Ka taba damuwa kan sauyi a muhallinka?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ka taba jin ranka ya baci ko ka damu saboda wani abu da ake yi a muhallinka da ya ke sauya muhallin da sunan cigaba? A harshen Turanci dai babu wata kalma da ke nufin wannan damuwa to amma a yanzu wani masani ya samar da ita.

Georgina Kenyon ta yi mana bayani.

A duk 'yan watanni kamus din Oxford ya kan mamayi duniya idan ya fito da sabbin kalmomi a cikin jerin kalmominsa na intanet.

Sabbin na baya bayan nan sun hada da kalmar 'hangry' (bacin rai saboda yunwa) da kuma 'manspreading' (zama kafa a warware).

Haka kuma su ma masu bincike suna fafutukar kirkiro sabbin kalmomi, wadanda ba a sa su a fitaccen kamus din ba, amma kuma ya kamata a ce an sa su.

Duk da cewa ba za ka sami kalmar a kamus na Turanci na Oxford din ba, masanin falsafa Glenn Albrecht ya taba kirkiro ire-iren wadannan kalmomi a lokacin da yake aiki a jami'ar Newcastle a Australia.

Wannan kalma ita ce 'solastalgia' wadda ya kirkiro daga hadakar kalmomin 'solace' da 'nostalgia'.

Wannan kalma ta bazu sosai domin ba a fagen ilimi kadai ake amfani da ita ba hatta a harkar lafiya a kasar Australiya da kuma tsakanin masu bincike na Amurka da suke duba illar wutar daji a California.

Kalmar tana bayyana damuwar da kake ji ne game da sauyin da ake samu a muhallin kusa da gidanka kamar yadda Albrecht ya yi bayani.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ka taba damuwa cewa muhallinka na samun sauyi wanda ke lalata shi ?

A lokacin da yake jami'ar Newcastle wasu mazauna birnin sun tuntube shi game da damuwar da suke da ita kan aikin hakar kwal da ake yi da kuma gurbata muhallinsu da ake yi a sanadin aikin tashar samar da wutar lantarki.

Ya ce, ''ina cikin aiki mutane za su bugo min waya suna rokon da in taimaka musu a kan wadannan abubuwa da ke damunsu. Fargaba da damuwar da suke da ita kan barazanar da wadannan illoli da ake yi wa muhallinsu da lafiyarsu abu ne da za ka fahimta daga yadda suke maka magana ta waya ma.''

Wannan kira ta waya da kuma ganin irin illar aikin hakar makamashin kwal din a muhallin su suka kai shi ga kirkirar wannan kalma.

''Solastalgia na nufin yanayin damuwar da mutum ke ciki a duk lokacin da yake jin an keta haddin kaunarsa da muhallinsa.''

Rahoton shekarar 2015 na Lafiya da Muhalli na mujallar harkokin lafiya ta 'The Lancet, ya tattauna yadda wannan damuwa take da alaka da rashin kwanciyar hankali saboda muhallin da ke da wata matsala wanda kuma mutanen da ke muhallin ba su da karfin da za su iya yin wani abu a kan lamarin.

Haka kuma Justin Lawson daga jami'ar Melbourne Deakin ya bayyana wannan kalma a fannin da ba na fagen koyar da ilimi ba, inda ya ce, wakar kungiyar nan ta 'No More Walks in the Wood ta The Eagles' za ta iya sa mutane su fahimci kalmar, wadda ke kokawa kan gushewar daji da tunawa da matukar muhimmanci da tarihinsa.

''Tana magana ne kan yadda muke ji da sauyin da ake samu a muhallinmu a tsawon lokaci.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption ''Ba sauran tattaki a cikin bishiyoyi, domin an sassare duka bishiyoyin'' a wakar da 'The Eagles' suka yi

Wadannan saue-sauye na muhalli za su iya kasancewa na haka kawai (fari ko wutar daji) ko kuma wanda mutum ke jawowa, kamar dumammar yanayi da gine-gine.

Kamar Albrecht, Lawson da abokan aikinsa na kokarin binciko wata kalmar wadda za ta kunshi matsalar da kuma damuwar.

Amma yayin da Albrecht ya yi amfani da kalmomin da asali na Latin da Girka ne, Lawson na kokarin lalubo wata kalma ce ta gargajiya, ''domin samo kalmar da za ta yi bayanin dangantakarmu da muhalli ta hanyar da ta fi dacewa.''

'Solastalgia ba abu ba ne na farko kadai a duniya, domin Sri Warsini mai bincike a jami'ar James Cook da ke Cairns a Australiya, tana duba abubuwan da suka danganci ma'anar wannan kalma da suka faru a kasashe masu tasowa kamar Indonesia sakamakon wani bala'i da ya faru.

Wannan bala'i ya hada da ruftawar kasa ko duwatsu da rasa gidaje da dabbobi da filayen noma da kuma hadarin da ke tattare da zama a wuraren da ke tattare da hadari, abin da ke shafar yadda mutum ya ke damuwa da kaunar muhallinsa wanda kuma ke sa mutanen da damuwa.

Duk da ma'anar wannan kalma, mutumin da ya kirkiro ta bai karaya ba.

Ya ce, ''ni mutum ne mai kwarin gwiwa kuma ina yin abubuwa da dama domin dakile duk wani cigaba da zai haifar da dumamar yanayi wanda kuma da hakan zan kara haifar da wannan kishi na nuna damuwar sauyi a muhalli,'' in ji Albrecht.

Idan ana son karantaa wannan a harshen Ingilshi a latsa nan Have you ever felt 'solastalgia'?