Hanyoyin bunkasa kwakwalwarka

Hakkin mallakar hoto SPL

Ga wasu hanyoyi shida na kare kwakwalwarka daga tsufa da dakushewa wadanda suka kama daga sauya irin abincin da kake ci zuwa shakatawa kamar lokacin da kake dan shekara 21.

Ga bayanin David Robson:

Kamar duk wata na'ura mai kyau, kwakwalwa ta na bukatar kulawa yayin da mutum ke tsufa domin ta ci gaba da aiki da kyau.

Idan da har tana da takardar bin ka'idojin aikinta to da mun ga hanyar da za a bi domin inganta aikinta ko kula da ita yadda ya kamata.

Amma abin takaicin shi ne shawarar kadai da ake da ita yawanci mai rudarwa ce da kuma rikitarwa.

Amma duk da haka BBC ta bincika ta kuma kawo hanyoyi shida masu muhimmanci da amfani na kara kaifin kwakwalwarka.

Ka da ka yanke kauna da basirarka.

Ko ka taba shiga wani daki kuma ka manta abin da ya kai ka dakin?

Yayin da mutum ke shekaru sai ya dauka hakan wata alama ce ta cewa kwakwalwarsa ta fara dusashewa.

Wannan abu ne da yake iya faruwa a kan yaro da tsoho gaba daya.

Saboda haka bai kamata mu yi saurin yanke hukunci cewa kwakwalwarmu ce ta fara gazawa ko tsufa ba, domin hakan kamar wata hanya ce ta tabbatar da abin da muke tsammani.

A shekaru goma da suka wuce, Dayna Touron ta Jami'ar North Carolina ta gano cewa, yayin da shekaru ke kama mu sai mu rika yanke kauna da basirarmu, duk kuwa da cewa kalau take.

Daga nan sai mu koma dogaro a kan wasu abubuwa kamar na'urar GPS mai nuna wa mutum wuri ko kuma mu rika rubuta abubuwa a wayarmu ta salula ta yadda ba za mu manta ba.

Abin mamakin shi ne idan ba a jarraba kanmu da hakan ne ma zai iya sa kwakwalwarmu ta rika tsufa.

Saboda haka idan ka samu kanka a kofar daki kana tantamar inda za ka, to ka dauki hakan a matsayin wani kalubale ko tuni na ka tashi tsaye don kara karfin kwakwalwarka.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kare kunnuwanka

Tunani ko zuciyar mutum ( ba tsokar ba) na wahala idan aka raba ta da sauran sassanta.

Kila ta hanyar dorawa hankalinka karin dawainiyar lura da kuma kange mu daga abin da ya fi amfani, rashin ji (rasa kunne) na sa kwakwalwa ta rasa kwayoyin bangarenta da ke kula da basira kamar yadda wani bincike ya nuna.

Hakan na kara hadarin dusashewar kwakwalwa da kashi 24 cikin dari a cikin shekara shida.

Komai shekarunka,abu ne mai muhimmanci ka kiyaye da duk wani abu da zai iya shafar lafiyar kunnenka.

Sauraren kida mai kara na tsawon dakika 15 kadai a rana zai iya bata maka kunne.

Ba ma wannan ba hatta amfani da na'urar busar da gashi (wadda mata yawanci ke amfani da ita) na tsawon dakika 15 kawai a duk rana, hakan ma zai iya cutar da kananan kwayoyin halitta na kunnenka.

Idan kuma tuni har ka fara gamuwa da matsalar rashin ji sosai to ka nemi magani wajen likita, domin dakile matsalar tun tana karama ka da ta ci gaba da bata maka kunne.

Hakkin mallakar hoto Getty

Ka koyi wani harshe ko kida

Maimakon ka yi ta fama da wata manhajar bunkasa kwakwalwa ko wani wasan hada kalmomi, kamata ya yi ka yi wani abu mai muhimmanci sosai da zai taimaka wa kwakwalwarka.

Kamar koyon wani sabon harshe ko wani kayan kida, saboda dukkanin wadannan abubuwa suna tattare da jerin kalubale da za su horad da kwakwalwarka ta fannin hadda da natsuwa da sauran ayyukan kwakwalwa.

Wannan aiki ko atisaye zai taimaka maka ta hanyar da kwakwalwarka za ta kasance cikin wata gogayya ko aiki da tasirinsa ko amfaninsa zai kasance da kai har tsufanka.

