Abin da ya sa kida yake ratsa mu

Hakkin mallakar hoto Getty

Wane ne zai ce wani kida bai taba ratsa zuciyarsa ba? Walau a wani gidan rawa ko a gidan biki ko a kasuwa ko a rediyo kida zai iya ratsa mu, ya bayyana yanayin dadi ko nishadi ko alhani fiye da kalmar baka.

David Robson ya duba mana dalilin haka.

Kamar yadda Philip, wani daga cikinku masu karanta labaran da muke kawo muku a wannan sashe, ya nuna dalilan da ke sa kida hakan ba a bayyane suke ba.

''Abu ne da yake a fili gareni yadda kida yake ratsa mutum ya dauki hankalinsa ya sa shi nishadi da jin dadi da tunani da kuma biyan bukata.

Wadannan duka na taimakawa wajen bayyana yadda kida ke da muhimmanci.

To amma abin neman a sani shi ne ta yaya ko kuma me ya sa kida yake da wannan tasiri a kanmu? Wannan tambaya ce da ta gagara amsawa ko kuma in ce ake ta fafutukar gano ta kamar yadda Philip ya bayyana a wasikar da ya aiko mana (BBC Future team).

Wannan tambaya ce mai muhimmanci da Philip ya yi, domin hatta mutumin da ya kirkiro maganar yadda halitta ta faro a kimiyyance, Charles Darwin ya yi matukar mamakin basirar dan-adam kan kida, har ya bayyana ta a matsayin daya daga cikin baiwar da mutum ya samu.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wasu masana kimiyya kamar Steven Pinker kwararre kan kwakwalwa, yana ganin anya ma kuwa kida yana da wani muhimmanci.

A ganinsa muna son kida ne kawai saboda yana mana matashiya a wasu fannoni na jikinmu, kamar sani ko gane yanayin wani abu misali na bai daya.

Ya ce idan ba haka ba kida a karan kansa ba shi da wani amfani da ya wuce rugugi kawai.

To idan dai haka ne kida ba shi da wani muhimmanci ko amfani sai a ce kenan mutane a fadin duniya na bata lokacinsu a abin da ba shi da wani muhimmanci ko alama.

Idan kana jin ka kamu da kida, to ka duba yadda 'yan kabilar BaBinga na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, wadanda suka ba kida muhimmanci inda kusan duk wani abu na rayuwarsu yana da irin rawarsa, kama daga diban zuma zuwa farautar giwaye.

Masanin zamantakewa da al'adun dan-adam Gilbert Rouget, wanda ya zauna ya rayu da 'yan kabilar a 1946, ya gano cewa barci a lokacin da ake bukukuwa na daga manyan laifuka.

A rubutun da masanin ya yi, ya nuna yadda mutanen suka ba wa kida muhimmanici kusan yadda ba za ka iya bambanta shi da cin abinci ba a wurinsu.

A kan wannan dalilin mutane da dama da suka hada da ni suke fafutukar ganin sun yarda cewa kida wani dan sashe ne na tarihin rayuwar halittar mutum.

Hakkin mallakar hoto Getty

Akwai nazariyya daban-daban a kan wannan magana ta matsayin kida.

Daya daga fitattu a cikinsu ita ce kida wata hanya ce ta kwarkwasa, kamar yadda dawisu ke yi da jelarsa, a matsayin wani salo na kasa abokin neman aure ko soyayya (mace ko namiji).

Sai dai wannan sheda ba ta da makama mai karfi, domin wani nazari da aka yi kan 'yan biyu 10,000 ya kasa tabbatar da nuna cewa mawaka sun fi sauran jama'a dace idan ana maganar samun masoya ( kodayake Mick Jagger da harry Styles ba lalle su yarda da hakan ba).

Wasu masanan kuma sun nuna cewa kida ya samo asali ne a matsayin wata hanya ta sadarwa a zamanin da.

Idan aka duba za a ga wani nau'in kidan a zahiri yana dauke da salo ko sako mai ratsa zuciya da kakanninku ke yi.

Wani kidan kuma yana tsuma mu ne, kamar yadda wani kuma yake kwantar mana da hankali.

Irin wannan kidan za ka ga abu ne da kusan yake watsa sako a duniya baki daya tsakanin manya masu al'ada daban-daban ko yara,ko ma wasu dabbobi.

To kila za mu iya cewa kida wata hanya ce da ta samu ta hanyar alaka da dabbobin zamanin da wadda ta hanyar muke iya bayyana sakonninmu ko yanayinmu kafin kirkirar magana.

Ana ganin wannan hanya ita ta kai ga samar da magana.

Wani abin kuma shi ne ana ganin kida ya taimaka wajen kara hada kan al'ummomi a yayin da garuruwa ke kara hadewa da girma.

Rawa da kida tare ana ganin sun taimaka wajen hada kan mutane su ji 'yan uwantaka a tsakaninsu.

Kamar yadda masana kimiyyar motsin jikin dan-adam suka nuna, idan kana motsin jikinka ya zo daidai da na wani a lokaci daya ( kuna rawa tare)nan da nan kwakwalwarka za ta fara rufe tunanin sanin kanta.

Za ka ga kamar dai kana kallon mudubi ne. Za ka ga wanda kuke motsin tare da shi kamar kai yake kuma ya dauki irin ra'ayinka.

Kuma kamar yadda kai kanka za ka gani da rawar da kake yi, kida shi ne hanya mafi dacewa ta sa mutane su yi motsi tare.

Kodayake abu ne da zai kara tasirin kida amma shiga harkar kida da waka a dama da kai kai tsaye ba abu ne da yake dole ba domin cin moriyarsa.

Sauraren wakar kadai wadda ke tattare da kida mai dadi, da ke tsuma jikinka wannan zai iya kara wa mutum jin kishin wasu da sadaukar da kai domin amfanin wani ko wasu.

Yayin da aka samu karin hadin kai da kishin juna da karancin hamayya da gaba da juna ta haka za a samu cigaba da bunkasa tsakanin al'umma kamar yadda ake cewa tsintsiya madaurinki daya kamar yadda za a gani a tsakanin 'yan kabilar BaBinga.

Kamar yadda Rouget ya rubuta: kidan yana sa mutum wani shauki yadda kowane mutum yake zama kamar daya da mawakan''.

Za a iya ganin amfanin kida a matsayin abin da ke kara dankon zumunta da 'yan'uwantaka a wakokin kwadago da bayi kan yi da ma'aikatan jirgin ruwa da kuma sojoji ta irin wakokin da suke rerawa.

Ba shakka kida da waka da alama na da da kulla zumunta a tsakaninmu.

Ko da mene ne asalin kida, a yau dole ne mu danganta wasu kade-kaden da wasu muhimman abubuwanmu na rayuwa.

Kida shi ne sinadarin saduwa da daukar ciki da haihuwa da jana'iza da kuma duk wani abu da ke tsakani.

Ba mamaki ashe dukkaninmu muke jin wani dadi da nishadi da tuna wasu abubuwanmu na da a duk lokacin da muka ji wata waka ko kidan da muke so.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why music has a hotline to our emotions