Kana yawan mu'amulla da wayar salula?

Hakkin mallakar hoto Josh Pulman

Ka kewaya cikin duk wani birni a wannan shekara ta 2015 abin da za ka gani shi ne mutane sun kura wa wayarsu ido ko kuma suna magana ta wayar. Waya na sauya yadda muke kenan?

Tom Chatfield ya yi nazari akai.

Wasu mutane sun tsaya kusa da wani ginin tarihi na mutum-mutumi ba wanda ya damu da kowa a wurin, kowa na sha'anin gabansa, kai a takaice ma ba wanda ya san da wani a wurin.

Can gefe daya ga wata mata baki a bude ta dafa kirjinta da hannu daya tana tafiya a titi mai cike da jama'a da ke kai kawo. Can kuma ga wasu matasa su biyu, ko 'yan uwa ne? - suna tsaye a kusa da wata katanga fara dukkanninsu sun karkatar da kai kusan wuri daya.

Wadannan na daga abubuwan da ke cikin hoton da Josh Pulman ya dauka a jerin hotunan da yake dauka da ake kira Somewhere Else (wani wuri), wanda ke nuna yadda mutane ke amfani da waya a matattarar jama'a.

Kusan kowane titi a kowane birni na kowace kasa a duniyar nan idan ka duba abin da za ka gani mutane na yi kenan, abin da a 'yan shekarun baya babu shi.

Yanzu har ma mun saba da cewa kasancewa a wuri daya ba yana nufin muna tare ba kenan ko muna abu daya da ya shafe mu baki daya.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Duk inda muka je, muna dauke da abubuwan da kusan sun fi ma wurin da muke tsaye kyau.

Wadannan abubuwa da muke dauke da su, suna bude mana hanyar ganawa da abokanmu da iyalai da samun labarai da ra'ayoyi da ganin fitattun mutane da aiki da jin dadi da bayanai da jita-jita da sauransu.

Ba abin mamaki ba ne a ce dukkaninmu a daure muke, ganin yadda fuskar mutanen da ke hoton Pulman ke cike da yanayi iri daban-daban

Za mu iya cewa muna da 'yanci, idan 'yanci ita ce kalmar da ta dace, mu jefa kwakwalwarmu cikin aiki ko kuma mudauki mata hankali a kowane lokaci.

Ba mu taba samun saukin kiran wadanda muke kauna ba ko wadanda muke bukata ko wadanda muke kula da su ko wadanda muka dogara da su ba, kamar yadda muka samu ta hanyar 'yan na'urorin da muke rike da su ba, wadanda kuma nann gaba kadan za mu rika sanyawa ko daura su a jikinmu.

Hakkin mallakar hoto Josh Pulman

Kamar yadda shi kansa Pulman ya tambaya, ''idan mutane biyu suna tafiya a titi tare kowannensu na waya da wani can, za mu iya cewa tare suke?

Kuma menene tasirin yanayin da suke ciki a lokacin wannan waya, ko na bacin rai ko na farin ciki ko na damu ne a kan mu sauran jama'a da muke ganin abin da suke ciki?

Kafin a ce mutum ya zama mutumsai yana da alaka da wasu mutanen. To amma za mu iya cewa basirarmu ta kai mu ta baro mu? Shin abu ne da zai yuwu a ce a lokaci daya ka hada alaka ta waya ko kana mu'amulla ta waya fiye da yadda ya kamata, idan har hakan za ta iya yuwuwa, me hakan zai zama kenan a rayuwarmu nan gaba.

Rayuwa ta waya

Tarho abu ne da ya kasance mai cikas ga mu'amulla (mutane ba sa haduwa gaba da gaba sai kawai su yi waya maimakon a da sai sun hadu da junansu) kuma abin sha'awa a fannin fasaha tun lokacin da aka kirkiro shi.

Ka yi tunanin yadda abin ya ke a karni na 19 lokacin da aka fara hada layukan wayar tarho inda ake jan waya bayan waya daga gari zuwa gari daga kasa zuwa kasa, inda ake nade wadannan wayoyi da zaka gani cunkus a tituna da jikin gine-gine.

