Za mu taba samun taba maras cutarwa?

Hakkin mallakar hoto Reuters

Tsawon shekara da shekaru kamfanonin taba suke ta fafutukar ganin sun bullo da wata taba maras cutarwa amma abin ya gagara.

Ed Yong ya gudanar da bincike:

Akwai wani azanci da mutanen da ke aiki a asibitoci ke cewa: Taba ce kadai abar da idan ka yi amfani da ita kamar yadda ya kamata za ta kashe ka.

Bincike na tsawon shekaru ya tattara illolin da ke tattare da shan taba.

Illolin da suka kunshi cutuka sama da 12 masu haddasa cutar daji iri-iri da cutar zuciya da wadanda suka shafi numfashi da sauransu.

Ko wadannan illoli ne na shan taba da ba za a iya kauce musu ba?

Ko kuma akwai wata hanya ta kirkiro tabar da ba ta haifar da wata illa?

Hakkin mallakar hoto No credit
Image caption Wani nau'in taba mai batir

''Ina ganin abu ne mai wuya,'' in ji Stephen Hecht na cibiyar cutar daji ta Jami'ar Minnesota, wanda ke nazari kan abubuwan da ke haddasa cutar daji.

Hayakin taba wata matattara ce ta cutuka da ke kunshe da akalla nau'in guba akalla 4,000 da suka hada da akalla 70 wadanda fitattu ne wajen haddasa cutar sankara.

Ba wanda ya kirkiro wata taba da ta rage yawan wannan guba sosai amma kuma duk da haka aba ce da mutane ke kaunar shanta, duk da cewa kamfanoni sun yi ta fafutuka kusan shekara 50 a kan hakan,'' in ji Hecht.

''Babu alamar hakan zai tabbata.''

Kamar yadda Hecht ya ce, ba kamfanonin ba ne ba su yi kokari ba. Wani dan jarida Will Storr a baya bayan nan ya tattara bayanai kan tarihin tarin kokarin da aka yi na kirkiro taba maras cutarwa daga wadda take dauke da gubar da ke haifar da cutukan daji amma abin ya ci tura.

Bayan da duk aka yi ta sarrafa ta daga wannan mataki zuwa wancan, sai tabar take dandanon gawayi da robar da ake konawa da kuma farar wuta (sulphur).

Matsalar ita ce babu wani mataki na yin tabar ko shanta da ya cika hayakinta da tarin gubar da ta kunsa.

Wasu abubuwan suna cikin ganyen tabar ne kansa, domin shukar na iya debo su daga taki da kasar wurin har ma daga iska.

Da zarar ka kunna wa taba wuta sai nau'in gubar daban-daban su rika haduwa a cikin hayakin kai kuma kana shakarsu.

Kuma a duk lokacin da kake kona ganye ko wani abu na shuka kana shakar hayakin, za ka cika huhunka da tarin kwayoyin cuta ko guba da ke haddasa cutar sankara.

''Babu wata hanya da za ka kaucewa hakan,'' in ji Neal Benowitz na Jami'ar California a San Francisco.

POTENT DRUG

Kamar a ko da yaushe abin da ya ke tattare da guba shi ne yawan sinadaran ne illar kuma jero yawan gubar ba ita ce hanyar tantance hadarinsu ba.

To amma abu ne sananne cewa yawancin wadannan sinadarai da ke cikin hayakin taba ana samunsu sosai a cikin hayakin da kuma jikin mai shakar hayakin.

Kuma suna yi wa kwayoyin halittta na DNA illa kamar yadda ake gani a kurji.

Hanyar shigar da wadannan sinadarai na guba cikin jiki, ita ma tana da tasiri.

Da yawa daga cikin sinadaran akwai su a cikin wasu abubuwan na amfanin yau da kullum na mutane ciki har da abinci.

To amma akwai bambanci babba tsakanin shigarsu jiki, bayan sun ratsa wasu sinadarai masu sarrafa abubuwan da ke shiga jiki har su kai cikin jini, da kuma zukarsu kai tsaye zuwa cikin huhunka inda daga nan za su shige jini.

Akwai wasu hanyoyi da za su iya rage yawan gubar da ke haddasa cutar sankara a haayaki.

Kamar yanayin sarrafa irin ganyayyakin tabar da sirka su da wasu abubuwan ko rage yawan karfi ko tace su da sauran hanyoyi kamar sanya mata audugar tace hayakin domin rage wasu sinadaran.

''Sai dai ba wata sheda da ke tabbatar da hakan yana wani tasiri, '' in ji Hecht.

Masanin ya kara da cewa,''muna mayar da hankali a kan sinadaran da muka sani ne masu hadari, to amma watakila wadannan din 'yan daruruwa ne kawai daga cikin 4,000 din da muka gano.

Za ta iya kasancewa akwai wasu abubuwan kuma da ke wakana da mu ba mu sani ba.''

Sannan kuma akwai maganar sinadarin nikotin (nicotine), wanda duk da cewa sinadari ne mai kama mutum sosai da ba ya cikin masu haddasa cutar daji, bai za a ce ba ya haddasa irin tasa illar ba.

Domin yana kara yawan bugun zuciya da matse jijiyoyin kai jini tare da jawo yawan maiko (cholesterol).

Akwai wata sheda ma da ke nuna yana iya hana kwayoyin halittar cutar daji hallaka kansu ko kuma taimaka wa girman jijiyoyin jini da suke kai iska da kayan abinci cikin kurji.

