Mutumin da ya yi nazarin mugunta

Hakkin mallakar hoto Getty

Me ya sa wadansu mutanen suke da matukar son kansu da wayo da yaudara da kuma tsabar mugunta da zalunci?

Tambayar da David Robson ya yi wa masanin kimiyyar da ya gudanar da bincike kan munanan dabi'un dan-adam ke nan.

Idan ka samu damar nike kwari a injin nika za ka ji dadin yin hakan? Ko da a ce kwarin suna da sunaye ka kuma san sunayen nasu kuma kana jin karar yadda injin yake nike su?

Ko za ka ji dadi a ce ka cika kunnen wani mutum da ke tsaye kawai a bakin titi wanda bai san ka ba kuma kai ma ba ka san shi ba da ihu mai karan gaske kawai don ka muzguna mi shi?

Wadannan na daga ire-iren jarrabawar da Delroy Paulhus ya yi amfani da su domin fahimtar mugayen cikinmu.

Masanin yana son kawai ya samu amsar da dukkaninmu watakila muke tambaya ko kuma muke son yi, wadda ita ce,''me ya sa wasu ke jin dadin yin mugunta?''

Ba wai kawai mutanen da ke da tabin hankali da masu kashe mutane ba, a'a hatta a makaranta inda wasu daliban ke cin zalin wasu da masu kutse a intanet kai har ma da shugabannin al'umma kamar 'yan siyasa da 'yan sanda.

Ya ce, ba wani abu ne mai wuya ba ka yi hasashe na gaggawa kuma mai sauki a kan wadannan mutane.

''Muna da dabi'ar danganta wasu mutanen da shedan, yadda muke daukar duniyarmu mu raba ta kashi biyu tsakanin mutanen kirki da kuma bata-gari,'' in ji Paulhus wanda ke Jami'ar British Columbia a Canada.

Duk da cewa Paulhus bai lamunci mugunta ba, amma ya bi tsarin nazarin ganin irin dadin da masu aikata miyagun abubuwan ke ji daga muguntar da suke yi wa mutane.

Paulhus ya fara ne da wanda ke son kansa, wanda zai yi duk wani abu na nuna son kai domin kare abin da yake gani kimarsa ce.

A lokacin, sama da shekara goma da ta wuce, wani dalibinsa Kevin Williams ya bayar da shawarar cewa su duba su ga ko wannan dabi'a ta kaunar kai fiye da kowa tana da alaka da wasu munanan dabi'un biyu.

Dabi'un biyu su ne, yaudara da hauka (mai sa fada ko mugunta da rashin tausayin mutane).

Malamin da dalibin nasa a binciken sun gano cewa kowacce daga cikin dabi'un na zaman kanta ne ko da yake a wani lokacin suna haduwa su haifar da abin da za a iya cewa, ''bakar mugunta''

Hakkin mallakar hoto Getty

Abin mamakin shi ne yadda mutanen da zai yi binciken da su za su fadi gaskiya a nazarin, domin tambayoyi ne kamar ''ina jin dadin cin zalin marassa karfi'' ko ''ya fi dacewa ka da ka gaya min sirrinka'', inda kuma abin da mutum zai amsa a nan shi ne ya amince da wadannan kalamai.

Kai kanka ka san cewa mutane za su ji kunyar amsa wadannan tambayoyi ko kalamai, amma dai a dakin bincike na kimiyya za su iya amsawa kuma amsarsu ta zo daidai da yanayin cin zali na rayuwar gaske kamar yadda ake gani a tsakanin matasa da kuma manya.

Haka kuma mutanen za su iya kasancewa su ki fadin gaskiya a binciken kamar yadda za su iya cin amanar abokan aurensu (kwartanci ko neman wasu mata a waje).

Duk da haka tun da dai Paulhus ba ya mayar da hankali a binciken nasa a kan masu aikata miyagun laifi ba ne ko masu tabin hankali, dabi'ar ba wai ta haduwar farko ba ce kenan.

