'Yan kwana-kwana za su rika tashi sama

Hakkin mallakar hoto Martin aircraft

Dubai na shirin bai wa ma'aikatanta na kashe gobara wata na'ura (jetpacks)da za su rika tashi sama kamar tsuntsaye, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Anya wannan dabara ce mai kyau kuma maras hadari?

Chris Baraniuk ya duba yadda wannan kasada take.

Tsawon lokaci ana daukar wannan sabuwar na'ura (jetpacks) a matsayin wata hanya da daidaikun mutane za su rika sufurinsu da kansu, inda za su rika tashi sama kamar tsuntsaye.

Hatta James Bond yana da wannan na'ura tasa ta kansa, duk da cewa ba ta zama gama-gari ba.

Amma a shekarun nan ana ta kara nuna sha'awar yadda za a yi wannan na'ura ta tabbata.

Yanzu dai 'yan kwana-kwana a Dubai watakila na daga cikin mutanen farko da za su samu wannan na'ura a matsayin kayansu na aiki.

Da farko dai abin da za a sani shi ne, wannan na'ura da wani kamfanin New Zealand Martin Jetpack ya kirkiro, ba ta tashi sama da iskar gas.

Maimakon haka tana da farfela ne kamar ta jirgi mai saukar ungulu a cikin wata 'yar akwati ta musamman.

Sannan kuma akwai wata 'yar farfelar a kasa ta sarrafa iska da tafiyar na'urar a sama.

Amma me ya sa Dubai take son bai wa ma'aikatanta masu kashe gobara wannan na'ura? Kuma shin abu ne ma da ya dace?

Kwangilar samar da na'urar tsakanin hukumar tsaro ta farin kaya ta Dubai da kamfanin Martin Jetpack ta miliyoyin dala ce, ko da yake ba a bayyana ainahin yawan kudin ba.

Ana ganin kamfanin zai samarwa da Dubai din jumullar wannan na'ura 20, kowacce da za ta iya tashi da gudun cin kilomita 72 a cikin sa'a daya, kuma ta yi sama tsawon kafa dubu daya.

Ana sa ran za a rika amfani da su ne wajen kai dauki musamman a lokacin gobara a dogayen gine-gine, inda za a rika lekawa domin gano alamar masu rai.

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Daya daga cikin zane-zanen Jean-Marc Côté a 1899 na yadda ya yi hasashen shekara ta 2000 za ta kasance, inda masu kashe gobara za su rika tashi sama

Alamar wannan tunani ta samar da 'yan kwana-kwana masu tashi sama an nuna ta ne a wani zane na wani hatimin wasika na kasar Faransa wanda aka zayyana tun a shekarar 1910, amma ba wani yunkuri da aka yi tun a lokacin na tabbatar da hakan sai a yanzu.

Ko da yake ma'aikatan kashe gobara na Manchester a Biritaniya na amfani da jirage maras matuka domin daukar hotunan gobara, ta yadda ma'aikatan da ke kasa za su san inda za su fesa ruwa.

Amma dai a ce ga mutane masu tashi sama kamar tsuntsaye, wannan wani sabon abu ne na daban gaba daya.

Jim Krane na jami'ar Rice, da ke Amurka, marubucin littafi a kan kasancewar Dubai birnin da ya fi habaka a duniya (dubai: The Fastest City), bai yi mamaki ba, yadda birnin ya ke niyyar amfani da wannan tsari wajen kashe gobara a dogayen gine-gine.

''Suna da bukatar hakan, saboda ba su da kwarewar da za su iya maganin gobara a dogayen gidaje da kuma ceto daga irin wadannan wurare,'' kamar yadda ya ce. ''Babbar matsale a gare su.''

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Anfani da irin wannan fasaha da ruwa ke daga allon da mutum yake kai, zuwa sama, za a ga kamar abu ne mai kyau a tsari amma a zahiri ba shi da amfani

Krane ya kara da cewa a shekarar 2007 ya ga yadda wata mummunar gobatra ta tashi a wani dogon gini da ake ginawa a lokacin.

