Hadarin da ke tattare da jima'i

Idan kusanci ya yi kusanci ( jima'i) ya yuwuwar samun ciki ko kuma ma mutuwa sakamon bugun zuciya a sanadin saduwar take?

David Spiegelhalter ya bincika:

Jima'i: kowa- i to, lalle kam a iya cewa kusan kowa na yi. To amma kamar yadda sauran wasu abubuwa na jin dadi suke tattare da hadari shi ma jima'i yana da irin nasa hadari.

Cikin shege ko kamuwa da cuta na daga fitattun hadarrun da ke tattare da shi.

Haka kuma akwai hadarin samun bugun zuciya yayin jima'in ko a ji ciwo idan gado ya karye.

kai ba wadannan ba ma, akwai ma yuwuwar a kama ku kuna yi a inda bai dace, kila wani lungu ko sako na jama'a.

To kenan dai abin da yake kamar wani mai sauki a wurin wasu akalla, ashe ba haka yake ba domin ga alama yana tattare da wasu abubuwa da dama da za a iya cewa masu girma ko sarkakiya.

Hakkin mallakar hoto Think Stock

Wannan na nufin ke nan sai mu fara neman alkaluman da suka dace domin gano yadda girman wadannan hadurra da ke faruwa galibi a daki kuma a kan gado yake.

Bari mu fara da wannan tambaya, kamar yadda yawanci suka yi da saduwa kawai tsakanin namiji da mace ba tare da sanya wani abu na kariya ba ( kororo); ya hadarin yadda wannan saduwa za ta kare da ciki yake?

Wannan bisa dalilan da aka sani ba abu ne mai sauki ba a iya nazarinsa a dakin bincike na kimiyya.

Kamar yadda aka ga wani bincike da aka yi a New Zealand, inda aka bukaci wadanda suka shiga binciken su yi jima'i sau daya kawai a wata, lamarin da ya sa da dama daga cikinsu suka fice saboda sun kasa bin wannan ka'ida.

Watakila alkaluman da za mu ce sun dan fi kusanci da ingantattu su ne na wani nazari da aka yi a Turai wanda ya kunshi matasan ma'aurata ( miji da mata) 782.

Dukkanin ma'auratan sun rika tattara bayanan saduwar da suke yi ta kullum ba tare da wani magani ko kariya ta daukar ciki ba, har sai da aka sami juna biyu 487.

Hanya mafi sauki da za a iya kiyasin damar daukar ciki ita ce a yi amfani da wa'adin da aka sadu sau daya kawai (misali a ce a wata daya ko wata biyu da sauransu).

Lokacin da aka fi damar daukar ciki ga alama yana kasancewa ne kwanaki biyu kafin kwan halitta na mace ya je mahaifarta inda zai hadu da na namiji idan an sadu.

A wannan lokaci damar daukar ciki kashi 25 ce cikin dari kamar yadda kididdiga ta tabbatar a baya.

Amma bayan wannan lokacin kuma damar sai ta ragu matuka zuwa kashi biyar cikin dari kawai a sauran kwanakin wannan lokaci.

A takaice jima'i sau daya a tsakanin matasa yawanci zai iya samar da ciki ne a ma'arauta daya a cikin ashirin.

Wannan na nuna cewa damar za ta iya zuwa a kowa ce rana, ba sai wata rana takamaimai ba, domin wadannan abubuwa sun fi faruwa ne a yayin da kake matashi.

Lissafin nasara

To bayan wannan bayani ya damar samun ciki take a tsakanin yawancin ma'aurata da suke son haihuwa?

Masu nazarin yawan jama'a sun bayyana yadda damar daukar ciki take a cikin wa'adi daya na haila.

Amma wanna ba shakka ya bambanta tsakanin ma'aurata daban-daban amma kiyasin da aka yi na yawanci shi ne tsakanin kashi 15 zuwa 30 cikin dari a kasashe masu arziki.

Idan muka dauki wannan karamin adadi ko alkaluma za mu iya kiyasin cewa kafin yawancin ma'aurata da suke son samun karuwa (ciki) akwai yuwuwar kashi 85 cikin dari ta saduwa a kowa ne wata ba tare da samu ba.

Idan muka dauka kowa ne wata daya yake kuma bai dogara da wani watan ba, to sai mu ce rashin damar daukar cikin ta kai 0.85 sau 0.85 linki 12 ( watannin shekara), wato kashi 14 cikin dari ke nan.

Ma'ana ke nan damar daukar ciki (a wa'adin haila daya) ta kashi 15 cikin dari na nufin 100 a kwashe 14, kashi 86 cikin dari ke nan ake da damar daukar ciki a shekara daya.

Yawanci kuma ana bayar da kashi 90 cikin dari ne a matsayin damar daukar cikin a shekara a tsakanin matasan ma'aurata, masu sa ran karuwa ba tare da sun yi amfani da wani abu na hana daukar ciki ba, wanda kashin daukar ciki a wa'adin haila daya nasu ya kasance kashi 18 cikin dari ke nan.

