Hanyar hasashe da ta fi

Hakkin mallakar hoto Getty

Wasu mutanen suna da baiwar yin hasashe a kan abubuwan da ke wakana a duniya, kuma kai ma za ka iya zama daya daga cikinsu in ji David Robson

Ka yi waiwaye ka duba wasu abubuwa na rikice-rikice da suka faru a duniya a baya-bayan nan. Ka hangi nasarar Shugaba Obama tun ma kafin ya zama dan takarar jam'iyyar Demokrat, ko kuma Hillary Clinton ka mara wa baya?

Yaya maganar iskar juyin juya halin kasashen Larabawa, ka ga alamar iskar tun da farko a yadda jama'ar kasashen ke nuna alamun rashin gamsuwa?

Kuma ka taba yin hasashen rikicin Ukraine na yanzu?

Idan har amsarka a kan wadan nan tambayoyi ta zama e, to sai a ce za ka iya zama kwararren mai hasashe, wanda zai iya hangen abubuwan mamaki da za su faru a duniya ya kuma yi hasashen yadda za su kasance daidai.

Wannan ba yana nufin sai ka kasance wani kwararren mai fashin bakin harkokin siyasa ba ne ko dan duba.

Wasu kwararrun masu hasashen mutane ne kawai kamar kowa, daga kowa ne fanni na rayuwa, wadanda kawai suke iya tsinkayen abubuwa da kyau.

A 'yan shekarun da suka wuce masana tunanin dan adam sun gano tarin baiwa da wasu mutane ke da su wadanda kuma ba lalle a iya gano su ba a wurin wadan nan mutane.

Misali akwai mutane masu baiwar gane mutum ko da kuwa sau daya suka taba ganin fuskarsa a shekaru.

Wasu mutanen kuma suna da baiwar gane dandano ne yayin da wasu kuwa suke da baiwar tuna lokaci da yadda abubuwa suke faruwa a yau da kullum.

Wannana baiwa duka za ta iya kasancewa ne sakamakon irin yadda kwayoyin halittarmu suke, yayin da hasashe shi kuwa zai iya kasancewa ne ta hanyar kwarewa da kuma koyo.

Amma kuma duk da haka kwararun masana harkokin siyasa sukan yi hasashen da ba ya tabbata.

Philiip Tetlock na Jami'ar Pennsylvania ya gano cewa wadan nan manyan masu hasashe sukan dan yi sa'a ne kawai.

''Ko da birai ne suka yi hasashen za su iya dacewa kamar kwararun,'' yadda wani masanin kimiyyar siyasa ke nan ya takaita bayanin a Jaridar New York Times.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumomin leken asiri suna da sha'awa a kan ayyukan bincike na iya hasashe

Ba shakka hukumomin leken asiri na soji su kan yi nazari tare da la'akari da ire-iren hasashen da a kan yi sosai.

A irin hakan ne hukumar gudanar da binciken leken asiri ta sojin Amurka ga alama sakamakon rahoton Tetlock ta yi sha'awar daukar nauyin gudanar da bincike na shekara hudu kan gano hanyoyin yin hasashe mai kyau a kan siyasa.

A karkashin shirin, hukumar ta dauki dubban mutane daga fannoni daban-daban domin gwada kwarewarsu ta hasashe a kan tambayoyi da dama kamar, ''shugabancin Robert Mugabe na Zimbabwe zai kare zuwa 30 ga watan Satumba na 2011?''

Ko '' Kasar Girka za ta ci gaba da kasancewa a kungiyar kasashen Turai ta EU har zuwa ranar daya d=ga watan Yuni na 2012?''

Maimakon amsar e ko a'a, wadda ba za ta iya nuna rashin tabbacin da yake tattare da rayuwa ba, an bukaci mutanen da su yi kiyasin hasashen da kowacce daga cikin tambayar za ta iya tabbata.

Shekaru uku da fara shirin, ayarin na Tetlock a yanzu ya fitar da wasu daga cikin sakamakonsa na farko ga mujallar kimiyyar tunanin dan-adam (psychological Science) da kuma wurin taron masana tunanin dan-adam din a San Francisco a watan Mayu na 2014.

Daya daga cikin abubuwan da ake fatan cimmawa shi ne a ga ko wasu daga cikin masu hasashen a ko da yaushe hasashensu yana tabbata.

Bayan shekara daya da shirin sai Tetlock ya tattara sakamakon mutane sama da 2,000 ya kuma tace fitattu kashi biyu cikin dari.

A karshen shekara ta biyu kokarinsu ya wuce na sauran masu hasashen da linki hudu (wato hasashensu ya fi na sauran tabbata da linki hudu).

Kwararrun da ba a sani ba

Ko da yake kwarewa ta siyasa na iya taimaka wa mutum ya iya yin hasashen da zai tabbata, to amma mutanen da aka sa a wannan shiri sun fito ne daga bangarori daban-daban na rayuwar jama'a.

Tetlock ya ce, ''daya daga cikin wadanda suka fi iya hasashen ma masanin harhada magunguna ne.''