A lokacin, ma'aikaci daya ya fado ya mutu, wani kuma ya mutu a ciki, sannan kuma da dama gobarar ta rutsa da su a ciki, kafin daga baya a ceto su.

''Mutanen sun makale ne a jikin ginin daga waje, yayin da yake cin wuta kuma ma'aikatan kashe gobara ba za su iya yin komai ba,'' in ji Dakta Krane.

Ya ce, yanzu dai abin jira a gani shi ne, ko samun wannan fasaha zai sa 'yan kwan-kwanar na Dubai su iya maganin babbar gobara irin ta dogayen gine-ginen.

Ko ma dai ya za ta kasance, wannan abu ne da ya dace da Dubai, a matsayinsa na birni mai kirkire-kirkiren sabbin abubuwa.

Dakta Krane ya ce, ''yadda suke yin abubuwansu kenan, a ko da yaushe suna son zama na farko da za su ci moriyar kusan komai.''

Masanin ya kara da cewa, ''idan abu ya kasance kamar wani iri daban (wanda hankali ba zai iya dauka ba), kuma kana bukatar wajen da za ka gwada shi ko kasuwar da za ka jarraba shi, to Dubai ne wurin.''

Kamfanin Martin Jetpack kusan ba shi kadai ba ne ke neman jan hankalin masu sha'awar sayen wannan fasaha da masu zuba jari ba.

Akwai kamfanin Australia ma, Jetpack Aviation, wanda a kwanan nan ya gwada irin tasa na'urar a wurin hasumiyar butun-butumin 'yanci na Amurka ( Liberty Statue), inda mutum ya tashi sama har zuwa wurin gunkin mai nisan mita 93 ko kafa 305 da inci daya daga kasa.

Hakkin mallakar hoto Buzz60
Image caption David Mayman ya tashi sama da irin na'urar ta jetpack har zuwa kusa da butun-butumin alamar 'yancin Amurka (Statue of Liberty)

Idan muka koma kan Dubai din kuwa, akwai kuma wata na'urar mai kamar riga da ke amfani da kamar fasahar jirgin sama ta Yves Rossy, wadda ita ma ta dauki hankalin jaridun duniya a kwanan nan bayan da Ba-faranshen ya tashi sama da ita har ya je gefen wani katon jirgin sama da ke tafiya.

Ita dai waccan na'ura ta baya (jetpack) har yanzu sabuwar fasaha ce domin hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama ba su ma fara tunanin amfani da ita ba.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Biritaniya na daya daga cikinsu, kamar yadda kakakinta ya ce, ''ba abu ne da aka ma bukace mu mu bayyana ra'ayinmu a kai ba.''

''Duk abin da yake tashi a sama, yana karkashin abin da aka sani dokokin iska kuma wannan ya hada da sauran fasahohi,'' ya kara da cewa.

''Duk da cewa ba ma ganin a nan kusa za a yi amfani da fasahar wurin aikin kashe gobara a Biritaniya a nan kusa, abu ne da za a so a gani yadda za a yi amfani da wannan na'ura,'' in ji mai magana da yawun kungiyar ma'aikatan kashe gobara ta Biritaniya.

''Musamman ma idan aka yi la'akari da irin dogayen gine-ginen Dubai, da matsalolin da sukan haifar wa masu kashe gobara wajen kai daukin gaggawa'' in ji mai maganar.

Irin wannan rashin tabbas ne amfani da jirgi maras matuki wurin kashe gobara ya fuskanta.

Kuma har yanzu yake fuskanta, amma dai ana cigaba da kokarin shawo kan hakan, musamman ganin yadda jiragen ke kara yawa.

Ganin yadda fasaha ke ta bunkasa musamman kan wannan na'ura (jetpack) watakila lokaci ya yi da ya kamata a ce mun fara tunani sosai kan amfani da ita.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Dubai wants to give its firefighters jetpacks