Yadda launin ja yake juya zuciya

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Watakila ja shi ne launin da ya fi tasiri a kusan dukkanin rayuwa ko dabi'arka, kama daga wurin aiki zuwa rayuwarka ta kauna ko soyayya. Na san za ka je ta yaya?

David Robson zai yi maka bayani:

Ba za mu taba sanin abin da ya sa kakanninmu suka rika tsinko furanni jajaye suna shafawa a jikinsu ba dubban shekaru da suka gabata ba.

Amma idan za mu yi hasashe sai mu ce watakila sun yi hakan ne saboda ja launi ne na jininmu wanda kuma jini tuni ne na zahiri na rayuwa da mutuwa.

A yau ana danganta launin ja da mulki ko iko ko mallaka ko kutse da kuma jima'i; kama daga tufafin kawa na sarauniyar Ingila zuwa fitulun kawa na lardin jar fitila na birnin Amsterdam dukkaninsu jajaye ne.

Kuma wannan dangantaka ko alaka ba haka kawai ta kasance ba akwai dalilai.

Wani sabon reshe na ilimin kimiyya wanda ya shafi nazari kan launi (colour psychology) ya gano cewa launin ja na iya yin tasiri a kan yanayinmu da yadda muke daukar abu a ranmu da kuma ayyukanmu.

Sanya jan tufafi zai iya ma sauya yanayin karfin jikinka da kuma jirkita kwayoyin halittarka kamar ya sa ka kara kwazo a wasan kwallon kafa.

Misali kana yanayi na sanyin jiki ka sauya lokaci guda idan ka sa tufafi ja ka zama mai kuzari.

To menene yake tattare da launin ja da ke sa launin zama mai tasiri ko karfi haka?

Alamun gargadi:

Ba tantama yadda muke daukar launin ja abu ne da ya zo daidai da lokacin da wani abu mai muhimmanci a tarihin juyi ko sauyin halittar dan-adam.

Dabbobi da yawa da ke shayar da 'ya'yansu nono kamar karnuka ba sa iya bambancewa tsakanin launin ja da kore.

Amma mu a lokacin da kakanninmu na asalin dan-adam suke kokarin sabo da rayuwa a daji, sai idonsu ya samar da wata kwayar halitta da ta sa suke iya gane ja ko nunannen dan itace a bishiyarsa.

Wannan cigaba sai ya samar da da sabbin wasu hanyoyi na zamantakewa ko mu'amulla.

Idan aka ga fata ta yi ja ta hanyar zuwan karin jini kusa da saman fata, wannan wata alama ce ta mallaka ga yawan halittu dangin mutane na da kamar yadda bayani ya nuna.

Akwai birai wadanda ake kira Mandrin wadanda ake samu a kasashen Kamaru da Gabon da Equatorial Guinea da kuma Kongo wadanda za su iya kasance babban misali na yadda zanen launin ja da yake a fuskarsa da duwawunsu ke nuna girma da matsayi a cikinsu.

Duk wanda zanen nasa ja ya fi turuwa to ya fi wanda na sa bai yi ja ba sosai matsayi a cikin biran.

Saboda haka da zarar wani birin ya ga wanda launin jansa ya fi na shi to ba ma zai tunkare da fada ba domin ya san ba zai yi nasara ba.

Hakkin mallakar hoto spl
Image caption wannan ba biri ne da za ka saki jiki ko wasa da shi ba

Sai a shekara ta 2004 wasu masana kimiyyar tunanin dan-adam, Russell Hill da Robert Bartonwadanda suke Jami'ar Durham suka yi tunanin ko su ma mutane haka suke kamar wadannan biran.

Ko da yake mu mutane ba ma fitar da launin ja jawur kamar yadda wadannan biran suke, to amma a wani lokacin ranmu na baci matuka.

Saboda haka watakila ganin jajayen kaya ko tufafi zai iya sa a danganta hakan da fada da mallaka.

Hill da Barton sun rasa yadda za su bullo wa binciken, sai a lokacin gasar wasannin olympics ta 2004 suka samu damar da ta fi dacewa.

A wasannin da suke kamar na fada, damben zamani na boksin da kuma kokawar taekwondo an ba wa 'yan wasan tufafi ja da shdi ba tare da bin zabinsu ba domin masana kimiyyar su tantance kokarin kowane dan wasa idan yana sanye da wani launin kaya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An fi ganin dan damben da ya sa jan kaya zai yi nasara

A yadda suka rika nazari da biybiyar kokarin 'yan wasan Hill ya gano cewa wadanda aka ba wa jan kayan sawa na wasan, da kashi biyar cikin dari an fi sa ran za su yi nasara kan masu shudin kayan.

Amma hill ya gaggauta cewa, ''sanya kaya masu launin ja ba shi ne kawai zai sa ka zama gwanin dan wasa ba.''

''Amma dai zai taimaka wajen ganin wanda zai yi nasara idan aka hada sa'oi.''

Wannan nazarin a kan launin ja a harkar wasanni, ya tayar da wasu binciken a wannan fage inda aka samu sakama iri daya a wajen kwallon kafa.

A fagen kwallon kafa nazari ya nuna da wuya idan gola ko mai tsaron raga yana sanye da jesi ko riga mai launin ja a ci si bugun fanareti.

Ba dadewa wannan ya sa wannan sabon fage na kimiyyar launi ya zama mai zaman kansa a da'irar kimiyya.

''Kuma wannan nazari na masanan biyu shi ya jawo bunkasar sha'awar gudanar da bincike a kan launi da kuma tasirin sa'' in ji Andrew Elliot na Jami'ar Rochester da ke New York.

