Maza ko mata, wadanne aka fi son samu a 'ya'ya?

Hakkin mallakar hoto juniors bildaarchiv gmbh alamy

Ko wasu dabbobi hadi da mutane za su iya zabar jinsin 'ya'yan da za su haifa? Kuma menene amfanin hakan?

Daniel Cossins ya nitsa bincike

An san yadda sarki Henry na takwas (Henry VIII) na Ingila ya yi ta fafutuka wajen ganin ya samu da namiji da zai gaje shi, inda har ya auri mata shida, wadanda ya hallaka biyu daga cikinsu domin ganin ya cimma wannan buri nasa.

Ya tsananta a kan buri nasa, to amma, ba Henry ba ne kadai yake da wannan fata na zabar jinsin 'ya'yansa.

Ma'aurata su kan jarraba hanyoyi da abubuwa da dama domin ganin sun samu da namiji ko 'ya mace.

A zamanin Girkawa na da, maza sukan kwanta a bangaren jikinsu na dama a yayin saduwa da mata domin su haifi da namiji.

A karni na 18 a Faransa, an yi amanna cewa idan namiji ya daure dan golansa na hagu a lokacin jima'i, shi ma zai samu namiji.

A wannan zamanin na yau kuwa littattafai irin su 'How to Choose the Sex of Your Baby' suna ba da shawara ga ma'aurata (ko namiji da mace da suke tare), wadanda suke son haihuwar namiji, da su yi kokarin samun ciki ranar da mahaifa za ta bude ko kuma kwana daya kafin ranar.

Dabarar a nan ita ce, maniyyin da yake dauke da kwayar halitta mai alamar harafin Y, wanda ke samar da namiji, ya fi maniyyin da yake dauke da kwayar halitta mai alamar harafin X, mai samar da mace gudu, amma kuma ba ya dadewa.

Babu wata sheda da ke tabbatar da duk wadannan dabaru suna da aiki, kuma da yawa daga cikinsu yanzu sun zama abin dariya.

Amma kuma ana ganin ga alama dabbobi da dama, ba tare da sun sani ba suna sauya yawan jinsin 'ya'yansu, inda suke haihuwar maza da yawa ko mata da yawa.

To me zai sa dabbobi su zabi haihuwar wani jinsi fiye da wani? Ta yaya suke yi? Kuma mutane ma za su iya yin hakan su ma?

A shekarun 1930 ne wanna labari ya fara, a lokacin da kwararre a kan ilimin halittu masu rai (biologist), Ronald Fisher ya yi kokarin bayyana wani abu da ya gagari Charles Darwin fahimta.

Wannan abin kuwa shi ne, yadda dabbobin da ke haihuwa yawanci su kan haifi yawan 'ya'ya maza da mata kusan daidai, amma kuma ba wanda ya san dalili.

Fisher yana ganin bambancin yawan jinsi abu ne da ya kamata ya daidaita kansa da kansa.

Idan maza suka fi mata yawa (a taron dabbobin), idan aka kasa kowane namiji daya zai samu kasa da mace daya.

Hakan na nufin kenan sai iyaye sun dauki nauyin samar da karin 'ya'ya mata, domin ta hakan ne za su samu damar samun jikoki, da kuma kare kwayar halittarsu daga bacewa daga doron kasa.

Saboda haka idan 'ya'ya maza suka yi yawa, sai iyaye su samar da karin 'ya'ya mata.

Haka kuma idan mata ne suka yi yawa, idan aka kasa kowane namiji zai samu fiye da mata daya, saboda haka sai iyaye su samar da karin 'ya'ya maza.

A bisa wannan dalilin ne tsarin yawan maza da mata ko da yaushe zai tabbatar da ganin yawan ya zama daidai, wato namiji daya mace daya.

Wannan bayani ne mai kyau. Sai dai akwai matsala daya. Masana ilimin halittu masu rai sun nuna cewa ba a ko da yaushe ba ne hakan yake zama daidai.

A wani lokaci iyaye sun fi jin dadin samar da wani jinsin fiye da wani, kamar a misali, kwaron itacen baure (mai kama da zanzaro), yana haihuwar mata ne yawanci.

