Kana yawan daukar hoto?

Hakkin mallakar hoto babycakes Romero

Wani bincike ya gano cewa yawan daukar hoto da wayarka ta salula ko kyamara na iya sa ka manta muhimman abubuwan da suka faru ko ka sani.

Tiffanie Wen ta yi bincike:

Dukkanninmu mun taba yi akalla ko da sau daya ne ko ma fiye da haka, wato ka dauko 'yar na'urarka ka dauki hoto na kyakkyawan yanayi a lokacin da rana za ta fadi, ko kuma na wani abinci mai dan karen hadi da ya burge ka a wani kantin cin abinci.

Abu ne da yake a zahiri cewa muna kokarin haddace abubuwa ta yadda kwakwalwarmu ba za ta dusashe ba.

To amma yadda hanyoyi da na'urori suka yi yawa a zamanin nan kuma muke amfani da su barkatai sau nawa za ka dauki hoto da za a iya cewa ya yi yawa? Muna daukar hotuna da yawa?

Idan ka duba sakamakon binciken Farfesa Linda Henkel masaniya a kan tunanin dan-adam a Jami'ar Fairfield, za ka iya dauka cewa amsar ita ce e lalle muna daukra hotuna da yawa.

Bincikenta ya nuna cewa daukar hotuna da yawa ka iya sa ka kasa tuna wasu abubuwan a nan gaba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawan daukar hotonmu zai iya haifar mana da illa kan yadda muke tuna abubuwan da muka gani

A nazarin da ta yi daga shekara ta 2014, an umarci wasu dalibai da suka je ziyarar gani da ido wani gidan ajiye kayan tarihi, su dauki hotunan wasu abubuwan wasu kuma ka da su dauki hotunansu illa dai kawai su nazarce su.

Da aka jarraba su washegari, ba su iya bayar da bayanai sosai a kan abubuwan da suka dauki hotonsu ba.

Wannan shi ne abin da Henkel ta kira ''illar daukar hoto''

Henkel ta ce,'' ina ganin abin da yake kasancewa shi ne muna daukar na'urar daukar hoto a matsayin wata ma'adana''

''Muna daukar cewa wannan na'urar daukar hoto za ta tuna mana da duk abin da muka dauki hotonsa da ita, saboda haka ba sai mun takura kanmu mun hardace wannan abin ba.''

Ko da yake ta ce daukar hoton zai iya sa mana illa a haddarmu a dan gajeren lokaci, amma ta ce a can gaba hotunan za su taimaka mana tuna wasu abubuwa.

Abin ban sha'awa shi ne, wannan illa ta daukar hoto ta kau lokacin da aka ce daliban su jawo wani bangare na abin da suka dauki hotonsa kusa(zoom) ta yadda za su ga wannan bangare sosai.

Wannan na nuna cewa wannan karin mayar da hankali kan yin hakan na taimaka wa haddar da mutum yake yi ta abu a lokacin da na'urar daukar hoton ta dauko wani wuri mai yawa.

''Wannan ga alama ya tabbata gaskiya domin bincike ya sha nuna cewa raba hankali babban abokin gaba ne ga harda, '' in ji Henkel.

Wato idan kana son mutum ya kasa hardace abu to ka raba masa hankali.

Hakkin mallakar hoto Getty

Ba shakka shekara da shekaru muke jin bukatar daukar hotuna a lokacin da kusan a ce kowa ne gida a yammacin Turai da Amurka yana da na'urar daukar hoto.

To amma cigaba fasaha da aka samu inda aka samu sauyi daga kyamara irin ta da mai fim zuwa ta zamani, hakan ya kawo sauyi a kan dalilan da suke sa mu dauki hoto da kuma yadda muke amfani da hoton.

Bincike ya tabbatar abin da yawancinmu muke gani, na cewa yanzu amfanin hoto ba irin na da ba ne, inda muke daukar hoto domin tunawa da wani taro na musamman ko wani abu na iyali.

Yanzu yawanci ana daukar hoto ne domin sadar da wani sako ga abokanmu ko fayyace yadda muke da kuma kulla wata alaka.