Dalilin wannan tasiri abu ne da har yanzu ake muhawara a kansa. Elliot ya nuna cewa wasu tarin bincike da aka yi sun nuna cewa mutanen da suka sanya tufafi jajaye su kansu suna jin karfi fiye da sauran mutane, wanda hakan ke kara bugun zuciyarsu da kuma yawan kwayar halittarsu ta maza (testosterone) wanda hakan zai bunkasa kwazonsa.

Ko kuma ma ta wani fannin jan tuaffin zai sa abokin karawar wanda ya sa jan kayan ya karaya, kamar yadda wadannan birai da jan zanen fuskarsu da duwawunsu bai kai na wani suke jin tsoron wanda ya fi su launin jan.

Elliot ya ce, ''idan ka ga ja sai gabanka ya fadi ka ji tsoro ka karaya sai yawan kwayar halittarka ta namiji ya yi kasa.''

Ko kuma a wani fannin su kansu alkalan wasa abin yana tasiri a kansu inda suke ganin 'yan wasan da suka sa jan kaya za su fi nasara.

Kamar yadda aka sauya kayan da wasu 'yan wasa na Jamus suka sa a hoton bidiyo a ka maye da wni launin, sai aka nemi kwararrun alkalan wasa su zabi wadanda suke ganin za su yi nasara sai suka zabi wadanda aka sauya wa kaya aka sa musu ja.

Hill ya ce duk dan wasan da yake sanye da kaya mai launin ja shi alkalin wasan zai zaba cewa zai fi yin nasara.

Idan muka bar fagen wasa muka karkata zuwa wajen caca, a nan ma kusan haka lamarin yake.

A nan kuma duk wanda yake rike da sanda mai launin ja a wasan caca ana ganin shi zai yi nasara fiye da wadanda suke rike da sanda mai launin shudi ko fari domin watakila ana daukar jar sanda kamar ta masu nasara.

A bangaren jarrabawa ko ganawa da mutum domin daukarsa aiki, ana ganin idan ka sanya wani jan kaya ana ganin za ka fi samun nasara.

Wasu kwararru a kan tufafi suna danganta jan nakataye (necktie) da kwarjini ko iko a wurin aiki.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Launi zai iya sa a sauya yadda ake daukarmu?

Watakila tasirin launin ja da aka fi nazari a kansa ma shi ne, na dangantakar launin da sha'awa da so da kuma alhaki ko sabo.

Wadansu bincike da Elliot da abokan aikinsa suka yi sun tabbatar da cewa mutane maza da mata idan suka sanya jajayen kaya sun fi ba da sha'awa ko kyau a kan wadanda suka sanya wasu kayan daban.

Ko da yake yawanci wadannan nazarce-nazarcen anyi su ne a dakin binciken kimiyya inda watakila za a nuna wa mutum hoto ne kawai, to amma sakamakon da alama ya kai har ga yanayi na zahiri.

An ga cewa ma'aikaciyar otal da ke yi wa baki hidima wadda ta sa jan tufafi ta fi samun kyauta daga maza da suka je otal din.

Haka kuma matar da ta sa jar riga, wadda ke tsaye a bakin titi take son a taimake ta a rage mata hanya ta fi samun dace.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Launin kauna ko danniya?

Duk da wannan bambanci da tasirin na jan launi, ka da ka zari jiki ka ce za ka sauya tufafinka da jajaye ko kuma ka ce za ka sauya fentin ofishink ya koma ja.

Saboda a wasu lokutan ko wani yanayin launin ja zai iya jawo maka abin ki.

Misali jan tufafi na sa a dauki namiji mai danniya da iko wanda hakan ke sa a yi sha'awarsa a wani fannin amma kuma a wani fannin tunanin danniyarsa zai iya jawo masa tsana ko ma farmaki, in ji Elliot.

Kuma a dakin jarrabawa ya gano cewa mutane ba sa kokari sosai a jarrabawar da ta shafi basira idan aka ba su takardar a jar takarda.

Duk da wadannan bayanai da aka gano har yanzu ba dukkansu ba ne suka cancanci a yarda da su zuwa yanzu.

Elliot ya ce ''ina ganin har yanzu wadansu nazarce-nazarcen suna matakin farko ne na bincike.''

Ya kara da cewa , '' a karshe watakila za mu iya amfani da kimiyyar launi mu samar da wurin aiki mafi dacewa ga jama'a, amma a yanzu muna nesa da kaiwa wannan matakin.''

Ina ganin ya yi wuri yanzu a ce ga launin jesin (rigar 'yan wasa) da za a rika yi na 'yan wasa ko kuma a ce za a hana amfani da jan abin rubutu (alkalami ko biro).

Sannan Elliot yana son ganin an kara dagewa wajen gudanar da bincike a kan sauran launuka.

Saboda yana ganin idan launin ja zai hana wasu kokari to launin kore da shudi na iya bunkasa kwazo a fannin wasu wasannin na kalmomi.

Duk da hakan ma Elliot yana ganin tasirin sauran launukan ba zai kai na ja ba a kan dabi'unmu.

''Yadda ake daukar launin ja abu ne da ya kai wani matsayi mai muhimmanci matuka,'' in ji Elliot.

''Ja shi ne launin nunannen dan itace shi ne kuma launin fuskarka a lokacin da ranka ya baci haka kuma launin fuskar mutumin da sha'awarsa ta motsa yake.''

Ta wannan, za a cigaba da danganta launin ja da rayuwa tare da yi masa fassara da ba shi ma'ana da kuma yin tasiri a wurinmu kamar yadda jinin da ke gudu a jijiyoyinmu yake yi.

Watakila muna kawai tabbatar da abin da kakanninmu suka riga suka gano ne shekaru dubbai, lokacin da suka fara shafa launin na ja a jikinsu: ba wani launi da ya kai shi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How the colour red warps the mind