Haihuwar mutum da mugunta

Fara gudanar da wannan bincike da Paulhus ya yi a kan mugunta ke da wuya sai saura suka biyo baya domin amsa wasu muhimman tambayoyi a kan yanayin mutum.

Misali ana haihuwar mutum da mugunta a zuciyarsa? Wani nazarin da aka yi a tsakanin tagwaye masu kama da juna da kuma wadanda ba su yi kama da juna ba ya nuna akwai alakar kwayoyin halitta sosai tsakanin dabi'ar cutar mutane domin son ran mutum da kuma tabin hankali (hauka na zaluntar mutane).

Ko da yake ita kuma dabi'ar yaudara ga alama tana kasancewa ne sakamakon yanayi na muhalli ko inda mutum ya samu kansa, za ka iya koyon yaudara daga wasu.

''Ba na jin akwai wanda aka haifa da kwayoyin halittar haukan zaluntar mutane kuma a ce ba abin da za a iya yi na magance hakan,'' in ji Minna Lyons ta Jami'ar Liverpool.

Hakkin mallakar hoto Getty

Idan ka kalli fim din James Bond da Don Draper ko Kordan Belfort a ''Wolf of Wall Street'' za ka gane cewa miyagun mutane suna da wata bukata kamar ta jima'i da suke samun gamsuwarta kawai ta hanyar mugunta kamar yadda sauran bincike na kimiyya suka tabbatar.

Za a iya gano sauran amfanin da suke samu kuma daga wata dabi'ar kuma ta mutum.

Wannan kuwa ita ce, kai mai harkokinka da dare ne ko kuma da safe kake yawan harkokinka.

Lyon da dalibarta Amy Jones sun gano cewa, mutanen da ake kira ''mujiya'' wato wadanda ba sa kwanciya da wuri kuma ba sa tashi da safe da wuri sun fi samun maki mai yawa a gwajin da ya shafi wata dabi'a ta dare.

Yawancinsu masu kasada, wanda wannan wata dabi'a ce ta masu tabin hankali da ke cutar da mutane kuma mutane ne da suka fi kasancewa masu yaudara kuma yadda suke masu son kansu sukan kzama masu dabi'ar ci da gumin wasu ko kuma gallazawa sauran mutane.

Za ka kara fahimtar hakan idan ka duba yadda yanayin rayuwar mutum ya samo asali daga mataki zuwa mataki.

Kamar yadda yake cewa mutanen da ke harkokinsu da daddare za ka ga sun fi kasancewa masu dabi'ar sata da yaudara da kuma badala (neman mata ko maza) a wannan lokacin da kowa yake barci.

Ko yaya gaskiyar wannan nazari take Paulhus yana ganin su dai mutanen da ke da wadannan dabi'u za su zalunci mutane bisa kowa ne dalili ne ma domin abu ne da ya zama jiki a wurinsu domin mutum yana da hanyoyi daban-daban na biyan bukatarsa, wasu sun kunshi halaye na gari wasu kuwa sai tsantsar mugunta. Kamar yadda masanin ya ce.

A kwanan nan ya ma fara zurfafa bincike kan zuciyar da ke sa mutane zalunci, yana mai cewa, ''tun da har mutane za su amsa cewa suna zaluntar wasu haka kawai ba wani dalili sai dai kawai domin jin dadinsu, wannan ya nuna ba daya daga cikin dabi'u ukun da muka bayyana a baya ba ne da ke sa mutane mugunta, wannan wata dabi'a ce ta zalunci ta yau da kullum wadda ya kira bakar 'yar hudu (dark tetrad da Ingilishi).

Injin nike kwarin nan ya bayar da dama ga Paulhus da abokan bincikensa dama ta sosai ta jarraba ko hallaka kwarin ta wannan hanya zai nuna ainahin rashin imanin da wasu mutanen ke nunawa a kan sauran mutane.

Sai dai a rashin sanin mutanen da za a yi gwajin rashin imanin da su wadanda za su halla kwarin, an tsara injin nikan ne ta yadda kwarin za su iya sulalewa ta wata kofa su shiga inda ba zai nike su ba, amma kuma za ka ji kara kamar yana nike kwansansu.