Yayin da manya ko iyaye suke daukar hoto da kyamara ta zamani a matsayin wani abu na tuna baya, su kuwa matasa suna amfani da kyamara ta zamanin ne a matsayin wata hanya ta sadarwa.

''A yau mutane da dama suna daukar hoto ne ba wai domin tuna baya ba a can gaba, illa dai kawai su nuna yadda suke ji yanzu a nan, '' in ji Henkel.

''Duba tsarin Snapchat a misali za ka ga mutane na daukar wadannan hotuna ne domin sadarwa amma ba don tunawa ba.''

Hakkin mallakar hoto Getty

Kokarinmu na adana abubuwa ya samu gagarumin cigaba da bullar na'urar SenseCam ta Microsoft, wadda aka kirkiro a 2003.

Wannan na'ura za a iya kwatanta ta da na'urar nan ta nadar bayanan jirgin sama (black box) amma ta mutum.

Ita wannan na'ura tana iya daukar hoto a duk lokacin da ta ga mutum a gabanta ko kuma idan an samu sauyin haske sosai.

Sannan kuma za a iya tsara ta yadda za ta rika daukar hoto bayan duk dakika 30.

Evangelos Niforatos, mai bincike a Jami'ar Italiya ta Università della Svizzera Italiana, ya yi bincike kan yadda sabuwar fasaha za ta iya shafar haddarmu.

Mai binciken ya yi nazari sosai kan adana harkokin rayuwar mutum a yau da kullum har tsawon shekara uku.

Kodayake bincike ya nuna nadar bayanan harkokin mutum na yau da kullum ta hanyar amfani da kyamara zai iya taimaka wa wadanda suke da matsalar tuna abubuwa tare da sake gabatar musu da hotunan rayuwarsu a lokaci-lokaci, Nifaratos ya ce babbar matsalar da ke tattare da wannan tsari ga wadanda suke amfani da shi sosai ita ce yadda za su iya amfani da dukkanin bayanan da aka tattara.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Idan ka kalli abu ba tare da ka dauki hotonsa ba, kwakwalwarka na iya yin aiki tukuru ta haddace shi yadda za ka iya tuna shi a gaba

''Idan ana maganar amfani da wannan tsari ne na nadar bayanai da hotunan harkokin mutum na yau da kullum za a iya cewa abu ne mai amfani sosai.

Amma a ce za a yi amfani da shi a rayuwar yau da kullum to wannan kuma wani abu ne na daban'' in ji masanin.

''Amma muna da kwarin gwiwa cewa za mu sa yi ya zama kamar kwakwalwarka ta ainihi, wato dai kamar wata gaba ta jikin dan-adam ta roba kamar hannu ko kafa ko wani kamar haka, wanda zai tuno maka abin da kake son tunawa.''

Nifaratos da abokan aikinsa suna tsara wani bincike da zai danganta na'urar nazarin bugun zuciya da wadda ke bin diddigin aikin da mutum ke yi, domin ganin ko sauyi a bugun zuciyar mutum zai iya nuna lokacin da ya fi dacewa a fara daukar hoto.

Kyamara ta zamani ba kawai ta sauya yadda muke daukar hoto ba ne kadai ta kuma kawo sauyi kan abubuwan da muke adanawa sakamakon shafukan sada zumunta na intanet.

Hakkin mallakar hoto AP

Ka rage rage yawan daukar hoto?

To sau nawa ya kamata mu rika daukar hoto? Sai dai idan kai mai sana'ar daukar hoto ne amma, Henkel tana ganin yana da kyau ka rage yawan hotunan da kake dauka kuma ka rika zabar wanda ya kamat ka yi domin ka samu karin amfanin da ke tattare da daukar hoto da kuma rage illar yawan daukar.

''Idan kana wani wurin shakatawa ne a lokacin hutunka, yana da kyau ka dauki 'yan hotuna, sannan ka ajiye kyamararka gefe daya can ka shakata, in ji ta.

''A gaba kuma sai ka duba su, ka zabi na zaba, ka wallafa su ka samu lokacin da kai da sauran mutane za ku kalle su domin tuna baya.

Wadannan duka abubuwa ne da za su taimaka wajen ganin ba ka manta abubuwa.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Are you taking too many pictures?