Yadda za ka rayu har abada

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Idan ana samun karuwar mutanen da suke kaiwa shekara sama da 100, shekara nawa kenan za mu iya rayuwa a hasashe? Kamar yadda Frank Swain ya tambaya. Kuma ta yaya za a iya samun hakan?

Dakta Huseland (daya daga cikin kwararru da suka fi basira a Jamus) shi ne ya rubutu kan hanyar tsawaita rayuwa mai suna 'On the Art of Prolonging Life' a shekarar 1797 bayan ya kammala binciken shekara takwas a kai.

Ya gano wasu hanyoyi da za a iya bi domin cimma wannan buri, wadanda suka hada da bin hanyar rayuwa ta tsaka-tsaki ta cin kayan itatuwa sosai da cin nama kadan da barin kayan ciye-ciye da shaye-shaye masu zaki na zamani, da kula da lafiyar hakori da wanka da ruwan dimi da sabulu a sati da wadataccen barci da shakar iska mai kyau sannan kuma ya kasance iyayen mutum su ma sun yi rayuwa mai tsawo.

A kusan karshen kasidarsa wadda aka fassara a Amurka, likitan ya nuna cewa ''rayuwar mutum za ta iya tsawaita linki biyu kan yadda take ba tare da mutum ya kasa moruwa da amfani ba.''

A bisa kiyasin Huseland, rabin dukkanin yaran da aka haifa za su rasu ne kafin su kai shekara goma, wadda wannan babbar annoba ce.

Sai dai kuka idan har yaran za su tsira daga cutukan da ke hallaka yara irin su kyanda da bakon dauro da sauransu suna da damar kaiwa sama da shekara talatin da rabi.

Dakta Huseland yana ganin idan komai zai tafi yadda ya dace mutum zai iya kaiwa shekara 200 a raye.

Anya wannan ba tunani ne kawai na nishadi na likitan karni na 18 ba? James Vaupel yana ganin wannan ba abu ne da za iya cewa ba zai yuwuwu ba.

Ya ce, ''lokacin da ake sa ran mutane za su kai a rayuwa yana karuwa da shekara biyu da rabi a duk shekara goma.'' Wato ''shekara 25 kenan a duk karni.''

A matsayinsa na darekta a harkokin a Jamus ( Laboratory of Survival and Longevity at the Max Planck Institute for Demographic Research in Rostock, Germany), Vupel ya yi nazari a kan tsawon rayuwa da rayuwa a cikin al'ummar mutane da dabbobi.

Ya gaya min cewa yanayin cigaban da aka samu na mace-mace ya karu sosai a shekara 100 da ta gabata.

Kafin shekara ta 1950 an samu yawancin nasarar tsawon rayuwar da ake sa ran mutane su rika kaiwa ta hanyar rage yawan mutuwar yara wadda Huselanda ya yi hasashe.

Tun daga wannan lokacin mutanen da suka wuce shekara sittin ne da kuma a baya bayannan 'yan sama da shekara 80 mutuwarsu ta ragu sosai.

Ma'ana kenan yanzu ana samun yara da yawa da suke rayuwa, kuma muna rayuwa shekaru da yawa fiye da da.

Bambancin shekaru

An yi hasashen cewa a fadin duniya yawan mutanen da suka dara shekara 100 zai linka goma tsakanin shekara ta 2010 da 2050.

Kamar yadda Huseland ya tabbatar wani abu mai karfi da zai tabbatar da ko za ka kai wannan shekaru ko ba za ka kai ba, ya dogara ne ga shekarun iyayenka, wato akwai kwayar halitta da ke tabbatar da tsawon rayuwa.

Amma kuma yawan karuwar mutanen da suka wuce shekara 100 ba abu ne da za a danganta shi da kwayar halitta ba kawai, wanda a zahiri bai sauya ba sosai a 'yan daruruwan shekarun da suka gabata.

A maimakon haka abubuwa ne da yawa da suka danganci sauyi a rayuwarmu suka haddasa hakan wadanda da yawa daga cikinsu na daga abubuwan da Huseland ya ambata.

Dalilan sun hada da kyakkyawan tsarin kula da lafiya da samun ingantattun hanyoyin yi wa marassa lafiya magani da samar da ruwa da iska masu kyau da ilimi mai nagarta da samar da rayuwa mai inganci kamar samar da gidaje masu dumi da ba su da lema.

''A takaice abin dai ya ta'allaka ne ga samun magani mai yawa da kudi,'' in ji Vaupel.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption A shekarun nan an samu karuwar yawan shekarun da ake sa ran mutane za su yi

Amma duk da wannan cigaba na karuwar shekarun mutane da ingantaccen tsarin kula da lafiya da kuma kyakkyawan yanayin rayuwa suka samar har yanzu mutane da dama ba su gamsu ba, kuma kokarin sanin wasu hanyoyin samun tsawan rayuwa ba ya nuna wata alamar raguwa.