Hakkin mallakar hoto Jane BurtonNPL
Image caption Nawa ne maza nawa ne mata a nan?

Kwaron da ke yada kwayoyin furen baure yana da dangantaka ta cuda-nni-in-cude-ka da bishiyar ta baure.

Shi kwaron yana yada kwayoyin da furen yake bukata ya haifar da 'yan ita censa, shi kuma a nasa bangaren itacen yana bayar da kariya tare da renon 'ya'yan kwaron.

Wata daya ko kusa da haka kafin 'ya'yan itacen baure su nuna, sai matar wannan kwaro ta je wurinsu, ta shiga ciki ta wasu 'yan kananan kofofi.

Wadannan kofofi bayan wani dan lokaci sai su rufe tare da matan a ciki.

Wannan mata sai su kai kwayoyin da furen ke bukata, sai dan itacen ya girma da matar kwaron a ciki, wadda ita kuma za ta yi kwayaye sannan ta mutu a ciki.

Idan kwayayen suka kyankyashe, sai mazaje marassa fukafuki su rika saduwa da mata, sannan kuma matan sai su tafi.

Yawancin nau'in wadannan kwari na baure suna samar da 'ya'ya ne masu kyawun gaske kuma 'yan kadan, inda a wani lokacin ma kusan kashi biyar cikin dari na 'ya'yan da suke samarwa maza ne.

Za a ga wannan kamar wani abu ne na daban, amma akwai dalilin da ya sa.

Saboda duk saduwar da ake yi tsakanin maza da mata, ana yinta ne a cikin baure daya, mazajen kwarin suna gasa ne da kannensu ('yan uwansu) wajen neman matan, wadanda su ma kuma kannensu ne yawanci. Mazan da ba su samu saduwar ba tamkar ma a ce ba a haife su ba ne.

Hakkin mallakar hoto Danita DelimontAlamy
Image caption Wannan kwaron nau'in zanzaro da ke yada furen baure yana iya tsara namiji ko mace yake son haifa

''Idan ka haifi maza kadan, gasar da sauran mazan da ke nan za su gamu da ita ta neman matan da za su sadu da su kadance, kuma darajar kowane da namiji ta karu kenan,'' in ji Stuart West na jami'ar Oxford a Biritaniya.

Wani abin kuma shi ne yawanci mazajen suna saduwa ne da 'yan uwansu (kannensu) mata, saboda haka ''idan ka haifi karin mata, ka samar da karin matan da 'ya'yanka maza za su sadu da su kenan.''

Wannan shi ne kamar daidai da abin da masanin halittu William Hamilton ya yi hasashe a kusan karshen shekarun 1960.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wani abin kuma shi ne idan ya kasance gasar saduwar tsakanin maza ta yi tsanani, (wato babu mata da yawa da za su yi aure da su), sai ya kasance iyayen suna samar da mazan kadan.

Nau'in wannan kwaro wanda ake kira nasonia vitripennis, babban misali ne na hakan.

A nazarin da West da abokan bincikensa suka yi a 2008 sun gano cewa, '' mata suna karkatar da jinsin 'ya'yansu ya dace da jinsin kwayayen da sauran mata suka zuba a wurin da suke zuba kwan.

Idan ya kasance matan da suka fara zuba kwai, sun yi na jinsin maza ne, to ita wadda ta zo daga baya sai ta yi na jinsin mata.

Haka kuma idan na farkon sun yi na jinsin mata ne ita kuma sai ta yi na jinsin maza, ta yadda ba za a samu gasa mai tsanani ba, a wurin saduwa.

Amma kuma idan matar ta zo ta ga ba wata da ta yi kwai a wurin, to sai ta yi kwan da za a samu mata.

Hakkin mallakar hoto Richard Du ToitNPL

A shekara ta 1978, Anne Clarke ta jami'ar Binghamton da ke New York, ta yi nazari a kan yanayin hayayyafar wani nau'i na biri da ake samu a kasashen Afrika na kudu da hamadar Sahara (thick-tailed bushbabies).

A binciken ta gano cewa wannan dabba na haihuwar maza fiye da mata, inda mai binciken ta ce hakan na kasancewa ne saboda gasar abinci.

