Shekara nawa za ka rayu?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Daga cikin alkaluman da ake fitarwa a kan lokacin da za mu iya mutuwa, akwai bayanan da suka shafi sauyin yanayin rayuwa da abubuwan da ke wakana a duniya da kuma yanayin tsufa na zamani.

David Spiegelhalter ya yi nazari

A kasidar da na rubutu ta karshe na duba yadda mutuwa take a wurin aiki ne, amma yanzu ina son in duba tsawon lokacin da za mu iya rayuwa.

Idan muka yi maganar tsawon rayuwa, yawanci ana bayyana ta ne da tsawon lokacin da ake sa ran mutum zai rayu.

Wato kiyasin tsawon rayuwar mafi yawan mutane, sai dai kalmar 'mafi yawanci' za ta iya batar da mutum. Domin kamar yadda take nunawa mafi yawancin mutane a Birtaniya suna da 'ya'yan marena daya ne.

Misali Zabura ta 90 ta ayyana a littafin Injila na King James, cewa, ''kwanakin shekarunmu uku ne sau 20 da goma'' (70), ko da yake har yanzu sai ka ci sa'a sosai ka kai wannan shekaru da aka bayyana a Baibul.

Wasu sanannun mutane kamar Augustus Caesar ya cimma wannan iyaka har ya dan zarta ta, inda ya kai shekara 75, yayin da Michelangelo ya yi fintinkau har zuwa shekara 88.

Tun zamanin Girkawa na da, akwai camfin da ake yi a kan hadarin da ke tattare da lambobin da suke da alaka da bakwai ko linki na lamba bakwai.

Ana daukar lambar 49 (7x7) da 63 (7x9) a matsayin shekaru masu hadari.

Ta wani bangaren domin kawar da wannan camfi, a 1689 wani malamin Kirista in Breslau a Silesia(wadda yanzu take a Wroclaw a Poland) ya tattara shekarun da mutane ke mutuwa.

A karshe dai Edmond Halley a Ingila ya samu wadannan alkaluma, inda ya ajiye aikin da yake yi na bincike kan taurari.

Ya yi jadawali mai inganci na farko a shekarar 1693, inda ya yi kiyasin hadarin mutuwa a shekara-shekara, ya fitar da hanyar da mutum zai iya rayuwa ya kai duk shekarar da yake so.

Ba wata sheda da ke tabbatar da karin hadarin mutuwa a shekara ta 49 ko 63, saboda haka Halley ya rushe wannan magana ta malamin Kirista Silesia.

Ba kamar maganar Baibul ba ta kiyasin shekarun mutum a duniya zuwa 70 ba, kiyasin da jadawalin Halley ya fitar na tsawon rayuwar mutum shi ne zuwa 84.

Ya yi kiyasin cewa akwai damar kashi biyu cikin dari ta kaiwa wannan shekara, kuma domin ya tabbatar da haka, ya mutu yana da shekara 85.

Wannan ya sa har ya zarta Bill Haley shi ma wanda ya yi suna game da binciken taurarin, wanda ya rayu zuwa shekara 55 kawai.

To amma a game da batun rayuwa, yawan mutuwa a lokacin yarinta yana da tasiri sosai a kan tsawon rayuwar da ake sa ran mutane za su yi.

Shekarun yawancin mutane na rayuwa za su kasance kadan, amma wadanda suka rayu za su iya kaiwa wasu shekaru masu yawa.

To watakila nazarin wannan lamari daga fannin duniyar kade-kade da wake-wake zai iya sa a samu hanya mafi inganci ta nazarin rayuwa da mutuwa.

Paul MacCartney yana dan shekara 16 ne lokacin da ya rubuta ''When I'm 64'', wanda wannan shekara ce da ake ganin shekara 64 shekara ce ta tsufa.

To amma idan muka duba yadda yaro zai iya rayuwa ya kai shekara 16, da kuma damar ci gaba da rayuwa ya kai shekara 64, za mu iya fahimtar abin da ya sauya tsawon shekaru gommai.

Misali idan muka duba bayanai na cibiyoyi masu inganci kamar cibiyar tattara bayanan mace-mace ta Birtaniya (Human Mortality Database), mun gano cewa a shekarar 1841, kashi 31 cikin dari na yaran da aka haifa a Ingila da Wales sun mutu kafin su kai shekara 16.

Amma idan har ka rayu akwai dama kusan kashi 50 cikin dari ta kaiwa shekara 64.

Lokacin da mawakan nan 'the Beatles' suka yi wakar 'when I'm 64 a 1966, kashi biyu da rabi cikin dari na yara sun mutu kafin su kai shekara 16 kuma yara mata da suka rayu suna da damar rayuwa kashi 84 cikin dari su kai shekara 64, amma damar da takwarorinsu maza suke da ita su kuwa kashi 74 ne cikin dari.

Bambancin yana nuna mummunan tsarin rayuwa na maza da yawa.

Zuwa shekara ta 2009, shekara ta karshe da muka yi kididdiga, kasa da kashi 16 ne cikin dari na yara suke mutuwa kafin su kai shekara 16, kuma damar kaiwa shekara 64 ta karu zuwa kashi 92 cikin dari a bangaren mata, su kuwa maza damar ta karu ne zuwa kashi 87 cikin dari.

