Me ya sa mata suka fi maza dadewa a duniya?

Hakkin mallakar hoto Getty

A duk fadin duniya mata sun fi dadewa a raye fiye da maza. David Robson ya binciki dalilan da ke sa hakan, da kuma duba ko akwai abin da maza za su iya yi a kan lamarin.

Haihuwata ke da wuya ta tabbata cewa zan mutu kafin rabin jariran da ke dakin haihuwata na asibiti, wanda wannan masifa ce da ba zan iya yin komai domin in kauce mata ba. Dalili? Jinsina.

Kawai saboda ni namiji ne, zan sa ran in mutu kusan shekaru uku kafin macen da aka haife mu rana daya.

Menene tattare da namiji da zai sa in mutu kafin matan da suke kusan shekaruna? Kuma ko akwai damar da zan iya kawar da wannan jafa'i na kan jinsina?

Ko da yake an san da wannan bambanci tsawon shekara da shekaru, amma sai a kwanan nan ne aka dan fara gano dalilan da ke haddasa haka.

Wani abu da aka dade da tunanin sanadin wannan bambanci shi ne cewa maza suna wahala da aikace-aikace wanda hakan ke rage musu tsawon rayuwa.

Aiki ne a wurin hakar ma'adanai ko a gona, maza na takura jikinsu kuma su ji raunuka da suke bujuro musu can gaba a rayuwa.

Amma duk da haka idan wadannan ne dalilan ai da sai a samu raguwar bambancin shekarun a yanzu, domin kusan mata su ma yanzu suna yin irin ayyukan da maza suke yi na wahala.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mata sun fi tsawon rayuwa kuma gibin ba raguwa yake ba

A zahirin gaskiya wanna babban bambanci na tsawon rayuwa ya ci gaba da zama yadda yadda yake duk da irin sauye-sauyen da ke samu a cikin al'umma.

Ka duba Sweden wadda take da ingantattun alkaluma na tarihi.

A shekarar 1800 ana sa ran mata su kai shekara 33 akalla kafin su mutu su kuwa maza shekara 31 ake deba musu.

A yau kuwa mata ana sa ran su kai shekara 83 da rabi su kuwa maza shekara 79 da rabi ake sa ran za su kai a raye.

A dukkanin lokutan biyu mata sun wuce maza a tsawon rayuwa da kashi biyar cikin dari.

Kamar yadda aka bayyana a wata kasida: '' Wannan bambancin tsawon rayuwa da mata suke da shi a kan maza, a farkon rayuwa da tsufa da kuma rayuwa gaba daya, abu ne da ake gani a kowace kasa a kowace shekara inda ake da yawan alkaluman haihuwa da mutuwa na gari. Babu wani bambanci kuma a halittar jikin mutum da ta wuce ta yanzu.''

Kuma ba a taba samun saukin tabbatar da cewa maza na wahalar da jikinsu fiye da mata ba kamar a wannan lokacin.

Abubuwa da suka hada da shan taba da giya da wahalar da jiki ka iya zama dalilan bambancin wannan gibi daga kasa zuwa kasa.

Misali maza a Rasha za su iya mutuwa shekara 13 kafin matan kasar, saboda ta wani fannin misali mazan na yawan shan giya da taba kullum.

To amma kuma haka su ma birai za ka ga maza suna mutuwa kafin mata, duk kuwa da cewa ba za ka ga biri namiji da taba a bakinsa ba ko kuma ka ganshi da kwalbar giya a hannunsa ba.

A maimakon duk wani hasashe kawai abu mafi sauki shi ne mu dubi asalin yadda juyewar halittarmu ta faro.

Ba shakka yanayin rayuwarmu yana da tasiri a lamarin amma ga alama akwai babban abin da ke haddasa wannan bambanci a tsarin halittarmu,'' in ji Tom Kirkwood na Jami'ar Newcastle da ke Burtaniya, wanda ya yi nazarin dalila da yadda tsufa ya ke.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Idan matsalar irin rayuwar da mutane ke yi ce, ba za a danganta lamarin kacokan a kan hakan ba

Akwai abubuwa da dama na cikin halittar mutum da za a iya dangantawa da wannan lamari; farko dai akwai dunkulen kwayoyin halitta da ake kira DNA.