Su wadannan dabbobi (bushbabies), idan suka girma, suka kai munzalin manya, sai su bar uwarsu.

Amma su mata ba sa tafiya su bar uwar tasu, sai su zauna tare da ita, abin da ke sa gasar abinci a tsakanin uwar da 'ya.

A saboda haka ne ake ganin su matan wannan dabba sun fi son su haifi maza.

Akwai wani binciken da ke kara tabbatar da hakan. A shekara ta 2008 Joan Silk wadda yanzu take jami'ar jiha ta Arizona a Tempe, ta yi nazari a kan yawan bambancin maza da mata a tsakanin nau'in birai 102.

Mai binciken ta gano cewa jinsin wadanda ake haifa yawanci na wadanda suka bar wurin uwayensu mata ne.

Amma wannan ba haka yake kasancewa ba a ko da yaushe. A wani lokacin iyayen da ke haihuwa, suna samar da 'ya'yansu ne domin su taimaka wajen haifar 'ya'ya na gaba wato jikoki. Wannan zai iya kawo sauyi a gaba dayan tsarin, wato ya mayar da hannun agogo baya.

Hakkin mallakar hoto Will BurrardLucasNPL
Image caption Karnukan dawa

A 2008 Silk ta yi aiki tare da J Weldon McNutt na Asusun hukumar kula da dabbobin daji ta Botswana, domin nazari kan yanayin bambancin jinsin maza da matsa tsakanin karnukan daji na Afrika.

Masu binciken sun gano maza sun fi mata yawa, amma kuma sun ce hakan ta kasance ne saboda yadda karnukan suke watsuwa.

Wasu sukan cigaba da zama a cikin garke daya, har bayan balagarsu, inda suke samar da abinci ga uwarsu da kuma kannensu, yayin su kuwa mata suke barin garken da wuri.

Silk ta ce, ''Maza sun fi mata taimako, saboda haka wannan kila shi ne dalilin da ya sa karnukan dajin suka fi haihuwar maza.''

Yawan haihuwar mazan ya fi tabbata a garken uwar da take karama wadda ba ta da 'ya'ya da yawa. ''Wannan shi ne lokacin da maza suka fi amfani,'' in ji Silk.

Duka wannan yana kara haifar da sarkakiya ne, kuma akwai wani rudanin ma da ke tafe.

Dole ne kuma mata su yi la'akari da yawan abincin da ake da shi, kafin su san jinsin 'ya'yan da za su haifa.

Babban misali a nan shi ne na wani nau'in tsuntsu mai kama da kanari,da ake samu a tsibirin Sikilis (syechelles) na tekun Indiya a gabashin Afrika, wanda ake kira Syechelles Warbler.

Auren wannan tsuntsu suna zama ne tare a wuri daya su kyankyashi da guda daya a shekara.

Yawanci maza matasa sukan watse ne su kama gabansu, yayin da su kuma mata sai su zauna tare da uwayensu mata suna taimakonsu.

Za ka dauka cewa za su fi samar da jinsin da ke taimaka musu ne (mata), to amma ba haka abin yake ba, in ji Jam Komdeur na jami'ar Groningen da ke Netherlands.

Ya ce maimakon haka abin da suke yi ya dogara ne ga inda suke zaune.

Idan suna zaune a wurin da yake da kwari sosai, mataimaka suna da amfani, amma idan a wurin da babu abinci sosai suke sai su samar da karin gogayya ta neman abinci.

Hakkin mallakar hoto Brent StephensonNPL

A 1996 Komdeur ya gano cewa auren wadannan tsuntsaye kashi 90 cikin dari na 'ya'yan da suke kyankyasa mata ne, idan suna wuri mai albarkar abinci.

Haka kuma suna samar da maza kashi 90 din cikin dari idan kuma wurin da suke ba shi yalwar abinci.

A wani gwaji da ya yi kuma, masanin, ya dauke wasu tarin aure na tsuntsayen daga wurin da ba abinci sosai ya mayar da su inda ake da abinci, sai ya ga sun sauya yanayin 'ya'yan da suke samarwa daga kashi 90 maza zuwa kashi 85 mata.

