Dogo ko Gajere : Wanne ne ya fi?

Hakkin mallakar hoto Getty

Babban abu ya fi karami ko kuma an fi samun abubuwan da suka fi a kanana? Kuma idan da an ba ka zabi dogo za ka zama ko gajere?

David Robson ya bincika mana.

Tsawonka halitta ce da ba za ka iya sauyawa ba, amma duk da haka abu ne da zai iya yin tasiri sosai akan duk abin da za ka zama ko iya zama ko kuma samunka a rayuwa ta inda ba ka sani ba.

BBC ta gudanar da bincike kan shedar da masana suka gabatar domin ganin tasirin tsawon a kan komai kama daga yadda mace za ta yi sha'awarka ko namiji ya yi sha'awarki zuwa asusun bankinka da kuma tsawon rayuwarka.

Kudi da Iko

A tsawon Abraham Lincoln na kafa shida da inci 4 (6ft 4in) ko santimita 193 (193cm) ya zarta Obama wanda shi kuma ya wuce tsawon yawancin Amurkawa (177cm) da santimita takwas (8cm) ko kuma inci uku (3in).

Wani nazari da ya tabbatar da alakar tsawon mutum da farin jininsa, ya tabbatar da cewa wadanda suka fi tsawo sun fi samun yawan kuri'a a zabe.

Bayan zaben shugaban Amurka ma, bincike ya nuna ana ganin dogayen mutane maza ko mata sun fi tabbatar da iko da lafiya da basira sannan kuma an fi zabensu a wasannin da suka kunshi gasa, sannan sun fi samun kudi a kan gajeru.

Ko da yake dai zai iya kasancewa mun fi danganta tsayi da nasara da kuma iko a rayuwa, wato abubuwa biyu da ke da alaka da shugabanci.

To amma duk da haka tsawo na nuna alamun samun abinci mai gina jiki a lokacin yarinta.

A don haka za a iya cewa abu ne da ke nuni da yadda ka samu kulawa a lokacin da kana yaro har ka taso, wanda hakan zai iya yin tasiri a iliminka da kuma nasararka can gaba a rayuwa.

To amma ba dukkanin wadanda suka yi nasara ba ne a rayuwa za a ce dogaye ne, domin kamar Winston Churchill da Martin Luther King suna da kwarjini duk da cewa gajeru ne.

Amma idan ana maganar farkon gani ne sai a ce dogaye sun fi kwarjini.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dogayen maza ka iya zama takaici a gado ba don janye gaba dayan mayafin ba kawai

Farin jini wajen mata ko maza (na sha'awa)

Dogayen maza sun fi ba da sha'awa. Bincike da nazari da dama da aka yi sun nuna dogayen maza da mata sun fi jan hanakali a kan gajeru.

Abin mamakin ma shi ne za ka iya fahimtar mutum dogo ne ko gajere daga hoton fuskarsa.

Wato ba yadda mutum zai boye alamun gajartarsa ko da a hoton da ya sa a shafin sada zumunta da mu'amulla na intanet na samartaka ko zawarci.

Sai dai duk da cewa za su fi kima a fagen gasar zabar masu tallata kaya na zamani (supermodels) dogayen mata ba su da farin jini sosai a wurin samun samari domin an fi son masu tsawo tsaka-tsaki.

Haka ma a tsakanin maza tsawo zai iya kasancewa alheri ta wani fannin kuma ya kawo cikas, idan mutane suka yi la'akari da wasu abubuwan bayan tsayi.

Wani nazari da aka yi kwanan nan ya duba yadda mata suke la'akari da girman azzakari.

Abin da aka gano shi ne yawan tsayin mutum yawan yadda mata suke la'akari da girman azzakarinsa wajen sha'awarsa.

Wato idan mutum yana da tsawo mace za ta yi tsammanin yana da girman azzakari hakan sai ya sa ta kara ganin kyawunsa.

Idan kuma ya ksance ga shi dogo amma azzakarin nasa ba shi da girma, to ba zai ja hankalin mace ba.

Amma fa ba a ko da yaushe ba ne maganar da wasu ke yi kan mazan da suke da katuwar kafa cewa suna da babbar mazakuta.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Girman jiki zai iya sa mutum karfi amma kuma ba kuzari ko sauri sosai

Wasanni

Da ka duba fagen wasan kwallon kwando da wurin gasar tsalle-tsalle da guje-guje za ka san cewa dogayen kafafauwa na da rana a wasanni da yawa.

Dogayen hannuwa da kafafuwa za su fi sauri da kaiwa wuri mai mai tazara fiye da gajeru.

Wani abu ma shi ne a wasan kwallon zari-ruga (american Football) dan wasan da ya fi tsawo za ka ga yana iya cilla kwallo ta kan abokin karawarsa wanda bai kai shi tsawo ba wanda hakan ba karamar dama ba ce ta yin nasara.

Sai dai a wani lokacin karamin jiki ko gajarta ita ma tana da ranarta.

Sadarwa tsakanin kwakwalwa da hannuwa da kafofi ba ta daukar dogon lokaci a wurin mutumin da yake gajere, saboda nisan dake tsakanin gabobin ba shi da yawa kamar na dogon mutum.

Saboda haka za ka ga gajeren mutum ko kuma maras tsawo yana da kuzari sosai, wannan yana taimaka musu a wasannin fada kamar yadda za ka iya ganin Jackie Chan.

