Illar abokan da ka tsana ga lafiyarka

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Kusan rabin abokanmu na iya kasancewa abokai ne da ba ma jin dadin sha'ani da su, wadanda kuma za su iya yin illa ga lafiyarka da kuma tunaninka.

Kamar yadda David Robson ya bayyana mana.

Ina da wata matsala. Matsalar ita ce ina da abokai da na tsane su. Wadannan (frenemies a Ingilishi) abokanai suna iya shafar lafiya.

Ka da ka yi min mummunar fahimta: Ba wai ba na son wadannan mutane ba ne, a'a, Ina kaunarsu. Abin kawai shi ne suna bata min rai ne.

A duk lokacin da muke hira ko wata magana da su ba wani abu da za ka ji suna kawowa sai zancen kawai ko kafewa a kan ra'ayinsu duk da cewa ba a kan gaskiya suke ba ko kuma su rika maka wasan banza ko wata takurawa.

Na gano cewa irin wannan abokantar ta fara daukar hankalin masana tunanin dan-adam.

Har ma wani lakabi na musamman suka yi mata a harshen Ingilishi (ambivalent relationship) abokantaka mai dadi da bacin rai.

Julianne Holt-Lunstad ta Jami'ar Brigham Young da ke Utah a Amurka, ta ce yawanci kusan rabin mutanen da muke mu'amulla da su, sun kunshi wadanda muke kauna da wadanda muka tsana.

''Abu ne mai wuya a ce ka hadu da mutumin da zai ce ba shi da ko da akalla daya na irin wadan nan abokai. Ta bayyana.

Wannan abin damuwa ne sosai fiye da yadda aka dauka da farko. Nazarin da Holt-Lunstad ta yi na nuna cewa irin wadan nan abokai suna da hadari fiye da mutanen da ka tsana ma.

Wadan nan abokai mutane ne da za su iya cutar da kai su haifar da illa ga lafiyarka.

To idan har haka lamarin abokantakarmu da su yake me zai sa lalle sai mun ci gaba da wannan abokanta maras amfani?

Taimakon juna

Idan muna son mu fahimci wannan akwai bukatar mu duba tasirin abokan da muke da su.

Domin yawanci dai muna daukar cewa amfanin tarin 'yan uwa da abokai shi ne samun kariya.

A nazarin da ta yi na littattafai ko kasidu 150, Holt-Lunstad kwakkwarar abokantaka tana rage maka hadarin mutuwa kamar yadda idan ka daina shan taba kake rage wa kanka hadarin mutuwa da wuri.

Kuma kasancewa kai kadai ba ka da abokanai kusan daidai yake da hadari ko illar da teba take yi ga lafiya.

Ta yaya? Amfanin abokai shi ne su taimaka mana mu samu kwanciyar hankali da kuma kare mu daga damuwa da gajiya.

Damuwa na haddasa matsalar hawan jini wadda ita kuma ta kan haifar da wasu tarin cutuka, yayin da su kuma abokai suke taimaka wa wajen kwantarwa da mutum hankali da debe masa kewa.

Bacin ran da kadaici ke iya haddasawa shi kansa zai iya karfafa wasu matsaloli ko cutuka kamar rashin barci.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A wannan zamani na fasahar sadarwa da wuya ka iya raba kanka da abokanai masu damu

Akwai abokantaka iri daban-daban. Kamar yadda Robin Dunbar na Jami'ar Oxford ya nuna, abokanai masu wuyar sha'ani wadanda ke da saurin sauya ra'ayi wani bangare ne na mu'amullarmu ta yau da kullum.

''A ko da yaushe kana gogayya ne kan abubuwa da dama. Matsalar ita ce yadda za ka iya shawo kan wadannan matsaloli ta yadda hankalin ku abokanan zai zama yana da alkibla daya,'' ya ce.