Daga nan mai binciken ya ce, ''wannan babbar alama ce da ke nuna cewa yawan jinsin 'ya'yan wannan nau'in tsuntsu (maza ko mata) ya dogara ne ga yanayin abincin da yake da shi a wuri.''

A wani nazari da aka wallafa a shekarar 2008 Komdeur ya sauya shekar tsuntsayen tsakanin auren da ba su da mataimaka, sannan ya sanya ido a kan tsuntsayen har tsawon shekara uku. Sai ya ga iyayen suna samun karin jikoki.

Misali, iyayen da ke zaune a wurin da ba abinci sosai suna samun karin jikoki idan suna da 'ya'ya maza wadanda ba su suka kyankyashe su ba, fiye da iyayen da suke zaune su ma a wurin wadanda su kuma suke da ta 'ya mace wadda ba su suka kyankyashe ta ba.

Haka kuma ana samun kishiyar hakan idan a wurin da ke da yalwar abinci ne.

Hakkin mallakar hoto David PikeNPL
Image caption Wannan tsuntsun (Seychelles warblers) yana da tsari na daban kan yadda jinsin 'ya'yansa zai kasance

Wato iyayen da suke kula da 'ya'ya mata, wadanda ba su suka kyankyashe su ba, a inda ake da abinci sosai, sun fi wadanda suke kula da 'ya'ya maza wadanda ba nasu ba ne a wurin da ake da wadatar abinci.

''A wuraren da ake da abinci da yawa, 'ya'ya matan da suke na goyo za su iya zama su ma abokan samar da 'ya'ya, inda za su rika yin kwai su ma a shekar uwar rikon nasu ba tare da sun cutar da 'ya'yanta ko kannensu ba,'' Komdeur ya yi bayani.

Wannan zai kara yawan jikoki kenan amma fa sai da wadatar abinci.

Tsuntsayen suna sauya yanayin yawan jinsin 'ya'yansu bisa dogara da yadda yanayin rayuwarsu ya kasance.

Sauran dabbobi kuwa sun dan zarta haka, inda su kuma suke sauya yanyin yawan jinsin 'ya'yan nasu bisa sauyin yanayin kansu.

Hakkin mallakar hoto Danny Green2020VISIONNPL
Image caption Barewa

Tim Clutton-Brock na jami'ar Oxford da ke Biritaniya ya taba kwashe shekaru yana nazari a kan barewa (mata) a tsibirin Rhum na Scotland.

A shekara ta 1984, ya gano cewa matan da suke da babban matsayi suna haihuwar maza da yawa, yayin da wadanda suke da karamin matsayi ko baya a dangi yawanci haihuwar mata.

Watakila wannan zai iya kasancewa ne saboda masu babban matsayin sun fi koshin lafiya da wadata.

Shekaru goma kafin wannan nazarin, Robert Trivers, masani kan halittu masu rai da masanin lissafi Dan Willard ya nuna cewa, matan bareyin da suke da koshin lafiya za su fi haihuwar 'ya'ya maza.

Suna ganin cewa su 'ya'ya mazan za su rika gasa wajen samun matan da za su rika saduwa da su, saboda haka mazan da suke da inganci ne kawai za su iya samar da 'ya'ya masu yawa.

Saboda haka idan uwa tana iya samar da abubuwa da yawa ga 'ya'yanta, samun 'ya'ya mazan abu ne mai amfani kenan.

A daya bangaren idan uwa ba ta da wadatar koshi ko lafiya sai ta samar da 'ya'ya mata kawai, saboda su mata ko a yanayi na wuya za su haihu.

Idan uwa ba za ta iya zuba jari ba sosai (wato ta yi wadataccen kiwo) da za ta haifi maza, sai ta hakura da 'ya'yan da ba sai ta wahala ba a kansu, wato mata kenan.

Tamatar barewa tana zabar jinsin 'ya'yanta ne bisa yadda yanayin wadatar lafiyarta take (idan da wadata ta haifi namiji idan ba wadata sosai ta haifi mace).

To amma kuma za ta iya yin hakan ma idan ya kasance namijin da zai sadu da ita yana da nagarta.