Wata hanya da aka fi sani ita ce ta rage yawan abinci, inda a shekarun 1930 wasu masana suka lura cewa berayen da aka rika ba su abinci kadan sun fi tsawon rayuwa a kan wadanda ake ba su abinci har su ci su koshi.

Haka kuma wani gwajin da aka yi irin wannan a kan birai shi ma ya tabbatar da hakan, sai dai, wani nazari na shekara 20 da cibiyar kula da yawan shekaru ta Amurka (US National Institute on Ageing) ta gudanar, ya gano sabanin haka.

A nazarin ta gano cewa biran da aka takaita musu yawan abincin da suke ci sun gamu da cutukan da suka danganci tsufa ko yawan shekaru, kuma yawanci ba su yi sheakaru masu yawa ba.

Masu binciken sun lura cewa, ko da yake takaita abincin da dabbobi ke ci yana da wasu alfanu, amma dai hakan ya dogara ne kuma ga wasu abubuwan, kamar kwayoyin halitta da irin abincin da suke ci da kuma yanayin muhallin da suke.

Wani abu kuma da ake sa ran zai kai ga burin da ake so a cimma, shi ne wani sinadari da tsirrai suke samarwa a jikinsu (resveratrol), musamman a fatar girho (lemo).

Abu ne dai da har yanzu ba a kai ga tabbatarwa ba ko cewa maganin tsufa yana nan tare a gonar girho.

An lura cewa wannan sinadari yana samar da alfanu iri daya ga lafiyuar dabbobin da aka takaita musu abincin da suke ci, amma har yanzu ba wani nazari da ya nuna amfani da wannan sinadari (resveratrol) zai iya kara yawan shekarun mutun.

Ba iyaka.

To ma me ya sa muke tsufa ne? ''Kullum muna jin rauni amma kuma ba ma warkar da raunukan,'' kamar yadda Vaupel ya yi bayani, ''to kuma tarin wannan rauni ne da ba ma warkarwa shi ke haddasa cutukan da suka danganci tsufa ko yawan shekaru.''

Sai dai wannan ba yanayi ba ne da duk wata halitta mai rai take da shi, domin misali tarin wata halittar ruwa (hydra), na iya warkarwa tare da maye gurbin duk kwayar halittarta da ta ji rauni da kuma wadda ba za ta warke ba.

A jikin mutum, wadannan kwayoyin halitta da suka ji rauni su kan haddasa ciwon daji.

Su wadannan tarin halittu na ruwa (hydra) suna ware wani kaso a jikinsu na gyara ko warkar da raunin da jikin ya ji, maimakon haihuwa,'' in ji Vaupel.

''Sabanin hakan, su mutane ainahi suna ware abubuwa ne a jikinsu domin haihuwa maimakon warkar da kwayoyin halittun da suka mutu, wannan tsari ne na bambancin rayuwa tsakanin halittu.''

Mutane za su iya rayuwa da sauri kuma su mutu da wuri, amma yanayin kwayoyin haihuwarmu na gado suka ba mu damar shawo kan wannan yawan mutuwa.

Tun da yanzu babu yawan mutuwar yara sosai, babu bukatar ware sinadarai da yawa a jiki domin haihuwa, in ji Vaupel.

''Dabarar ita ce karfafa warkar da ciwukan maimakon tura wannan sinadarai wajen samun karin maiko a jiki.

A rubuce, hakan abu ne da zai iya faruwa, ko da yake ba wanda ya san yadda hakan za ta iya faruwa ko yadda za a iya yin hakan.''

Idan za a yi kawo karshen lalacewa ko raunin da kwayoyin halittar jikinmu ke yi a hankali a hankali, to da kenan shekarunmu ba za su kasance da iyaka ba idan muka manyanta.

Kuma idan da hakan za ta kasance to da babu wani dalili da zai sa mu mutu ma samsam.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Wannan halitta hydra za ta iya gyara kusan duk kwayoyin halittarta da suke mutuwa ko lalacewa

Abu ne da zai zama mai ban sha'awa da mamaki a samu lokacin da za a ce mutuwa zabi ce, idan mutum yana so ya yi idan kuma ba ya so ya tsaya a raye.

''A yanzu dukkaninmu a takaice an yanke mana hukuncin kisa, duk da cewa yawancinmu ba mu yi wani abu ba da muka cancanci wannan hukunci ba.'' In ji Gennady Stolyarov, wani masanin falsafa kuma marubucin littafin yara na 'Death Is Wrong' mai cike da cece-kuce wanda ke karfafa wa matasa zuciya su yi watsi da tunanin cewa mutuwa dole ce.