''Saboda haka sai ka zama cikin shiri na yabawa da koda abokan tafiyarka, wadanda suka hada da abokan da ba ka jin dadin zama da su.

Kana hakuri da su ne domin kana son ka ga sun gyaru.''

Bukatar jan tafiya tare da abokananmu su kuma abokan da ba ma jin dadinsu mu kara jansu a jika sosai ta tabbata ke nan.

Sai dai abin takaici bincike da nazarin da aka yi a can a kan tasirin abokananmu a kan lafiyarmu bai bai duba wadan nan matsalolin ba.

Saboda haka Holt-Lunstad da Bert Uchino a Jami'ar Utah sun duba wanda ya fi tasiri ko karfi tsakanin amfani da illar wannan abokanta da ke takura ma.

Abin da suka gano ya ba su mamaki matuka.

Matsin lamba

A daya daga cikin nazarin da suka yi, sun yi gwajin abokanta tsakanin mutane ta matsakaici da kuma dogon lokaci, ta hanyar takardu masu dauke da tambayoyi, inda suka sanya wa mutanen na'urar tantance hawan jininsu, kafin kuma daga bisani suka bar mutanen suka koma rayuwarsu ta ainahi cikin jama'a na wasu 'yan kwanaki.

''A duk lokacin da suke mu'amulla da wani (su mutanen da ake gwajin da su), na'urar auna hawan jini tana auna yanayin bugun zuciyarsa,'' in ji Holt-Lunstad.

Kamar yadda za ka yi tsammani a duk lokacin da mutum yake tare da abokansa na kwarai da ke taimaka masa zuciyarsa ba ta bugawa sosai fiye da yadda take a ka'ida , wato gabansa ba ya faduwa ko hankalinsa ba ya tashi ba kamar idan mutum ya hadu da abokin aiki ko shugaban da ke takura masa ba.

Amma abin mamakin shi ne gabansu yana faduwa sosai wato hawan jininsu yana karuwa idan suka hadu da abokan da ba sa jin dadinsu.

Karin gwajin da aka yi kan wannan sakamako ya kara tabbatar da hakan da kuma kara bayyana karin wani abin ma.

Domin an ga cewa ''ko da wannan abokin da ba sa jin dadinsa yana wani daki ne a kusa da inda kake duk da haka hawan jininka yana karuwa, ma'ana hankalinka yana tashi da kuma damuwa,'' inji Holt Lunstad.

''Kawai tunanin za ka iya haduwa ko magana da shi ne.''

Karin abin mamakin ma shi ne hatta rubutun sunayen irin wadan nan abokanai idan aka nuna maka bugun zuciyarka na karuwa.

Bert Uchino ya ce , ''wannan na nuna cewa duk wani abu da zai iya tuna mana su yana jefa jikinmu cikin irin wannan hali na karin aiki wato bugun zuciya ko kuma fargaba.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hawan jininka yana karuwa a lokacin da kake magana da abokin da ke damunka

Ta wannan hanya za mu ga cewa irin wadan nan abokanai suna daga cikin mutanen da muke mu'amulla da su wadanda suke takura mana.

Ta wani fannin saboda rashin tabbas dinsu. ''Akwai wannan rashin tabbas,'' inji Holt-Lunstad.

''Za su zo min ne da magana mai dadi ne ko kuma wata maganar za su sake zuwa da ita ta takura min?'' Masaniyar ta kara da cewa.

Uchino yana ganin dangantaka ko kusancinmu da su ka iya sa su cutar da mu fiye da wadanda ma muka dauka makiyanmu ne.

Ya ce , ''sun zama tamkar wani bangare namu. '' Saboda haka abin da duk suka yi ko suka ce zai iya shafarmu sosai.

Kuma saboda muna da alaka mai karfi da su(abokantaka) wannan ya ba su dama mai karfi su cutar.''

Yana ganin abu ne mai sauki ka yi watsi da duk wani abu na makiyin da ka sani, tun da ba su da wani muhimmanci a wurinmu.