Hakkin mallakar hoto Ross HoddinottNPL

Abin shi ne kyawun fasalin namiji alama ce ta irin ingancin kwayar halittarsa.

Idan ya haifi 'ya'ya maza su ma za su yi gadon wannan nagarta saboda ya yi aiki tukuru wajen na kula da su.

Wannan na nufin 'ya'yan namiji mai nagarta su ma za su samar da 'ya'ya masu yawa.

Idan mace ta sadu da namiji mai kyau, za ta haifi maza ne saboda suma za su zama masu kyau, su sami matan da za su sadu da su masu yawa,'' in ji Tim Fawcett na jami'ar Bristol ta Biritaniya.

Wannan kusan shi ne ke faruwa a wasu tsuntsayen. A shekarar 1999, Ben Sheldon na jami'ar Oxford da aboka aikinsa sun nuna yadda wani nau'in tsuntsu shudi mai kama da kanari (blue tits), idan tamatarsa ta sadu da namijin da yake da gashin fuka fuki mai kyau da haske sai su samar da 'ya'ya maza da yawa, idan aka kwatanta da tamatar da da sadu da namijin da ba shi kyau.

Da Sheldon ya kare wannan haske da kyallin da fuka fukin namijin mai kyau yake yi, ya zama ba wannan daukar idon da yake yi, sai matan idan sun sadu da su su rika samar da 'ya'ya mata.

Duka wannan yana nuna mana cewa dabbobi su kan iya tsara yadda suke son jinsin 'ya'yansu, ko da kuwa abubuwan da suke sa su wannan ra'ayi sanannu ne.

Amma kuma wannan ya kara taso da wata tambayar, wadda ita ce, ta yaya suke yin hakan?

Hakkin mallakar hoto Dmitry KnorreAlamy
Image caption Tarin kwayar halitta mai alamar harafin X ya fi mai alamar harafin Y girma

A kan kwari kamar su tururuwa ko kiyashi da zanzaro da zuma abu ne da yake sananne.

Kwayoyin halittarsu suna cikin wata doguwar halitta ce (chromosomes), wadda daya daga ciki ke kula ko tsara yadda jinsin 'ya'ya zai kasance.

Jinsin abin da za a haifa ya dogara ne ga yawan samfur nawa gare shi na wannan halitta.

Kwan da bai hadu da wani gauraye na maniyyi ba, yake da samfur daya kawai na wannan kwayar halitta sai ya samar da namiji.

Shi kuwa kwan da ya gauraya da wani maniyyi, ya samu samfur biyu na kwayar halittar sai ya samar da mace.

Saboda haka idan mata suka tsara ko kwansu zai hadu da wani maniyyi, ya samu wata kwayar halitta ko a'a suna iya tsara yadda jinsin 'ya'yansu zai kasance, mace ko namiji.

Sai dai a wurin dabbobi masu shayar da 'ya'yansu nono (mammals) da tsntsaye abubuwan da ke haifar da wannan sun fi daure kai.

''Abin da dabba za ta yi domin zabin yadda jinsin abin da za ta haifa zai kasance, abu ne da yake sananne sosai, amma kuma yadda suke yin hakan ne shi ne ba a sani ba,'' in ji Fawcett.

Ba kamar zanzaro da kudan zuma ba, dabbobi masu shayarwa da tsuntsaye suna tsara yadda jinsin 'ya'yansu zai kasance ne ta hanyar hada kwayoyin halitta daban-daban.

A dabbobi masu shayarwar, mata suna da wannan kwayar halitta mai kama da juna mai siffar harafin X, su kuwa maza suna da daya mai siffar harafin X da kuma mai siffar harafin Y.

Maza suna samar da yawan maniyyi daya da kwayar halitta mai X da kuma mai Y.

A bisa wannan tsarin, dace ne kawai, maniyyi mai wace kwayar halitta ne zai hadu da kwan mace (mai waccan kwayar halitta iri daya X).

Saboda haka damar daya da daya ce (1:1). Amma akwai sheda karara cewa mata za su iya kaucewa hakan ta wata hanya.