Wasu mutanen sun ce ba za su iya wannan rashin imani ba suka ki shiga, yayin da saura kuma cikin walwala da so da ma zakwadin kashe kwarin aka yi da su.

''Sun kasance cikin shirin yin wannan abu na nuna tsabar rashin imani ga kwarin har ma da bukatar kara yin hakan'' in ji Paulhus.

''Wasu kuwa gani suka yi abin tsabar rashin imani ne wanda ba ma za su iya zama a yi wannan abin a gabansu ba''.

Haka kuma wadannan mutanen da suka nuna rashin imanin kisan kwarin sun kuma sami maki mai yawa wajen tsabar mugunta a rayuwa ta yau da kullum.

Hakkin mallakar hoto Science photo library

A wani karin binciken kuma Paulhus ya gano cewa mutanen da ke da zuciya ta cin zalin mutane a rayuwa ta yau da kullum suna yin duk wani abu da za su samu damar yin hakan ba domin komai ba sai dai kawai domin dadin da suke ji daga wannan mugunta da suke yi wa sauran mutane.

Suna kuma jin dadin yin hakan duk da cewa ba wani lada ko wani abu suke samu ba sai dai kawai domin jin dadin kansu idan suka ga mutum na kokawa da wannan zalunci.

Masanin yana ganin wannan ya zo daidai da yadda masu zamba ko kutse ta intanet suke yi.

''Wadannan mutane sun zma kamar masu cuta ta intanet, wadanda suke yawo kawai su ga wanda za su zalunta.''

Abubuwan da ya gano a binciken nasa, sun ja hankalin hukumomin 'yan sanda da sojoji har suka nemi hada gwiwa da Paulhus domin ganin ko binciken zai bayyana yadda wasu mutane suke amfani da mukamansu domin muzguna wa wasu mutanen.

''Abin shi ne wadannan mutanen da sani za su iya zabar ayyukan da za su ba su damar gallazawa mutane'' ya ce.

Idan kuwa haka ta kasance to karin bincike zai iya nuna hanyoyin da ya kamata a rika bi wajen tantance mutane a yayin daukar aiki.

Hakkin mallakar hoto Getty

Haka kuma masanin ya nuna sha'awar gudanar da wani sabon binciken kan abin da ya kwatanta da amfani da zuciyar rashin imani ta hanyar da ta dace wato mutanen da za su yi amfani da ta'adarsu amma ba ta wata muguwar hanya ba (kamar yadda su suke gani).

A wani yanayin rashin imani na iya zama dole. ''Domin idan har za ka zama fira minista to sai ka tashi tsaye ka dage ba za ka zama wani mai sanyi-sanyi ba, dole sai ka kawar da tausayi ka rufe ido ka takura wa mutane kafin ka cimma burinka,'' in ji masanin.

''Ba za ka iya taimakon al'umma ba idan kawai ka zauna ka mike kafa a gida kana haba-haba da kowa.''

Dukkanin wadannan na daga abubuwan da muka dauka na cewa rayuwar mutum ta rabu biyu mai kyau da maras kyau, abin da Paulhus ke fafutukar tabbatarwa.

Ta wata hanya wannan abu ne da ya shafi rayuwar mutum a wata kuma abu da ya shafi aiki.

Shi kansa ya yadda cewa yana da wannan dabi'a ta mugunta, inda misali yake son kallon wasan da ya kunshi mugunta kamar karate ko damben zamani na boksin da makamantansu.

'' Ba zai dauki wani lokaci mai tsawo ba a gane cewa na zarta yawancin mutane a wannan ta'ada na mugunta, '' in ji shi.

''Amma saboda yadda nake zakuwa na son abu a matsayina na masanin kimiyya da kuma jin dadina na binciken wadannan abubuwa, ina ganin ina matsayin da ya dace na nazarin wannan mummunar dabi'a ta mugunta.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Psychology: the man who studies everyday evil