma na bayar da shawarar sanya wa katifa da matashin kai riga da dai sauran matakai.

Wadannan matakan sun taimaka kwarai wajen hana yaduwar kudin cizon musamman a manya-manyan otal masu tsada, saboda za su iya kashe kudi domin daukar matakan, in ji Boase.

Ya kara da cewa, inda aka fi fama da wannan matsala ta kudin cizo a Birtaniya a yanzu, sai a yankunan unguwanni ko gidajen talakawa.

Ya ce hakan ba yana nufin wai don talakawa daman sun fi zama cikin hadarin matsalar, a'a sai dai saboda su talakawa ba za su iya bin wadannan matakan ba.

Ita ma Amurka tana da irin wannan matsala. Hanyar da ta fi wajen maganin kudin cizo ta dogara ne ga magunguna masu sauki da aiki da aka samar a kasuwa.

Mutane da dama idan za su rubuta sunan wannan kwaro da Ingilishi suna rubuta shi a matsayin kalma daya ne ''bedbugs'' amma kwararru masu ilimin kwari idan suna bayyana shi suna amfani da kalmomi biyu ne ''bed bugs'' saboda ya amsa sunansa.

Ba a kana kudin cizo ba har ma duk wani kwaro mai addabar mutum haka masanan suke rubuta sunansa wani misalin shi ne, na kuda, ''housefly'' kamar yadda ake rubuta shi a ke nan amma su sai sun raba kalmomin, ''house fly'' domin shi ma yana damun mutum, amma malam-buda-mana-littafi, ''butterfly'' haka suke barinsa a kalma daya, saboda shi ba ya damun mutane.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Will we ever… get rid of bed bugs?