Wannan dunkule da yake bibbiyu a jikin duk namiji da mace ya bambanta, inda na mata duka biyun suke iri daya, inda ake siffanta su da harafin XX na maza kuwa XY ne.

Wannan bambanci ka iya shafar yadda tsufan kwayoyin halittar da su wadannan curi ko dunkulan kwayoyin halittar suke ciki yake kasancewa.

Tun da mata suna da curin wadannan tagwayen kwayoyin halitta XX za a iya cewa ke nan suna da kowace kwayar halitta biyu ke nan, idan daya ta samu matsala dayar sai ta zama ta maye gurbinta.

To su kuwa maza kamar yadda muka bayyana a baya curin wadannan kwayoyin halitta biyu ba iri daya ba ne (XY) saboda haka idan wata kwayar halitta ta jikin mutum ta gamu da matsala babu wadda za ta maye gurbinta, wannan ke nan zai jefa jikin namiji cikin babban hadarin kamuwa da cuta.

Akwai kuma dalilin da ake bayarwa na cewa bugun zuciyar mata yana karuwa a lokacin zagaye na biyu na lokacin watansu na al'ada, wanda ake kwatanta wannan karin bugun zuciya da cewa daidai yake da motsa jiki.

Wato ke nan sakamakon wannan tasiri na motsa jiki duk wata, akwai yuwuwar hakan ya jinkirta cutar zuciya da matan za su iya kamuwa da ita can gaba a rayuwarsu.

Idan kuma duk ba wannan ba ne za ta iya kasancewa girman jiki ne kawai yake sa su wannan tsawon rayuwa fiye da maza, saboda dogayen mutane sun fi yawan kwayoyin halitta a jiki, kuma hakan yana tattare da hadarin samuwar wasu cutuka da kwayoyin halittar , kamar cutar daji.

Babban jiki kuma ya fi yawan aiki, wanda kuma a sakamakon hakan yake tattare da hadarin jin raunin jijiyoyi da kuma tsufansu.

Saboda haka tun da yawanci maza sun fi mata tsawo za su gamu da matsalar zaizayewar jiki ke nan a rayuwarsu.

Amma kuma watakila abin ya dogara ne ga kwayoyin halitta na namiji wadanda ke haifar da sauran bambance-bambance na jikin namiji kamar murya mai karfi da gashin kirji da kuma sanko.

A wannan fanni kuwa wani masanin kimiyya na Koriya Han-Nam Park ya yi nazari a kan wasu bayanai na tarihi na fadar sarakunan gargajiyar kasar tun daga karni na 19 inda ya bincika bayanin wasu maza (bayin sarki) da aka dandake su 81 kafin su balaga.

A nazarinsa ya gano cewa mazan da aka fidiye sun rayu har zuwa kusan shekara 70 idan aka kwatantasu da sauran mutanen da suke tare wadanda ba a dandake ba wadanda su kuma rayuwarsu ta kare a kusan shekara 50.

Gaba daya kiyasi ya nuna cewa damar da suke da ita ta iya rayuwa su kai shekara 100 ta linka sau 130 a kan sauran takwarororinsu wadanda ba a cire musu kwalatansu ba a wannan zamanin a Koriya.

Hatta sarakuna wadanda su ne wadanda suka fi kowa samun kulawa da rayuwa ta wadata da jin dadi a fadar, ba su kai kusa ma da wadan nan shekaru ba.

Ko da yake ba dukkanin nazari ba ne a kan mazajen da aka fidiye ya nuna wannan bambanci ba.