Kamar yadda za ka yi tsammani wadannan kwararrun masu hasashe sun fi samun maki mai yawa (hasashensu ya tabbata) a abin da ya shafi labaran sirri fiye da sauran takwarorinsu.

Amma kuma dukkanninsu suna da wani abu daya, wanda shi ne sauraron ra'ayin jama'a ( rashin kafewa kan ra'ayi).

A rayuwar yau da kullum ta jama'a ana kuskuren daukar irin wannan hali a matsayin sassaucin ra'ayin siyasa, amma a kimiyyar tunanin dan-adam ana kallon hakan a matsayin yadda za ka iya fuskantar wani kalubale.

Ba shakka mutanen da suke sauraren ra'ayi da fahimtar sauran mutane suna iya fahimtar wata matsala daga dukkanin bangarori, wanda hakan ke taimaka wa masu hasashe su ajiye fahimtarsu bisa wata sabuwar hujja.

Tetlock ya ce, ''kana bukatar sauya ra'ayinka da wuri kuma a kai a kai.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har zuwa yaushe Shugaba Mugabe zai ci gaba da zama a kan mulki? Kwararrun masu hasashe sukan fadi abin da yake tabbata daidai

Wata hanya ta yin hasashe mai tabbata da Tetlock ya bayyana ita ce ta sanin kanka ma'ana sanin rauninka.

Wannan abu ne da hatta kwararrun masu hasashe suke faduwa a kai, kuma saboda haka ne ayarin Tetlock ya yanke shawarar yin wani gwaji na sa'a daya na wani aiki mai sauki da zai taimaka wa masu hasashe su kauce wa yin kura-kurai.

Ko da yake bai bayar da cikakkun bayanai masu yawa ba saboda ka da masu hasashensa su san da su har bayanan su yi tasiri a hasashensu a gaba.

Amma dai ya nuna cewa a lokaci da yawa masu hasashe suna fara wa ne da la'akari da ra'ayin ciki na wata matsala.

Idan ana maganar hasashe a kan ko Shugaba Mugabe zai cigaba da kasancewa a mulki, misali, za su iya farawa da duba halin rashin kwanciyar hankali a kasar.

Amma duk da haka bincike ya nuna cewa za ka iya yin hasashe da zai iya tabbata idan ka kalli bayanan tarihi na baya.

A nan ina kana duba maganar lokacin da Mugabe zai iya cigaba da kasamcewa a mulki, za ka iya la'akari da tsawon lokacin da ya yi a kan mulki, kafin ka yi kiyasinka.

Sauran dabaru kuwa su ne na kokarin rage ra'ayoyi da aka sani na tunanin mutum.

Misali, bincike ya nuna cewa mutane sukan dauki hukuncin da ya fi dacewa da kyau idan aka tuna musu kura-kuren da mutane suka fi yi, kamar kambama hadarin wani abu na tayar da hankali kamar harin 'yan ta'adda.

Haka kuma za su iya tuna mafi muni da kuma mafi kyau na wani abu da ya faru, tun da wannan ne zai sa zuciya ta yi kalle su ta yi la'akari da su ta yadda mutum zai yi lakari da su ya yi hasashe.

Wannan dabara ce da ke a bayyane, amma kuma dukkanin shedu a kan tunanin dan-adam sun nuna ana saurin mantawa da su, hatta a tsakanin mutanen da ya kamata su fi kowa sani.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Watakila kana da wata baiwa ta boye ta hangen abin da zai faru a gaba

Tetlock ya kuma duba yadda shi kansa zai yi amfani da basirar masu hasashen.

Masana tunanin dan-adam da dama sun yi amanna cewa kwararrun da suke aiki a matsayin ayari sun fi yin kuskure a kan wadanda suke aiki daban-daban, domin idan aka yi nisa a aiki sukan zama 'yan amshin shata ga ra'ayin waninsu.

Tetlock ya ce, ''Sai abin ya zama haukan taron jama'a.'' Amma idan aka ba su dan horo a kan yadda za su kalubalanci ra'ayin junansu da kuma mutunta ra'ayin wani, sai ka ga sun samu sakamako mafi kyau idan aka ba su damar yin aiki tare.

A karshe dai ayarin na Tetlock na fatan wadannan dabaru da ya gano za su sa gwamnatoci su sauya yadda suke hukunce-hukuncensu da shawarwarinsu.

''Wannan ba magana ba ce ta fadar abin da zai faru a gaba, abu ne na fayyace yadda lamari yake,'' in ji Tetlock

''Muna son kara fito da gaskiyar da ke tattare da basirar yin hasashe ne.''

Wannan shiri zai iya taimakawa wajen bayyana hanyoyin da mu dukkanmu za mu iya bunkasa iliminmu ko kwarewarmu ta yin hasashe na yau da kullum.

Kana bukatar daukar wani muhimmin mataki ko shawara a kan rayuwarka? Ka amince da rashin tabbas kuma ka gane rauninka ko san ranka.

Ba shakka idan daman kana daga cikin gwanayen masu hasashe, watakila ka hangi wannan shawara.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The best way to predict the future