Stolyarov na matukar adawa da abin da yake gani kawai a matsayin wani kalubale na fasaha da ke jiran samun kudin da ya dace da kuma kuduri domin magance shi ( mutuwa).

Masu kawo sauyi

Wani abu da fasaha za ta mayar da hankali a kai shi ne dakatar da gutsirewar bakin kwayoyin halittarmu wanda ke kare zaizayewar zaren karshen kwayar halittar (kamar 'yar robar nan ta karshen igiyar takalmi wadda ke hana zaizayewar igiyar).

Saboda a duk lokacin da kwayar halittarmu ta rabu wannan baki sai ya gutsire, wanda hakan ke sanya wa kwayar halittar wata iyaka ta sau nawa kwayoyin halittar za su hayayyafa.

Ba kowace dabba ba ce take da wannan yanayi na gutsirewar wannan baki, kuma hydra na daga cikinsu.

Sai dai akwai dalilai masu amfani kan wannan takaitaka a kan dabbobi. Sauyawar kwayoyin halitta zai iya bai wa kwayoyin halitta su rika lillinkawa ba tare da gutsire bakin kwayoyin halittar ba, wanda hakan zai sa a samu kwayoyin halittar da ba za su mutu ba.

To amma a yanayin da zai kasance wadannan kwayoyin halitta marassa mutuwa za su yi ta samuwa ba tare da ka'ida ba, hakan ba zai zama alheri ga jikin mutumin da suke cikinsa ba domin za su rika zama kurajen ciwon daji.

Mutane dubu 150 ne suke mutuwa a duniya kullum, kuma biyu bisa uku na wannan adadi suna mutuwa ne sakamakon rashin haihuwa da girman kwayoyin halitta na jikin mutum sakamakon shekaru,'' Stolyyarov ya gaya min.

''Saboda haka ko da za mu iya hanzarta zuwan wannan fasaha domin cimma nasarar dakatar da wannan rashin hayayyafa na kwayoyin halittar da kwana daya, da za mu ceci rayukan dubban daruruwar mutane kenan.

Marubucin ya bayar da misalin wata magana da wani fitaccen mai nazari kan tabbatar da karuwar tsawon rayuwa Aubrey de Grey, inda ya ce akwai dama ta kashi 50 bisa dari ta rage rashin hayayyafar kwayoyin halittar mutane a shekaru 25 nan gaba.

'' Akwai kyakkyawar damar cewa hakan zai tabbata a lokacin rayuwarmu, kafin mu ga matukar illar rashin hayayyafar kwayoyin halittar,'' in ji Stolyarov.

Amma kuma Vaupel ya ce cimma wannan nasara a shekaru 25 abu ne da zai iya tabbata, amma kuma ba lalle ba.

Sai dai ya amince cewa abu ne da zai iya yuwuwa a tsawaita yawan shekarun mutane ta hanyar samun fasahohi a fannin likitanci.

Amma kuma ya yi gargadin cin karo da kalubale ko matsalolin da ba mu yi tsammani ba.

''Cutuka da matsalolin tattalin arziki da dumamar yanayi za su iya haddasa yawan mutuwar mutane,'' in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Zaizayewar bakin wannan kwayar halittar mutum (Chromosomes) na da alaka da tsufa

Stolyarov yana fatan haifar da kwarin gwiwa da kyakkyawan fata na sanin yadda za a iya cimma rayuwa mai dorewa, wadda ba mutuwa.

''Abin da nake gani ya wajaba yanzu shi ne samun kudurin hanzarta cigaban fasahar,'' ya ce.

''A yanzu muna da damar wannan yaki, amma idan har muna son ganin hakan ta tabbata dole ne mu zama masu jagorantar tabbatar da hakan.''

A halin yanzu sai dai masu karatu su samu kwanciyar hankalin cewa, akwai tabbatattun hanyoyi na kokarin kauce wa hanyoyi biyu da suka fi kashe mutane a yammacin duniya, wato cutar zuciya da kuma ta daji, ta hanyar motsa jiki da cin abinci mai kyau da kuma takaita shan barasa da cin jan nama.

'Yan kadan ne daga cikinmu muke jurewa mu kiyaye da wadannan kai'doji, watakila saboda muna ganin rayuwa 'yar gajeruwa cikin wadatar abinci da barasa aba ce da ba za a iya kaucewa ba, abin da wai kuda ke cewa ''ranar biyan bukata rai ba a bakin komai yake ba''

Wanda wannan ya kai mu ga tambayar nan ta cewa, ''idan rayuwa ta dundundun aba ce da za a iya samu, shin a shirye kake ka yi abin da za ka same ta?

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How to live forever