Haka kuma abu ne mai wuya ka tankwara jikinka ka juya idan kana da tsayi, wanda kuma za ka ga masu karamin jiki suna iya yin hakan cikin sauri da sauki.

Wato dai suna yin fice a wasannin linkaya da sulun kankara da na tsalle da adungure da juye-juyen jiki (gymnastics) da makamantansu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu girman jiki sun fi rashin kintsi da samun hadari?

Rashin kintsiko tsari

Ka dauka jikinka kamar mota yake. Za ka ga yawan girman motarka yawan wuyar da take da ita wajen kaucewa karo ko tsayar da ita idan za ka yi karo.

Kuma hakan ke nan na nufin tun da tana da girma idan aka yi karon za a fi yin illa a kan motar da ba ta da girma.

Haka kuma gajerun mutane ba sa bukatar wani wuri mai nisa su fadi, kamar yadda wani kiyasi ya nuna mutumin da ya fi tsawo da kashi 20 cikin dari sai ya samu gudu kashi biyun na wanda ya fi tsawon a yayin da zai fadi.

Ga lama wannan zai iya fayyace dalilin da ya sa dogayen mutane suka fi fuskantar hadarin jin ciwo a rayuwarsu.

Alkaluma sun nuna cewa matan da suka kai tsawon kafa biyar da inci takwas (5ft 8in) sun fi hadarin jin rauni a kugunsu kashi biyu a kan matan da tsawonsu yake kafa biyar da inci 2 (5ft 2in).

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ko tsayi hadari ne ga lafiyar mutum?

Tsawon rayuwa da lafiya

A duk girman nahiyar Turai garin Villagrande Strisaili da ke tsibirin Sardinia na kasar Italiya a tekun Bahar Rum ya fi yawan mutanen da suka kai shekara dari a raye.

Duk da cewa ana ganin akwai wasu abubuwan da suka sa suke kai wadannan shekaru a raye, wadanda suka hada da irin abincin da suke ci da rayuwar walwala da suke yi, wani dalili da ake dangantawa da hakan shi ne, yawancinsu ba su da tsawo kuma ba su cika gajarta ba (tsaka-tsaki ).

Yawanci namiji tsawansa kusan kafa biyar ne da inci uku ko santimita 160 a cikin tsofaffinsu.

Wannan abin mamaki ne domin a can baya an ji cewa yaran da suke da koshin lafiya sun fi tsawo, saboda haka za ka dauka cewa tsayi alama ce ta cikakkiyar lafiya ta kowa ne fanni.

Amma idan aka yi la'akari da sauran abubuwa kuma kamar abinci mai gina jiki da tsarin kula da lafiya za a ga dogayen mutane suna shan wuya idan suka kama hanyar tsufa.

Misali yawan girman jikinka yawan kwayoyin halittar da ke jikinka, wanda hakan karin yuwuwar samun cutar daji ne

Haka kuma jiki mai girma zai iya bukatar karin aikin jiki, wanda hakan yake fitar da guba wadda za ta iya kara zagwanyewar jiki.

Sakamakon hakan zai iya rage maka shekaru da dama na rayuwarka, kamar yadda aka gani a tsakanin mutanen tsibirin Sardinia, inda dogayen cikinsu ba su kai wadanda suka fi tsawo ba rayuwa da shekara biyu.

Wani binciken kuma a kan mutane miliyan daya da dubu 300 na Spaniya ya gano cewa a duk karin tsawon santimita daya da mutum yake da shi yana da ragin digo bakwai (0.7) a yawan shekarun da ake sa ran zai yi a duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ko dogayen mutane sun fi samun sauki a rayuwa?

Farin-ciki

Duk da wadannan matsaloli da ke tattare da tsayi akwai alherin da kuma ke tattare da shi.

Misali wani bincike ya nuna cewa yawan tsawonka yawan yadda za ka samu damar farin ciki da jin dadin rayuwa.

Wannan zai iya kasancewa kamar yadda bincike a baya ya tabbatar cewa tsawonka zai iya yin tasiri ka samu aiki mai samu sosai ko kuma nasararka a rayuwa yadda ka samu kudi da yawa.

Hakan na nufin dogayen mutane za su fi iya samun saukin rayuwa a kan marassa tsawo.

Matsaya: Yawan tsawonka yawan farin-cikinka

Ana ganin dukkanin wadannan abubuwa ne da suka dogara ga wasu kafin su tabbatar da amfani ko illar tsayi ko gajartar mutum.

Akwai abubuwan da suke sabawa dukkanin sharudda da dokokin da ake dangatawa da tasirin tsayin da su.

Dukkanninmu akwai yadda tsarin halitta ya ajiye mu da irin sa'a ko rashin sa'ar da za mu iya samu, amma kuma rabon ya ksance daidai wadaita da kowa zai samu daidai da shi.

Ko yaya girman jikinka yake akwai daidai kasonka. Watakila za a iya cewa dukkanin wannan kiyasi ko kididdiga na tabbatar da gaskiyar maganar nan da ake cewa, nasararka a rayuwa ba ta dogara ba ne ga girman jikinka sai dai yadda ka yi amfani da jikin.

Kuma wannan shi ne gaskiyar lamarin ba dadi (tsayi) ba ragi (gajarta).

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Tall vs short: Which is it better to be?