Amma dai gaba daya ga alama mutane da dabbobin da ba su da kwalatai ko 'ya'yan marena suna rayuwa mai tsawo fiye da wadanda suke da 'yan golaye.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bambanci tsakanin dunkulen kwayoyin halittar maza da mata zai iya sa kwayoyin halitta tsufa

Ba a dai tabbatar da ainahin dalilin ba amma David Gems na Kwalejin Jami'ar Landan yana ganin ana samun illar karancin rayuwar mazan ne bayan balaga.

Masanin ya bayar da bayanan wasu fursunoni masu larurar tabin hankali a Amurka a farkon karni na 20, inda aka fidiye wasu kadan daga cikinsu a dole, a matsayin wani mataki na yi musu maganin wannan tabin hankali.

Su ma kamar wadancan bayin sarki na Koriya sun rayu fiye da yawancin sauran fursunonin da suke tare, amma idan har an yi musu wannan fidiya kafin su kai shekara 15.

Kwayoyin halitta na mazancin namiji (testosterone) ka iya sa jikinmu karfi a farko-farkon shekarunmu na ganiya, amma can a gaba sai su sa mu gamu da cutuka irin su cutar zuciya da cutar daji can idan mun girma sosai da kuma sauran cutuka.

Misali su wadannan kwayoyin mazancin suna iya kara yawan maniyyin namiji amma kuma suna haddasa cutar daji ta kwalatai.

Ko kuma za su iya inganta aikin zuciya a farkon rayuwar mutum amma kuma can a gaba su haddasa ciwon hawan jini da cutar daskarewar maiko a cikin jijiyoyin jini (atherosclerosis), kamar yadda Gem ya bayyana.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Watakila kwayoyin halittar mazanci ne sanadin bambancin shekarun

Ba ma kaucewa hadarin da ke tattare da cutukan da kwayoyin halitta na mazancin namiji mata suke amfana da shi ba, za ta iya kasancewa suna kuma amfana da yanayin rayuwar jikinsu ta yarinta ko matasa wanda ke taimakawa wajen kawar da matsalolin da ke tattare da girma.

Kwayoyin halittar matanci ko jima'i na mace (oestrogen) suna kawar da guba da ke sanya wa kwayoyin halittar jikin mutum gajiya ko tsufa.

A gwajin da aka yi a jikin dabbobi an gano cewa matan dabbobi da ba su da wannan kwayar halitta ta jima'i ba sa tsawon rayuwa kamar wadanda ba a cire musu wadannan kwayoyi ba (wannan shi ne kusan kishiya ko sabanin abin da yake faruwa da namijin da aka fidiye wanda shi kuma yake samun lafiya).

''Idan ka cire wa macen bera mahaifa, kwayoyin halittarta ba sa warkewa idan suka samu wani rauni,'' in ji Kirkwood.

Kirkwood da Gem suna ganin wannan wata dama ce ta yadda maza da mata za su iya yada kwayoyin halittarsu ga 'ya'yansu.

A yayin jima'i mata za su fi neman samun namiji mai kuzari ta hanyar kwayoyin halittar mazanci na maza.

To amma da zarar na haifi 'ya'yan sai mazan su zama masu rauni in ji Kirkwood. ''Jin dadin 'ya'yan ta ta'allaka ga jin dadin mahaifiyar.

A takaice abin da yake da muhimmanci a wurin yara shi ne lafiyar mahaifiyarsu amma ba ta mahaifinsu ba''

Wannan dan abin takaici ne ga maza a yau. Amma kamar yadda lamarin yake masana kimiyya sun yarda cewa sai dai a ci gaba da laliben cikakkiyar amsar wannan bambanci na tsakanin tsawon rayuwar mata da maza.

'' Wajibi ne ya kasance a shirye muke mu yarda da bayanin bambancin kwayoyin halitta da sauran abubuwan a kan wannan tazara ta rayuwar mace da namiji,'' in ji Kirkwood.

Amma dai fatan shi ne, a karshe ilimin da za a samu zai iya bayar da hasken da zai taimaka mana mu rayu fiye da shekarun da muke rayuwa a yanzu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why do women live longer than men?