Wani nazari da aka yi a shekarar da ta wuce ya nuna cewa mawaka suna da kariyar kusan kashi 60 cikin dari daga kamuwa da cutar mantuwa idan aka kwatanta su da wadanda ba sa kade-kade.

Wani binciken kuma ya nuna koyon wani harshe ka iya jinkirta zuwan wannan cuta ta mantuwa da shekara biyar.

Ko ba komai wannan zai taimaka maka ka fahimci kokarinka a wannan lokaci.

Kuma idan kana ganin aikinka ba zai ba ka damar koyon wani sabon abu ba, to ka dauka ka yi sa'a.

Saboda ayyukan da ke daukar hankalin mutum na taimaka masa wajen ci gaban kwakwalwarsa ko da yake ba lalle ya ci gaba da moriyar wannan alfanu ba bayan aikin nasa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Ka gu ji cin tarkacen abinci

Kiba na iya cutar da kwakwalwarka ta hanyoyi da dama. Idan maiko ya taru a jijiyoyin da ke kai jini kwakwalwarka, hakan zai hana jini da iska kaiwa ga kwakwalwar da take bukata ta yi aiki.

Haka kuma yawan cin abinci mai zaki da maiko zai iya kawo cikas ko rikita yadda jikinka ke samar da sinadarin insulin, wanda hakan zai iya rikita aikin jikinka da zai kai ga taruwar wani danko-danko a kwakwalwar.

Amma duk da haka akwai wasu sinadaran abinci kamar bitamin D da B 12 da omega 3, wadanda ga alama suke taimaka wa wajen maganin matsaloli ko illolin da ke shafar kwakwalwa.

Wannan kila shi ya sa tsoffin mutanen da ke cin abinci irin na mutanen yankin Bahar Rum kwakwalwarsu ke nuna kwarewa ko kokari kamar irin ta mutanen da basu kai su tsufa ba da shekara bakwai da rabi.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ka rika motsa jiki

Mukan bambanta tsakanin basira ko kwakwalwa da karfi. A gaskiya gina jiki daya ce daga cikin tabbatattun hanyoyin gina kwakwalwarka ko cuciyarka(tunani).

Motsa jiki ba kawai yana tabbatar da gudanar jini zuwa kwakwalwa ba ne, abu ne da kuma yake bunkasa samar da sinadarin da ke taimaka wa girman jiki da kuma tabbatar da dorewar sadarwa a kwakwalwa.

Amfanin hakan ya kama ne tun daga haihuwa har zuwa mutuwa, domin yaran da suke tafiya da kafa zuwa makaranta sun fi samun kyakkyawan sakamako.

Yayin da su kuma tsofaffi suke zama cikin natsuwa da tuna abubuwa idan suna dan tattaki wanda ke zaman motsa jiki.

Kawai abin da za ka yi shi ne ka duba irin motsa jikin da ya fi dace wa da kai ka soma.

Ka rika liyafa kamar dan shekara 21

Idan duka wadancan abubuwan da na bayyana maka kana ganin sun yi ma kama da aikin wahala, to wata hanya da ta fi wajen kare kwakwalwarka ita ce mu'amulla ta liyafa.

Mun san cewa mutane halittu ne masu mu'amulla, kuma alaka da mu'amulla da 'yan uwa da abokai na kara mana karsashi da kalubalantar mu mu jarraba wasu abubuwa na rayuwa tare da rage mana damuwa da bacin rai.

Wani nazari mai ban mamaki a kan tsoffi 'yan shekara 70 ya nuna cewa wadanda suka fi mu'amulla suna da damar kauce wa dakushewar kwakwalwa da kashi 70 cikin dari a cikin shekara 12 idan aka kwatanta su da mutanen da ba sa mu'amulla kamarsu.

Mu'amulla da mutane a kai a kai na taimaka wa kwakwalwa ta kowa ne fanni kama daga tuna abubuwa da hadda da saurin tunani.

Masana kimiyya dai na ganin ba wata hanya daya ta musamman ta horar da kwakwalwa. Amma dai mutanen da ke tsufa da tunaninsu da kwakwalwarsu da kusan komai nasu da kyau fiye da saura su ne wadanda suke dan yin kusan komai a rayuwarsu da ya danganci cin abinci iri daban-daban mai gina jiki da motsa jiki da kuma mu'amulla da abokanai na gari.

Kuma yin wadannan duka ba abu ne da za a ce ya yi yawa ba a matsayin hanya ta tabbatar da kwakwalwa na aiki da kyau domin tabbatar da rayuwa cikin lafiya da farin ciki.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Dos and don'ts to preserve your brainpower