Amma duka wannan bincike ne da aka yi a dakin kimiyya.

''Ba tabbas hakan na faruwa ajikin wata dabba mai rai.'' In ji Hecht.

''Babbar matsalar sinadarin na nikotin dai ita ce, sinadari ne da ke sa taba ta kama mutum sosai, ya zama ko da yaushe yana son shanta.

Kokarin da kamfanonin taba suka yi na samar da tabar da ke da karancin wannan sinadarin na nikotin a shekarun 1960 da kuma 1970 bai yi nasara ba, har ana ganin matakan.

Bayan samar da tabar a wancan lokaci sai aka gwada shan nata a na'ura.

Ko da yake an ga alamun raguwar zukar sinadarin a wannan gwaji to amma wasu masu binciken kwakwaf suna ganin ai mutum ba na'ura ba ce akwai wasu halaye da hatta yanayinsa na rike tabar da za su sa a samu bambanci.

Binciken ya nuna cewa lamarin ma zai kai sa mutane shan karin tabar ne wato shakar karin hayaki, kuma duk da ikirarin kamfanonin hakan zai kara jefa mutane cikin hadarin kamuwa da kwayoyin cutar daji.

Maras cuta?

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Taba mai batir da abin chajinta

Ire-iren tabar da aka bullo da su marassa hayaki sun dan fi saukin hadari.

Amma su ma duk da cewa tsotsa ko taunawa ko kuma shakarsu ake yi, ba a kunna musu wuta, suna dauke da wadannan kwayoyin cutar daji kamar taba mai hayaki kuma na danganta su da haddasa cutar sankara ta baki da makogwaro da kuma ta ciki.

Irin wannan tabar da fita daban, ba ta haddasa wadannan cutu ka ita ce ta kasar Sweden(snus).

Ita wannan taba ana sa ta ne a baki, mutum ya rika tsotsonta a karkashin lebe daga cikin.

Saboda ba ta dauke da wasu sinadarai kuma ana bin wasu ka'idoji wajen yinta, duk da haka tana da nikotin da ke sa mutane son yin amfani da ita sosai.

Yanayin yadda take ana ganin shi yasa ba a samun masu kamuwa da cutar daji ta huhu da baki a kasar ta Sweden, idan aka kwatanta da sauran kasashe da ake yawan shan taba mai hayaki.

''Ta fi rashin hadari amma daiba za a ce dari bisa dari ba ta da hadari ba akwai yuwuwar ita ma tana iya jawo cutar sankara'' in ji Benowitz.

Hakkin mallakar hoto PA

Ba shakka wasu gwaje-gwajen da aka yi a kwanan nan sun nuna ita ma tana tattare da hadarin sa cutar sankara ta ciki da kuma hadarin mutuwa daga cutar daji.

''Idan ka ce kowa ya daina shan taba ya rika amfani da irin wannan ta Sweden za a samu muhimmin cigaba a fannin kula da lafiya, amma maganar ita ce, ko mutane za su amince da yin hakan,'' in ji Benowitz.

Fargabarsa ita ce wannan tabar da wuya ta bar wadanda taba ta zamar musu jiki su yi watsi da dabi'ar ba, saboda ita kuma za ta sa su ci gaba da sha'awar sinadarin nikotin (nicotine) ko kuma ta bude wadanda ba sa shan taba hanyar somawa.

''Watakila dai shanta ya fi shan taba amma mai yuwuwa kai dai, ba za ka so ka sa ta a bakinka ba,'' in ji Hecht.

Wannan dalilin shi ne aka kawo a kan maganar shan taba mai amfani da batir.

Wadda ita kuma ta hanyar amfani da ita za a samu biyan bukatar sinadarin na nikotin ta hanyar fitar da tiriri ba tare da kwayoyin sinadaran da ke haddasa cutar daji na taba ba.

Wannan bayani a takarda kenan amma ba a zahiri ba, domin babu cikakken bayani kan abin da ita kuma za ta fitar sannan abin zai dogara daga samfuru zuwa samfuri.

Sai dai wani bincike na hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka ya nuna ita ma dai wannan taba mai batir za ta rika fitar da wasu sinadarai masu sa cutar daji.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

''A rubuce wannan za ta fi waccan tabar ta Sweden ( snus) rashin hadarin cutarwa in ji Benowitz amma duk da haka ana dar-dari da su saboda ba wata doka a kanta tukuna, saboda haka ba wanda yasan abin da za ka kwasa idan ka sha ta.''

Amfani da wadannan nau'in tabar biyu ta Sweden da mai batir abu ne da zai zama da cece-kuce ko da an samu karin bayani a kansu.

Wannan ba shakka ya nuna irin dambarwar da ke tattare da harkar kula da lafiya, bisa la'akari da cewa shan taba abu ne da ke zama jiki ga mutum kuma mai illa.

Sboda haka za a iya cewa abu ne da ya dace a rage wannan hadari ta hanyar tabbatr da samar da tabar da ta fi lafiya amma wadda kuma ba za a ce gaba daya kacokan ba ta da illa ba?

Idan da ba mu taba ganin taba(mai hayaki) ba da sai mu kalli taba maras hayaki(ta zamani) mu ce, ''kai yakamata a hana amfani da ita'' in ji Hecht.

A duniyar da ba a taba sanin taba ba, za a yi wannan muhawara.

To amma wannan duniyar ba ita; me za mu yi a wannan to?

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Will we ever… have safe cigarettes?