Bunkasa haddarka cikin dakika 40

Hakkin mallakar hoto Getty

Ka taba jin cewa abubuwan da ka sani da dadewa ka fara manta su a hankali? To akwai wata hanya mai sauki da za ka iya dawo da haddarka ta abubuwan da ka sani a baya.

Ga bayanin David Robson.

Ka taba gani ko jin wani sashe mai ban sha'awa na wani fim ko waka ko barkwanci, wanda kuma ka manta shi zuwa wani lokaci?

Maimakon a ce ka iya tuna wannan abu karara wanda kake son tunawa, sai kawai dan kadan daga ciki kake iya tunawa ko ma abin takaici da haushi gaba dayansa ya bace maka.

Hatta wani muhimmin abu kamar saduwa da wani fitaccen tauraron fim, abin mamaki zai iya bace maka kacokan, cikin dan kankanin lokaci.

Sai dai ga alama da akwai hanya mai sauki ta kare wannan hadda taka daga zagwanyewa.

Kamar yadda wani bincike da Chris Bird a jami'ar Sussex da ke Biritaniya ya yi, abin da ake bukata kawai shi ne 'yan dakikoki na lokacinka da kuma dan tunani ba wani mai yawa ba.

A kwanan nan Dakta Chris Bird ya gudanar da wani aikin bincike, inda ya bukaci wasu dalibai su kwanta a cikin wata na'urar daukar hoton aikin kwakwalwa kuma suna kallon wasu hotunan bidiyo na YouTube (wanda ya hada da misali yadda makwabta ke barkwanci da juna).

Kai tsaye bayan kallon wasu daga cikin hotunan bidiyon, am ba su dakika 40, su sake ayyana abin da suka kalla a zuciyarsu, su bayyana wa kansu.

Sauran kuwa sun koma kallon wani sabon bidiyo ne kawai.

An gano cewa ta hanyar bayyana wa kansu abin da suka gani a hoton bidiyon kadai, hakan ya bunkasa damarsu ta tuna abin ainahin yadda yake bayan sati daya ko kusan haka.

Yawanci sun iya tuna kusan linki biyu na yawancin abubuwan da suka gani a hotunan bidiyon.

Dakta Bird ya kuma gano cewa hotunan aikin kwakwalwar da ya dauka suna nuna karfin haddar.

A lokacin aikin kwakwalwar yayin bayyanawa kan nasu a zuci yadda suka ga hotunan,kan yadda hankalinsu ya koma kacokan kan lokacin kallon bidiyon kusan daliban sun haddace abubuwan domin tunowa a gaba.

Wannan watakila wata alama ce ta yawan kokari da kuma bayanan da suke tunani, yayin da suke bayyana abubuwan da suka gani.

Zai kuma iya kasancewa, hakan na ba wa daliban damar danganta abubuwan da wasu abubuwa da suka sani (haddace a da), kamar yadda wani dalibin ya kwatanta wani daga cikin mutanen da ya gani a fim din da James Bond, wanda wannan ya sa ya yi saurin tuna shi.

Ma'ana dai idan kana son abu ya zauna a kwakwalwarka, kawai ka dauki minti daya ko sama da haka ka bayyana wa kanka abin, kana mai lura da muhimman bayanan da abin ya kunsa.

Masanin yana ganin yadda hakan ke da muhimmanci musamman a kotu, inda ya ce, '' nazarin yana da hadari ga duk wani lamari da ake bukatar cikakken bayani kan yadda abu ya faru, kamar bayanin yadda hadari ya auku ko aka aikata wani laifi.''

''Za ka iya bayar da cikakken bayani daga bisani idan har ka rika bitar yadda lamarin ya faru daki-daki jim kadan bayan aukuwarsa.''

Wannan dabarar tana da amfani a wurin duk wani mutum da shi ma yake son haddace wani abu da ke da muhimmanci.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Improve your memory in 40 seconds