Hatsabiban jiragen yakin Amurka

Hakkin mallakar hoto usaf

Daya daga cikin tarin jiragen yaki da hukumar kula da sararin samaniyar Amurka ta mallaka shi ne mai kama da gidan mai a sararin sama.

Abin tambaya shi ne me ya sa hukumar ta ke da tarin jiragen yaki kuma na musamman duk da cewa ita ba hukumar tsaro ba ce?

Stephen Dowling ya bincika:

Wani sabon hoton bidiyo da aka fitar kwanan nan ya nuna cikin dakin matukin jirgin saman mai zuba wa jirage mai a sama na hukumar kula da sararin samaniyar Amurka.

Suna kiran wadannan jirage masu rakiya. Tarin jiragen yaki ne irin wadanda rundunar sojin saman Amurka take amfani da su da takwararta ta ruwa da kuma dakarun sojin Amurkan na musamman.

Hakkin mallakar hoto nasa

Sai dai wadannan jiragen yaki masu gudun tsiya su suna da wani aiki ne daban, inda ake amfani da su wajen horad da matukan jiragen sama su juye zuwa 'yan sama jannati da gadin jiragen sama jannati na hukumar kula da samaniya ta Amurka da kuma zaman na gwaji.

Hoton bidiyon jirgin da aka bayyana ga jama'a ranar 27 ga watan Mayu da ya wuce, yana nuna yadda matukin jirgin yaki ne samfurin F-15D yana kukkurdawa da dabarar yadda zai sha mai a saman daga wani jirgin sama samfurin KC-135 da ke zaman na dako da shayar da jirage mai a sama.

Ana horad da matuka jirgin sama yadda za su yi amfani da wannan jirgi da tamkar za a iya kiransa gidan mai a sama, su sha mai a jiragensu yayin da suke tafiya mai dogon zango.

Hanyar shan man na bukatar kwarewa sosai, domin matukin jirgin yakin samfurin F-15, sai ya dawo da jirginsa bayan mai dauki da man wanda bai kai na yakin tafiya ba, sannan ya daidaita jirgin nasa ta yadda wata mesa ta jirgin man za ta shiga tankinsa ya sha man.

Can a jelar jirgin man akwai abin da ke saiti idan akwai bukatar hakan domin a tabbatar komai ya wakana daidai.

Hakkin mallakar hoto usaf
Image caption Jiragen yaki suna shan mai ta sama a kai a kai. Amma ana bukatar kwarewar matukin jirgin da zai yi haka

Me ya sa hukumar kula da sararin samaniyar Amurka take da wadannan jiragen saman yaki masu gudu irin wadanda sai hukumomin soji masu kudi ne suke amfani da su?

Tun farko-farkon kafa hukumar yana daga tsarinta ta mallaki irin wadannan jiragen yaki masu gudu.

Kuma a shekarun 1960 aka sabunta tsarin jiragen yakin kamar samfurin F-104 masu siffar makamin roka domin a rika amfani da su wajen gwajin gudu da shawagin koli-koli (sama sosai).

Hakkin mallakar hoto nasa

Yawanci ana amfani da jiragen saman yakin masu gudun ne yadda za su rika samar da tsaro ga sauran jiragen saman hukumar (samaniyar ) Nasa, idan suna tafiya.

Matukan jiragen kamar karin masu gadi ne na musamman a lokacin gwajin jiragen na Nasa. Suna kuma zaman aikin kyamarar daukar hotuna.

Hukumar ta Nasa ta yi amfani da jiragen saman yaki samfurin T-38 Talon na bayar da horo, irin wadanda ake amfani da su wajen koyad da sojin sama na Amurka.

Hukamar na amfani da jiragen samfurin T-38 domin kare jirgin sama jannati idan ya sauka a kasa.

Daga cikin jiragen saman yaki na hukumar sararin samaniyar Amurkan akwai samfurin F-15 da irin jirgin yakin sama na sojin ruwan Amurka samfurin F/A-18 wadanda dukkaninsu biyun a kan yi gwajin shawagi da su.

Sannan ana amfani da su wajen tabbatar da ganin wadanda za su zama 'yan sama jannati na gaba sun ci gaba da iya tuka jirgin saman.

Domin idan kan koyon tukin jirgin sama jannati zuwa sararin samaniya kana bukatar kwarewa wajen tuka wani jirgin da ya fi jirgin sama na sosai.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Nasa's fleet of fighter planes