Matakai shida na karfafa kudiri

Hakkin mallakar hoto olivia howitt
Image caption Rike fitsarinka na iya taimaka maka kauce wa yin hukunci ko matakin da ba tunani a cikinsa

Bayan basira, kudiri shi ne abu daya mafi muhimmanci da amfani wajen cimma nasara a rayuwa.

Ga bayanin wasu hanyoyi masu sauki domin kula da kanka yadda ya kamata ta yadda za ka cimma burinka kamar yadda David Robson ya gabatar.

Abin mamaki, Firai ministan Birtaniya David Cameron, kamar yadda ya yi ikirari ya ce shi kansa yana amfani da wannan dabara kafin duk wani muhimmin taro.

Dabarar ita ce yayin da kwakwalwa take mayar da hankali kan wani aiki, sauran sassanta sai su kuma su kula da wasu ayyukan.

Misali a wani bincike ko nazari da aka yi, an bukaci mutanen da za a yi nazarin da su, su sha wani ruwa mai zaki.

Kafin su tafi bandaki sai aka ba su damar yin wani dan aiki da za a biya duk wanda ya tsaya ya yi wasu 'yan kudade.

Wadanda suka damu da zuwa bandakin ba su damu da wannan dan kudin da za a ba su ba saboda haka sai ba su tsaya sun yi aikin ba, domin zuwa bandakin ya fi musu muhimmanci saboda damar da za su samu ta tsayawa cikin natsuwa (ba sa jin fitsari ko kashi) su yi abin da ya fi dan wannan kudin a gaba. Wannan wani babban misali ne na auna karfin kudurin mutum.

Masana tunanin dan-adam suna ganin kudiri wani abu ne mai iyaka wanda za ka iya karad da shi a tsawon rana.

Ba shakka ba za mu iya zabar lokacin da za a jarraba natsuwarmu ba, amma mu sani cewa a duk lokacin da muke bukatar yin hukunci a kan wani muhimmin abu na rayuwarmu, misali sayen sabuwar mota ko kashe aurenka ko aurenki, zai fi dacewa ka dauki lokaci ka tsaya ka yi tunani sosai da daddare lokacin da ka kwanta.

Idan ba haka ba, za ka wayi gari da safe cike da nadama da da-na-sani.

Hakkin mallakar hoto olivia howitt
Image caption Ka kwanta da tunaninka a zuci: Ba kasafai zuciya za ta iya sa mu aikata wani abu na bacin rai ba da safe

Natsuwa tana amfani da karfin da kwakwalwa ta adana na ko-ta-kwana, ma'ana ba ka da natsuwa da kwarin gwiwa idan kana jin yunwa.

Akan haka ne wani bincike ya gano cewa alkalai suna hukuncin da bai dace ba kafin cin abincinsu na rana.

Haka kuma wannan dalili ne dai ake ganin ya sa muke da saurin fushi a kusan lokacin cin abincinmu na dare ( kamar yadda ake cewa mutumin da ke jin yunwa ransa a bace yake).

Amma idan ka samu dan wani ruwan lemo mai zaki ko makamancinsa ka sha, wannan zai dawo wa kwakwalwarka tanadin nan na ko-ta-kwana da ka yi amfani da shi.

Hakkin mallakar hoto olivia howitt
Image caption Sha wani ruwa mai zaki: Kara yawan sukarin cikin jininka zai iya kara maka kwarin gwiwa wanda zai iya sa ka yanke shawara mai kyau

To amma fa hakan ba dabara ce mai kyau ba idan kar kana kokarin kiyaye lafiyarka.

Hakkin mallakar hoto olivia howitt
Image caption Ka rika dariya: Idan muna cikin farin ciki mun fi jure yanayin damuwa zuwa lokaci mai tsawo

Ko da yake kudiri zai iya kare maka a rana ( musamman idan kana jin yunwa) akwai hanyoyin dawo da shi. Wasan barkwanci ko na ban-dariya na daya daga cikin wadannan hanyoyi.

Wani nazari ya gano cewa mutanen da suka kalli wani hoton bidiyo na ban-dariya sun fi samun natsuwa bayan kallon. An ce za su fi jurewa shan wani magani maras dadi a baki, domin amfanin lafiyarsu.

Hakkin mallakar hoto olivia howitt
Image caption Natsuwa: Zama shiru cikin natsuwa zai sa ka fuskanci abin da ka sa a gaba sosai

Natsuwa yawanci ta kunshi yanayi na yadda mutum zai danne zuciyarsa kan wasu abubuwa masu wahala kamar misali bacin rai, yayin da ka mai da hankalinka kan amfanin da kake hange da zai iya biyo bayan natsuwar.

Wani abu mai muhimmanci shi ne tunani cikin natsuwa zai taimaka maka ka tsaya a tsakiya ba tare da wani mummunan yanayi ko abu ya ja ka bangarensa ba, ta yadda za ka cigaba da gudanar da abubuwanka yadda kake bukata bisa burin da ka sa a gaba.

Hakkin mallakar hoto olivia howitt
Image caption Ka daina jin kai mai laifi ne: Idan kana jin kai mai laifi ne za ka yi ta tunanin aikata abu na bacin rai. Saboda haka ka rika juriya a kai a kai

Wata dabara daya mai sauki ita ce ka sanya hankalinka a kan sassa daban-daban na jiki kana lura da yadda kowa ne sashe yake ji.

Zuciya tana danganta laifi da jin dadi, ma'ana muna jin dadin yin wani abu maras kyau idan dai har zuciyarmu ta raya mana cewa wannan abin ba shi da kyau, domin aikata laifin kansa na sanya mu nishadi.

Sabanin wannan kuma dan abin da kake bukata da zai taimaka maka tsaya wa a kan kudirinka, shi ne ka zama kana da dan karfin halin cewa abin da kake yi ba laifi ba ne.

Saboda haka idan ka ga kana dan kaucewa daga hanyar burin da ka sa a gaba, ka da ka damu kanka sosai.

Kawai ka dauki hakan a matsayin wani dan rauni, wanda ba a rasa ba na dan lokaci da zai kauce ka ci gaba da fafutukar cimma burinka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Six steps to stronger willpower