Kasada da mota mai amfani da lantarki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daliban suna gasa ne da sauran dalibai daga sassan duniya

Wani ayarin matasa 'yan makaranta ya tari aradu da ka ta nuna juriya da yanayin zafi da kuma sauran hadura wajen shiga gasar tseren motoci masu amfani da wutar lantarki a Australiya.

Jack Stewart ya yi mana nazari.

Gasa ce mai hadarin gaske wadda matuka motocin ke fuskantar hadarin motarsu ta kama da wuta suna ciki, da haduwa da manyan motoci da shanu da babba-da-jaka da sauran namun daji.

Bugu da kari ga kuma tsananin zafin rana da ya kai lamba 45 a ma'aunin celcius ko ma sama da haka.

Bayan duka wannan, motar da kake tseren da ita mai amfani da wutar lantarki ce da ake samu daga hasken rana, inda take dauke da gima-giman faya-fayai na sarrafa hasken ranar a kanta.

Motar ba ta aiki da mai sannan ana fatan ba za a yi mata caji ba ko a yi mata janwe.

Gasar tseren motocin masu amfani da hasken rana ta duniya wadda ake kira 'Bridgestone World Solar Challenge an yi ta ne a Australia, inda motocin suka tashi daga arewacin kasar zuwa kudanci.

An fara ta ne daga ranar 18 ga watan Oktoba zuwa 25 ga watan, kuma a wurin Matt Price da abokansa wadanda dukkanninsu matasa ne, shiga gasar wani babban cigaba ne.

Wannan dai ba karamin kalubale ba ne hatta a wurin direbobin da suka saba shiga gasar tsere, ba ma ga shi Price mai shekara 17 ba.

Shi da abokan nasa daga kwalejin Ardingly ta Biritaniya, sun shiga gasar ne a daidai lokacin da suke haddar karatunsu domin jarrabawa.

Daliban biyar wadanda shekarunsu suka kama daga 17 zuwa 18 sun je Australiyan ne domin fafatawa da wasu kungiyoyin biyar, yawancinsu daga jami'oi fitattu masu tsada daga fadin duniya.

''Abin na da 'yar wahala kuma idan ka duba sauran motocin gasar, za ka ga tsere ne na ban mamaki,'' in ji James Price, mai magana da yawun matasan kuma daya daga cikin direbobinsu, kafin su fara gasar.

''Wannan wata sabuwar kasada ce ga kowa, raba kasar biyu, ka keta ta daga wannan bango zuwa wancan bangon, dama ce da mutum zai iya samu sau daya a rayuwa.''

Gasa ce mai wuya. Sun rika tukin ne daga karfe takwas na safe zuwa biyar na yamma kullum, kuma a lokacin da rana take tsananin zafi inda motocin ke samun hasken ranar da suke amfani da shi.

'yan tseren sun yi fama da bambancin yanayi kama daga tsananin zafin hamada zuwa yanayi mai danshi na arewaci da kuma yanayi mai sanyi a can yankin kudanci.

Wadanda suka yi gasar a baya sun yi fama da kutsen dabbobi irin su shanu da babba-da-jaka a kan tituna, ga kuma hadarin gamuwa da macizai idan za a kwanta da daddare.

Gasar tseren motocin masu amfani da hasken rana ta duniya, wata hanya ce mai tsanani ta kokarin gano mota mai aiki da lantarki mafi inganci a duniya.

Sau daya duk bayan shekara biyu masu gasar suke gayyatar wasu daga cikin matasan da suka fi hazaka a duniya domin duba batutuwan da suka shafi hanyar sufuri mafi inganci.

An raba kungiyoyin gasar kashi uku ne, inda motocin da za su fafata tseren za a ga iya lokacin da za su iya keta nahiyar.

An kera motocin ne kanana masu ban sha'awa kuma dab da kasa.

Kungiyar matasan daliban da suka je gasar daga kwalejin Ardingly ta fafata ne a bangaren gasar motocin yawon shakatawa da bude idanu.

Wannan na nufin motar ta kasance mai karfin shiga kwazazzabo kuma mai wurin mutum biyu.

Jumulla akwai ka'idoji 366 wadanda wajibi ne motar ta cika shu, wanda wannan kalubale ne da ya kai ita kanta gasar.

Jagoran daliban na Biritaniya, Price ya ce kundi ne da ya ke da shafi 43.

Su kuwa motocin gasar a bangaren 'yan kasada, motoci da ba a gindaya musu wasu tsauraran ka'idoji ba.

Sannan kuma an hada da motocin da suka shiga gasar a bara, inda aka ba su damar sake shiga gasar, amma kuma da wasu sabbin 'yan tsere.

Motar daliban na Ardingly, an zayyana ta ne ta hanyar amfani da wata manhaja ta zamani wadda kamfanin New Technology Cadcam, wanda ya ba wa matasan horo wajen kera motar ya samar ta yadda za ta dace da gasa.

Hakkin mallakar hoto Ardingly Solar

Price ya ce , ''wannan tallafi shi ya karfafa mana gwiwa sosai.''

Kafin wannan lokacin neman kamfanonin da za su dauki nauyinku babban kalubale ne, domin babu wani abu na a-zo-a-gani da za ku nuna.

A game da aikin motar kuwa,'' karshen gudunta shi ne kilomita 82 a cikin sa'a daya,'' in ji Price.

Duk da cewa ba za ta iya cin wani tsere ba, amma dai ba za a bar ta a baya ba.

An hada wa motar 'yan baturan hasken rana har 264. Duk da cewa faya-fayan karbar hasken ranar masu inganci ne, duk da haka suna bukatar a dora su a wuri mai fadi sosai ta yadda za su samar da isasshiyar wutar lantarkin da motar ke bukata.

Saman motar da gabanta da kuma bayanta dukkaninsu an tsara su ne yadda suka zama madaukan faya-fayan tarar hasken ranar.

Wannan shi ya sa motar ta zama kamar wata akwati, amma kuma abin da ake bukata shi ne inganci ba kyau ba.

Wannan na nufin gudun motar zai takaita ne a kilomita 50 cikin sa'a daya, inda za ta dan rage kadan domin wuce manyan motoci a titunan Australiyan.

Matasan daliban sun rika sanar da magoya bayansu bayanai a kai a kai ta shafin Facebook da Twitter kan cigaban da suka rika samu da dalin da suke cike.

A wani lokaci sai da matasan suka gamu da wasu 'yan matsaloli ta farko inda 'yan sanda suka tsayar da su, sannan kiris su yi karo a wani wuri, kuma a wani lokaci suka bi wata hanya ta daban.

Sai dai a karshe daliban jami'ar Delft ta kasar Holland ne suka yi nasarar zuwa na daya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zakarun gasar

Kungiyar daliban ta Nuon Solar Team, ita ce ta farko da ta kai layin da aka shata na karshen gasar ta nisan kilomita 3,000 da aka kammala cikin kwanaki hudu.

Kungiyar daliban jami'ar Twente, ita ma daga Holland ita ta zo ta biyu, yayin da daliban jami'ar Tokai daga Japan suka zo na uku.

Idan akan son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The teens taking on a gruelling solar car challenge