Hakkin mallakar hoto Tom RadfordAlamy
Image caption Salwa irin ta Japan

Wata hanya da ake ganin hakan ke faruwa ita ce, kwayoyin halittar da suke kewayawa a jikin uwa mai haihuwar, wadanda yanayin muhallin da dabbar take yake da tasiri a kan kwayoyin, yana taka muhimmiyar rawa.

A 2006, Marion Petrie ta jami'ar Newcastle ta nuna cewa yawan jinsin tskanin maza da mata na tsuntsayen nan nau'in salwa ta Japan yana bambanta da yawan kwayoyin halitta na gajiya (corticosterone.)

Haka kuma ta gano cewa idan aka yi yadda yawan wannan kwayoyin halitta ya karu sai tsuntsayen su fi karkata wajen samar da 'ay'ya mata.

Haka kuma yawan sukarin halitta na jikin dabba (glucose) ka iya tasiri wajen jinsin da dabba za ta samar.

A shekara ta 2008 wani nazari da aka yi ya nuna cewa tamatar beran da yawan sukarin cikin jikinta ya ragu tana haihuwar mata sosai fiye da wadda yawan sukarin yake yadda ya kamata.

Za kuma a iya samun yanayi da matar za ta zubar da kwayoyin wani jinsi. Sannan za su iya hana wasu kwayayen haduwa da maniyyin.

Akwai dai hanyoyi da dama da abin zai iya kasancewa, kuma babu dalilin da za a iya cewa dukkanin dabbobi suna suna amfani da tsari ko dabara iri daya.

Hakkin mallakar hoto World History ArchiveAlamy
Image caption Sarki Henry na takwas na Ingila ya matsu kan son haihuwar da namiji kuma ba shi da tabbas kan mata

'yan bincike kalilan sun duba yadda bambancin yawan jinsin mutum yake.

A 2009 Thomas Pollet na jami'ar VU ta Amsterdam da abokan aikinsa, sun bincika bambancin jinsi a tsakanin yara dubu 95 na matan Ruwanda, wadanda da dama daga cikinsu suna aure ne a mazajen da ke da mata fiye da daya.

Sun gano cewa matan da ba su da matsayi sosai sun fi haihuwar 'ya'ya mata fiye da mata masu matsayi da ke auren namiji daya.

A 2012 Shige Song ta jami'ar City da ke New York, ta nuna cewa matan kasar Sin (china) sun haifi mata da yawa fiye da maza a cikin shekaru biyun da aka yi fari a 1959 zuwa 1961, a lokacin da mutane miliyan 30 suka mutu saboda yunwa.

Wannan ya nuna cewa idan akwai karancin abinci, sai jikin mutum ya karkata samar da 'ya'ya mata, wadanda za su iya haihuwa ko da kuwa ba su da kuzari idan sun girma. Haka abin yake a dabbobin da ke shayarwa ma.

A daya bangaren kuwa kamar yadda wani nazari na 2009 ya nuna attajirai suna haihuwar 'ya'ya maza fiye da mata, kuma wadannan 'ya'ya mazan suna haihuwar jikoki fiye da su 'ya'ya matan.

Idan har za a iya yarda da duka wadannan nazarce-nazarcen, to kenan mutane suna da dama kamar yadda dabbobi suke yi ta karkata yawan jinsin 'ya'yansu yadda suke so.

Sai dai abin ba ya aiki ta yadda yawancinmu muke so ya zama.

Ko ma menene yake faruwa dai a wadannan nazarce-nazarce, ba abu ne da yake wanzuwa da saninmu ba, kuma watakila ya fi karkata ga jikin uwa fiye da na uba.

Kuma ba shi da wata alaka da abin da mutum ya fi so. Za ka iya burin ka samu 'ya mace ko da namiji saboda wasu dalilai na kashin kanka, amma ka sani duka wannan ya dogara ne ga kyawun kwayoyin halittar jikinka da kuma damar iya haifar 'ya'ya da jikoki masu nagarta.

Za ka iya kasancewa da matukar karfin burin jinsin abin da kake so ka haifa, amma kwayoyin halittarka sun fi karfi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Is it better to have more sons or more daughters?