Me ya sa nake ji kamar zan fadi idan zan yi barci?

Hakkin mallakar hoto istock

Ko ka taba jin kamar za ka fadi a lokacin da barci ya fara daukarka? Wata mai karanta labaran da BBC ke sanya wa ne da suka shafi ire-iren wadannan abubuwa ta ke son sanin dalilin da hakan ke faruwa a kanta. To ga kimiyyar da ke sa hakan. Kamar yadda William Park ya bincika.

To kafin mu fara bayani bari mu fara mika godiya ga Reena Patel kan wannan tambaya da ta turo wa BBC kan yadda take jin kamar za ta fadi a barcinta.

Kai ma idan kana da wani abu da kake son sani da suke da ban mamaki ko sarkakiya ko daure kai kana aiko wa ta email (cikin harshen Ingilishi) zuwa ga sari.zeidler@bbc.com ko william.park@bbc.com.

To yanzu bari mu koma kan waccan tambaya ta abin da ke sa mutum ya ji kamar zai fadi a yayin da barci ke daukarsa.

Wannan abu ne da kowa yake yi, kuma idan ya hadu da mafarki sai ka ji kamar kana fadowa ko ka fadi kwatsam.

Idan abin ya zama kamar na mafarki misali kamar a ce fadowa cikin iska, wannan shi ne abin da ake kira haduwar mafarki, kuma yana bayyana yadda zuciyarmu ke iya hada abu, kamar yadda Tom Stafford ya rubuta kenan a kan abin a shekara ta 2012.

Wannan abu da ke faruwa da mu yana bayyana irin dauki ba dadi ko gwagwarmayar da ke gudana a cikin kwakwalwarmu ne a lokacin da muke fafutukar shiga barci.

Me yake sa mu rika wannan fizga ko rausayawa?

Idan muna cikin barci jikinmu kamar ya mutu ne ba ya motsi, kuma ba mu san abubuwan da ke faruwa a duniya ba. Amma abin da ke tafiyar da aikin jijiyoyin jikinmu ba ya tsayawa da aiki kamar misali mukunnin fitilar lantarki (switch) idan an kashe kwan fitilar.

Wani bangare na kwakwalwarmu shi ne yake tafiyar da muhimman ayyukan jikinmu, kamar numfashi, kuma shi ke gaya mana idan muna farke (ba barci muke ba).

Wani bangaren na daban a kwakwalwar kuma shi ke sanar da mu idan mun gaji.

To a lokacin da muka kama gangarar barci sai wancan bangaren na farko ya saki iko da jikin namu sai wanda yake fada gaya mana mun gaji shi kuma ya karbi iko da jikin namu.

Wannan aiki yana kasancewa ne kamar mukunnin fitilar lantarki da ake rage hasken kadan-kadan ko kuma abin kara maganar rediyo, inda ake rage maganar kadan da kadan har ta yi shiru gaba daya, to haka wannan aiki na jikinmu yake a lokacin da muka kama hanyar barci sai dai ba cikin sauki shi yake kasance wa ba.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mukan hada wani abin da muke ji na zahiri da mafarki.

Bijirowar da sauran karfinmu na farke yake yi shi ne ke sa mu wannan 'yar fizga ko rausayawa da muke yi lokacin gywangywadi da yayin da muka kama hanyar barci, kuma har yanzu ba a san cikakken dalilin da ke sa mu hakan ba.

Ba kamar lillinshewar ido ba, wannan 'yar fizga ba ta da wata alaka da kwakwalwarmu da ke yanayi na mafarki a lokacin, burbushi ne na sauran karfinmu na ranar.

Abin yana da hadari?

Wani yanayi na jin kanmu kamar zai fashe shi ma irin wannan dabi'ar jiki yake yi, inda abubuwa biyu yanayi na farke da kuma na barci ke gwagwarmayar kwace iko da jikin mutum, hakan kuma sai ya haifar da wannan yanayi na ganin hasken wuta da jin kara.

A wani lokaci idan abin ya yi tsanani yakan hana mutum barci ko ma mutum ya yi ikirarin an sace shi.

Gaba daya dai wannan yanayi da mutum ke samun kansa ciki, ba wani abin damuwa ba ne, yanayi ne kawai na wata 'yar dambarwa mai ban dariya ta hawa da kuma gangarar zuwa duniyar barci.

Akwai kyakkyawan fasali tsakanin motsin da muke yi iri biyu lokacin da muke barci,'' kamar yadda Stafford ya rubuta.

Lillinshewar idanuwa birbishi-birbishin alama ce ta mafarkin da za a iya gani a duniyar farke (lokacin da ba barci muke ba).

Ita kuwa wannan 'yar fizga ko rausayawa da muke dan yi kamar 'yar alama ce ta rayuwar farke wadda ke yi wa duniyar mafarki kutse.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why does it feel like I'm falling as I go to sleep?