Wannan ya sa kenan mata suke da damar rayuwa zuwa shekara 82 maza kuwa zuwa shekara 78.

Abubuwan da ke faruwa a duniya;

Alkaluman tsawon rayuwar da ake sa ran mutane su kai suna da muhimmanci duk da cewa akwai wasu muhimman abubuwan da suke da tasiri a kan alkaluman.

Bayan yake-yake na duniya, tunkarar birnin Moscow da Napoleon ya yi, abin da ya hallaka mutane 400,000 ya rage tsawon shekarun da ake sa ran mutane su kai zuwa shekara 23 na wani dan lokaci.

Annobar masassar da aka yi a 1918 zuwa 1919 ta rage shekara goma ta tsawon rayuwar da ake sa ran mata za su yi a Faransa.

Yayin da cuta mai karya garkuwar jiki a Afrika ta Kudu ta rage tsawon rayuwar da ake kyautata zaton mutane za su yi daga 63 a 1990 zuwa 54 a 2010.

Abin mamaki an samu sauyi a wasu kasashen. Misali a 1970 tsawon rayuwar da ake sa ran mutane su yi a Vietnam shekara 48 ne, amma yanzu 75 ne.

Ya dauki Ingila da Wales tun daga 1894 zuwa 1986, kafin su samu wannan sauyi.

Hatta a cikin kasa daya ma za mu iya ganin irin wannan bambanci.

Misali a shekarar 1901 tsawon rayuwar da ake sa ran mutane za su yi tsakanin bakar fata a Amurka shekara 32 ne, inda kashi 43 cikin dari ke mutuwa kafin su kai shekara 20.

Su kuwa farar fata shekarun da ake sa ran su kai a lokacin su ne 48, kashi 24 cikin dari ke mutuwa kafin su kai shekara 20.

Har yanzu bayan shekara 100 da kuma fafutukar masu kare hakkin dan adam, wannan gibi yana da girma' ko da yake ya ragu daga bambancin shekara 16 zuwa biyar tsakanin bakar fatar da farare.

Yanayin tsufan mutane;

Idan muka duba an fada mana cewa yawan mutanen duniya ya kai biliyan bakwai kuma yana cigaba da karuwa sosai, saboda haka za mu iya yin hasashe mai ma'ana a kan tsawon shekarun da mutane za su iya kaiwa.

Idan aka samu ingancin harkar kula da lafiya, za mu iya yin hasashen cewa mazan da aka haifa a Ingila da Wales yanzu yawanfinsu za su iya rayuwa har shekara 90.

Mata kuwa za su kai shekara 94, inda kashi 32 cikin dari na maza za su iya kaiwa shekara 100, mata kuwa kashi 39 cikin dari su kai shekara 100 a 2012.

Wadannan alkaluma dai abu ne da za a yi mamaki a kansu, to amma daman hasashe wanda za a iya yin cece-kuce a kansa.

Akwai wani tsari a jikin mutum ne na tsufa, kuma za a iya dawo da shi baya (mutum ya dawo kasa da shekarunsa)?

Ko akwai wani wa'adi na shekaru da za mu wuce da karfin tsiya?

Akwai dai abin da yake tabbas ba makawa a kan yaran da za a haifa a nan gaba, za su fuskanci matsalar kula da tsofaffi da dama, domin wadanda suka tasamma tsakiyar wa'adin shekarunsu ba za su mutu ba.

Majalisar dinkin duniya ta yi kiyasin yawan mutanen da suka wuce shekara 60 zai linka biyu tsakanin 2007 da 2050 domin mutane za su yi tsawon rayuwa kuma rashin yawan haihuwa na nufin matasa kadan za a samu.

'Yan sama da shekara 60 za su kai mutane biliyan biyu a duniya nan da 2050 kuma 'yan sama da shekara 80 za su kai kusan miliyan 400.

Bayan shekaru 70 da aka ayyana mutum zai rayu, bayanin ya cigaba a littafin na Zabura na 90 da cewa '' idan kuma har suka kai shekara 80, karfinsu zai ragu tare da damuwa, domin ba da dadewa, zai yanke, sai mu tashi, wannan baya nuna wani yanayi mai kyau na tsufa.

To muna wannan kokarin ne domin mu yi tsawon rai, ta yadda za mu rika zama a kofar daki, talabijin na kara, muna kokarin jin abin da bakin da ba su damu da mu ba ke kumajin gaya mana?

A gaskiya lamarin ba zai kai haka baci ba, domin a 2008 mazan Birtaniya masu shekara 65 suna da ragowar kusan shekara 17 da ta rage a rayuwar da ake sa ran za su yi, wadda goma daga cikin ana ganin za su yi ta ne cikin lafiya ko koshin lafiya.

Su kuwa mata suna da ragowar shekara 20 yawancinsu, kuma 11 daga cikin za su yi ne da koshin lafiya.

Dukkanin wannan jin dadi ne a gare ni. Nan da 'yan shekaru zan kai shekara 64 kuma tuni gashin kaina da dama ya zube.

Kuma ina sa ran cigaba da rayuwa iya iyawata kafin in shiga rukunin tsofaffin masu kididdiga

Idan ana son karanta wannan a harshen Ingilishi a latsa nan Life expectancy: How long will you live?