A keta haddin bango, na kare magana, inda yanzu sai dai ya kare kallo amma ba magana ba, mutum ya jefa gida cikin wani sabon tsari na mu'amulla.

Hakkin mallakar hoto Josh Pulman

Na'urar aikewa da wasika ta waya (telegraph) tuni ta ba wa duniya wani abu mai matukar mamaki, ta yadda ake aikawa da sako cikin sauri kamar walkiya.

Ko da yake tarho ba kamar wasikar tangarahon ba ce amma tun a shekarar 1897 wani marubucina Burtaniya ya koka da yadda cigaban tarho zai kawar da sirrin ganawar gaba da gaba.

Irin wannan fargaba da akae dangantawa da zuwan fasaha ba sabon abu ba ne, abu ne da ake yi tun a zamanin Girkawa na da.

Duk da cewa a wancan lokacin an zuzuta illar da ke tattare da zuwan tarho ta wani fannin ta zo da albishir.

Idan a wancan lokacin muna ta huda bangon gidajenmu da ofisoshi muna makala wayoyin layin taroho nan da can rakwacam, to yanzu wannan abin ne muke yi a jikinmu maimakon bango kuma shi ne muka fara jin illar hakan.

Kamar kakanninta na karni na 19, wayar salula ta fara ne a matsayin wata alama ta manyan mutane masu hali da iko.

To amma a hankali a hankali sai ta zama gama-gari, kusan ko ina da akwai.

Abu har ya zama jiki a harkokinmu na yau da kullum inda za ka ji mutum na cewa, ''idan na isa can da rana zan yi ma waya.''

A lokacin abu ya zama cewa rashin samunka ma kamar wani abu ne na daban da ba za a yi tsammami ba ko kuma ma abin da zai tayar da hankalin mai nemanka.

Kamar tarihi ne yake maimaita kansa, a yanzu ma sai gargadi ake yi kan illar wayar salula.

A wannan zamanin yawan mu'amullarmu da wayar ya kawar da hankali daga abin da ya kamata a damu da shi na cewa wai shin da me ma ake hada mu ne.

Ka duba yadda a cikin sauki labari ya bazu na wani mutum mai shekara 31 da aka yi wa magani saboda ya kamu da matsalar yawan amfani da intanet, saboda yawan amfani da tabaran Google. Sanya tabaran Google kamar a ce ka daura wayar salularka ce a fuska.

Kuma ana kunna shi ne ta hanyar magana ko dan taba shi da yatsa.

Likitoci sun gano shi wannan mutum da ya samu matsala yakan yi irin wannan motsi da yatsa kamar zai kunna tabaran ba tare da ya sani ba.

Ya kai hannunsa gefen goshinsa yana dan tattabawa kamar yadda yake kunna tabaran ko da kuwa ba ya sanye da tabaran.

Yana sanya tabaran tsawon sa'a 18 a duk rana kuma da daddare yana mafarkin kallon abubuwan da ke faruwa a duniya ta tabaran.

Hakkin mallakar hoto Josh Pulman

Wannan babban misali ne na labari mai tsoratarwa da aka yi domin wannan lokaci namu ( mutumin da abin ya auku a kansa an ce yana da 'yar matsalar tabin hankali da kuma yawan shan barasa).

Zamu ta tarad da mujemu ke nan, domin mutum ne da ke cikin wani mawuyacin hali ya gamu da wata hanya da ba zai iya kauce wa ba, sai kawai ya afka ciki.

Ga wadansu masu karatu, ko da yake ina ganin lamarin zai sa wasu tambayoyi na tashin hankali.

Sau nawa kake kai hannunka kan wayarka ba tare da ka sani ba, ko kuma ka kai hannunka wurin da kake ajiye wayar?

Ya kake jin karar wayar a jikinka a duk lokacin da aka turo maka wani sako, ko kuma rashin jin karar wayar idan ba sabis ko sadarwa ta yanke?

Yaya halin da mutumin nan mai amfani da tabaran Google na ya samu kansa ciki yake tuna maka alakarka da fasaha?

Matsalar ita ce wadannan ba tambayoyi ba ne masu amsa ta kai tsaye ko tartibiya.