Uchino ya ce, ''wannan ba abu ne da za ka iya yi ba kai tsaye domin za ka yi ta tunanin abin da suka yi maka da ya bata maka rai a tsawon lokaci.''

Yanke abota

Ya zuwa nan nazarin da Uchino da Holt-Lunstad suka yi ya duba tasirin gajeren lokaci na illar abokai masu takura ma.

Abin da za su yi a yanzu kuma shi ne binciken illar da yadda idan wannan tasiri ya taru bayan shekara da shekaru zai yi.

A bayanan da Uchino yake da su illar za ta iya kaiwa har ga kwayoyin halittar mutum (DNA).

Yayin da muke girma shekaru na kama mu wadan nan kwayoyin halitta namu su ma suna tsufa, suna rauni da za su iya kamuwa da cutuka kamar na daji.

Wannan rauni da kwayoyin halittarmu ke gamuwa da su sakamakon shekaru, haka ma damuwa ke kara sa musu wannan rauni, wato ke nan damuwar da muke samu daga wadan nan abokai ta shafi kwayoyin halittar.

Idan sauran nazari da bincike sun tabbatar da irin wannan sakamako, to sai mu ce akwai bukatar mu sake nazarin dangantakarmu ko abokantarmu da irin wadan nan abokai, ko muhimmancinta ya kai mu ci gaba ko mu yanke ta.

Sai dai abin takaicin shi ne ba abu ne mai sauki ka iya yanke hulda da irin wadan nan abokai ba, musamman idan aka yi la'akari da cewa kila abokanai ne da kuka taso tare.

Lokacin da Holt-Lunstad da Uchino suka tambayi mutane me yasa ba za su yanke abokantarsu da wadan nan mutane ba, da yawansu sai su kawo maganar biyayya ko hakuri.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawanci mukan kawar da kai daga laifin abokin da ke takura mana. Anya hakan ba yana kara mana damuwa ba?

To tun da wadan nan masana sun san duka wadan nan abubuwa, wace swara za su bayar da yadda za a yi mu'amulla da abokanan da suke takura wa?

Dabarar da Uchino ya yi amfani da ita shi kansa, ita ce ya yi magana da wannan aboki da baya jin dadinsa ya gaya masa abubuwan da ba ya so da yake yi domin fahimtar juna.

''Idan ka duba yadda mutane suke yi da irin wadan nan abokai nasu, za ka ga babu irin wannan mataki na fuskantarsu keke da keke, yawancin lokaci mukan yi musu karya, wato ba ma gaya musu gaskiyar abin da ba ma so da su, ko mu kauce musu idan za mu iya.''

Masanin yana kuma duba yuwuwar amfani da natsuwa da zuzzurfan tunani wanda wata hanya ce ta jurewa damuwa, har ma abokai marassa dadin hulda.

Hakan ba kuma zai sa ka samu kwanciyar hankali kadai ba ne zai ma taimakawa tunaninka da lafiyarka.

To amma Uchino yana ganin ba a yi wani babban gwaji mai kyau ba a kan wannan, saboda haka yake son yin cikakken bincike a kai.

Idan akan maganar abokantaka ta ce daya daga cikin kalaman Uchino ne a zuciyata.

''Hankalin dukkanninmu yana kan wasu abubuwa ba ma lura mu gane cewa mutane suna bukatar tallafi, wanda hakan ka iya kaiwa ga jin abu mai kyau ko kuma maras kyau daga alakarmu ko abokantarmu da wasu,'' ya ce.

Ba wani abu ba ne da zan yi alfahari cewa na amsa laifi a kansa kamar yadda ake tuhumata. Domin irin yadda na dauki kaina zan iya zama abokin kaina da ke takurawa kaina.

Wato daya daga cikin abokaina da bana jin dadin mu'amulla da su shi ne ni kaina.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Anti-social network: Health risks of love-hate friends