Rage hadari

Hakkin mallakar hoto

To amma idan a dauka ba kwa son ku samu karuwa (ciki), yaya tasirin hanyoyin hana daukar ciki yake ke nan?

Ana bayyana wannan ne gaba daya a matsayin yawan cikin da ake samu a tsawon shekara daya da amfani da tsarin da aka zaba, kuma hakan ya dogara ne sosai ga yadda aka kiyaye ka'ida.

Hanyoyi kamar na amfani da kwayoyi da sanya roba a farji da allura an ruwaito suna tasiri kashi 99 cikin dari, wato kasa da mace daya ce a cikin dari da ke amfani da su za ta dauki ciki bayan shekara daya.

Shi kuwa kororon roba na maza yana tasiri ne kashi 98 cikin dari idan aka yi amfani da shi yadda ya dace.

Nau'in robobin da ake sanya wa mata a cikin mahaifa (diaphragms, caps) masu dauke da maganin kashe kwayoyin maniyyin namiji su tasirinsu an ce ya kai kashi 92 zuwa 96, wanda ke nufin tsakanin mata hudu da takwas da suke amfani da su za su dauki ciki a kowa ce shekara.

Wadannan alkaluma suna da muhimmanci musamman idan ana son rage yawan cikin shege da 'yan mata ke yi.

A shekarar 1988 a Ingila 'yan mata 41,000 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 ne suka yi ciki a waje.

Wato 'yan mata 47 ke nan a duk cikin 'yan mata 1,000 ko budurwa daya a cikin duk 'yan mata 21.

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Yunkurin gwamnatin Burtaniya na rage wannan adadi na 'yan mata da suka yi ciki a waje akalla da rabi, daga lokacin zuwa shekara ta 2010 bai yi tasiri sosai ba.

Saboda zuwa shekara ta 2009 yawan ya ragu ne zuwa 'yan mata 38 a cikin duk 1,000, wato raguwar kashi 19 cikin dari ke nan maimakon burin gwamnatin na rage kashi 50 cikin dari.

Kashi 49 cikin dari na wannan cikin shege da 'yan matan suka yi a Burtaniya an zubar da shi amma duk da haka da dama sun haife.

A shekara ta 2001 wani rahoto da hukumar kula ta yara ta Majalisar dinkin duniya UNICEF ta fitar ya nuna cewa Burtaniya ta fi sauran kasashen Turai samun wannan haihuwa ta 'yan mata inda mata 30 a cikin 1,000 masu shekaru daga 15 zuwa 19.

Kuma Amurka ce kawai ta wuce ta a tsakanin kasashe masu arziki inda ita kuma 'yan mata 52 a cikin 1,000 suke haihuwa a waje.

Wannan ya saba sosai da abin da ake samu a kasashe kamar su Koriya da Japan da Switzerland da Netherlands da kuma Sweden wadanda dukkaninsu 'yawan 'yan matan da suke haihuwa a kwararo bai kai bakwai a cikin 1,000 ba.

Kogi ne kawai ya raba kasar Netherlands da Burtaniya amma duk da haka matasanta suna da bambanci da na Burtaniyan kan yadda suke tunkarar jima'i.

Abin kaico

A karshe ba za mu manta da hadarin da ke tattare da wannan gogayya (jima'i) ba.

A shekarar 2011 masu bincike sun yi kiyasin cewa mutuwa daya a cikin 45 ta bugun zuciya ta faru ne sakamakon jima'i.

Fitattun mutane kamar Nelson Rockefeller da Errol Flynn da Shugaba Felix Faure na Faransa da wadansu fafaroma-fafaroma biyu duka an ce ta haka suka mutu.

A da a kan danganta masu dabi'ar wasa da al'aurarsu da sauran sassan jikinsu domin jin dadin jima'i da makanta da tsumburewar jiki, abin da kuma babu wata sheda mai yawa a kai.

Ma'ana a da ana cewa mai wasa da jikinsa har ya samu biyan bukata ta jima'i yana tattare da zama makaho ko jikinsa ya tsumbure.

Wasu na ganin wannan dabi'a a matsayin hanyar tsira daga hadurran da ke tattare da jima'i, ko da yake sun ce idan ta kunshi daukewar numfashi ba sa bayar da shawarar a yi musamman ga mutumin da yake dari-dari.

Saboda akwai mutane da yawa da suka mutu a sanadiyyar hakan, wadanda suka hada da dan wasan fim David Carradine da mawaki Michael Hutchence da wani dan majalisar dokokin Burtaniya.

Wani bincike ma ya gano mutane 117 ne suka mutu ta wannan dabi'a a lardina biyu kawai a kasar Canada.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Sex: What are the chances?