Tantancewa tsakanin menene dabi'a da abin da ya zama jiki a wurinmu na nufin bayyana abin da muke nufi da dabi'ar da take mai kyau wadda aka yarda da ita. Idan za a ce fasaha ta cigaba to bai wuce a ce ta kawo sauyi ne ba daga abin da aka saba cikin sauri.

Na yi shekara da shekaru ina kokarin fayyace dangantakarmu da fasaha amma har yanzu abin ya gagara.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

A hannu daya kamar yadda masanin falsafan nan Julian Baggini ya taba bayyana min cewa, ''mutane za su iya sauyawa amma ta hanyoyi da dama muna nan yadda muke''.

A daya hannun fasahar zamani na nufin dangantakata da da sauran jama'a da kuma duniya ta bunkasa fiye da duk wani abu da hatta kakannina suka sani.

Ina iya samo bayanai da dabi'u da ilimi daban-daban daga kwamfuta.

Kamar yadda masana falsafa kamar Andy Clark da David J Chalmers suka ce, zuciya ta kamar wata hadaka ce tsakanin kwakwalwata da na'urar da ke hannuna kamar wayata.

Ni ke nan abu ne mai fannoni da dama da da ya hada duka wadannan abubuwa biyu wato waya da kwakwalwa.

Tun da haka ne me zai hana in yi murnar wannan sauki kamar yadda nake ji da 'yancin da ke tattare da mallakar mota da na'urar wanke kwanuka ko amfani tabaran likita da zai gyra min matsalar idona.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani hanzari ba gudu ba shi ne, ko da ba ka yarda cewa wayar salulata kamar wata zuciyata ta ce da nake rike da ita a hannu ba, ba za ka iya kawar da kai daga tarin shedar raunin kwakwalwar mutum ba.

Mu ba halittu ba ne kadai masu dabi'a, halittu ne masu karanci da kuma iyakar tunani.

Misali ka yi kokarin raba hankalin wani ta hanyar ba shi lissafi ya yi maka, yana cikin yi kuma sai ka wulkita wani abu ta gefen idonsa, daga nan za ka ga ka rikita shi.

To amma a yau kusan duk matakin da za mu dauka ya gogara ne ga irin tarin miliyoyin bayanan da muke tattarowa daga 'yan na'urorin da ke aljihunmu (waya).

Shin muna bukatar mu ci gaba da cin moriyar ko kuma mu raba jikinmu da guba?

Menene amfanin mu daina yanzu in har za mu dawo mu ci gaba a wani lokaci?

Gara mu fuskanci al'amura yadda suke mu ci gaba da alakarmu mai muhimmanci wadda za ta cigaba da karfafa tsakanin kwakwalwa da ke jikinmu da fasahar intanet da muke kulla alaka a tsakaninsu.

Hakkin mallakar hoto Josh Pulman

Kuma ko ba komai ba ina bata lokacina ba ne wajen kallon fuskar wayata kawai, ina zuba ido ne a kan hadakar zukatan mutane da ba a taba samun irinta ba a tarihi wanda kowanne ya fi kwamfutar da ta fi sauri a duniya karfi.

Idan abin damuwa shi ne yawan kurda-kurda da shige-shige da muke yi a intanet, abin yi shi ne sai mu rika lura da inda za mu shiga da wanda za mu yi mu'amulla da shi da kuma abin da za mu rika tambayar juna. Domin maganar yanke hulda da intanet abu ne mai wuya ko kuma wanda ba zai yuwu ba.

Hoton da na fi so a jerin hotunan Josh Pulman(Somewhere Else) na takwas, na daban ne, saboda matar da ke ciki tana murmushi. Ban san dalilinta na murmushin ba amma ina ganin saboda abin da muryar da take sauraro a kunnenta ne, watakila wani labari ne mai dadi ko wata sa'ida ko wani abin dariya.

Yayin da za ka ga hoton sauran mutane da ke waya wasu alamun hankali a tashe wasu cikin damuwa a tsakanin nisan duniya da wadanda suke magana. Ita kuwa wannan matar tana cikin farin ciki kuma na tabbata wanda take wayar da shi, shi ma yana cikin farin ciki.

Yanayin bai yi kama da gidan fursuna ba; zuciya biyu cikin farin ciki na fadada duniya.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Are you 'over-connected'?