Sabuwar fasahar kama barawo

Hakkin mallakar hoto science photo library

Kantunan sayar da kayayyaki sun fara amfani da fasahar gane fuskar mutum da kuma na'urar bin diddigin zirga-zirgar masu siyayya domin kama barayi.

Jonathan Keane ya gudanar da bincike

Wani mutum ya kama hanyar shiga wani kantin sayar da kayan kawa na mata a birnin Rotterdam, ya tsaya kofar ta bude ya shiga amma sai ta ki budewa. Ya tsaya yana jira. Yayin da yake jira a kusa da kofar, wata na'urar daukar hoto mai gane fuskar mutum cikin gaggawa ta dauki hotonsa, tana kwatanta shi da hotunan jerin masu sata a kantuna daga ofishin 'yan sanda na yankin.

Bayan wani lokaci sai a ka gano cewa an taba kama shi da laifin sata a wani kanti kuma mai wannan shago ba ya son ganinsa a harabarsa.

Wannan daya ne daga misalan wata sabuwar fasaha mai suna FotoSwitch a shekara ta 2011, wanda shiri ne da hukumar 'yan sanda ta Rhnmond da ke Rotterdam da ma'aikatar harkokin tsaro da shari'a ta Netherlands da kuma hukumar kula da harkokin gwala-gwalai da azurfa hade da tallafin wani kamfanin tattara bayanan jama'a na Spaniya mai suna Herta Security suka yi.

Shirin yana ba wa masu kantin sayar da kayan kawar na mata damar gudanar da binciken gaggawa ta hanyar na'urar daukar hoto a kan wanda ya zo sayen kaya kantin kafin ya shiga, ba tare da ya sani ba.

Haka kuma kofar ba za ta bude ba idan mai shiga yana sanye da bakin tabarau ko wani abu da ya rufe masa fuska.

Wannan ita ce fasaha ta zamani ta baya-bayan nan da masu kantunan sayar da kaya suke amfani da ita domin maganin barayi a kantunansu. To amma wannan ta isa ta sa su yi galaba a kan barayin?

Alkaluman da ofishin kididdiga na Biritaniya ya fitar sun nuna an samu karin yawan laifukan sata a kantuna, inda aka samu har 326,464 tsakanin watan Afrilu na 2014 da watan Maris na 2015 a kasar, idan aka kwatanta da 321,078 da 300623 a shekaru biyu da suka gabata.

Ana kara samun masu sata a shaguna, inda barayin suke amfani da sabbin dabaru wajen satar, misali yadda suke tsara ta'adar da za su yi ta shafin sada zumunta da muhawara na intanet.

Steve Rowen na kamfanin gudanar da bincike kan harkokin kantuna RSR da ke Amrka, ya ce daga cikin shagunan da ya ke yi wa aiki, ya gano cewa kalubalen yadda za su yi maganin yadda barayi ke satar fitar da kaya daga kantunansu shi ne suka fi fuskanta.

Hakan ne kuma ya sa aka samu bukatar samar da karin na'urori, ba na sanya ido ba kadai har da na kula da harkokin shagon gaba daya, daga ma'aikata zuwa gabatar da kayayyaki.

''Na'urar daukar hoto ta tsaro (CCTV) ba abin da za ta iya sai dai bayyana yadda mutum kawai yake,'' in ji Rowen.

Hakkin mallakar hoto Herta
Image caption Kamfanin Herta ya ce, na'urarsa tana bukatar ganin fuskar mutum ne ko da kadan ne kawai ta gane shi

Na'urar CCTV kyakyawan misali ne na ganin alamar wanda ake zargi yake, amma kuma ba abin da za ta iya yi kuma idan ba hoton wani da za ta kwatanta da shi, misali jerin sunayen masu sata a kanti ko wadanda ake zargi da hakan.

A yanzu kamfanoni da dama suna amfani da fasahar gane fuskar mutum (barayi) domin kare shagunansu daga barayi, in ji Joseph Rosenkranz, shugaban kamfanin fasaha na FaceFirst, wanda ya kirkiro na'urar gane fuskar.

Ya ce, a 'yan shekarun da suka gabata, yawancin kamfanoni ba sa ma maganar sayen wannan na'ura saboda tsadarta.

Fasahar Herta tana bukatar samun hoton mutum ne kawai sai ta kwatanta da tarin wadanda aka adana hotunansu a matattarar adanawa, kuma za ta iya gane fuskokin mutane 20 zuwa 30 a cikin taro, in ji Gary Lee, babban jami'in bunkasa harkar kasuwanci na kanfanin.

Kamfanin ya ki bayyana sunayen kamfanonin da suke amfani da fasahar tasa amma a yanzu yana jarraba fasahar ta gane fuska a kamfanonin kayan laturoni (electronics) da yawa.

Rosenkrantz na kanfanin FaceFirst ya ce, yawanci wadanda suke amfani da fasahar tasu sun hada da kantunan sayar da kayayyakin kawata gida na yi-da-kanka (DIY) da manyan kantunan sayar da kayayyaki.

Hanyoyin shiga rumbun bayanai:

Ta yaya fasahar gane fuska take aiki? Da zarar an samu hoton da ya yi daidai da na wannan barawo da ya zo kofar shagon, sai a tura wa shagon bayanan mutumin kamar hotonsa da aka dauka a lokacin karshe da aka kama shi da sauran bayanai kamar sunansa da irin laifin da ya yi da kuma inda ya yi sata a baya.

''Dukkanin wadannan bayanai za a tura su ne cikin dan kankanin lokaci ga babban jami'in shagon ko jami'in da ke kula da tsaro a shagon wanda hakan yana da muhimmanci,'' in ji Rosenkrantz.

''Misali idan akwai shaguna 500 da suke amfani da wannan fasaha kuma wani barawo ya tunkari daya daga cikinsu a Essex da ke Ingila, kuma ba ka son ka gaya wa sauran masu shagunan. Fasahar tana la'akari da wurin da abu ya shafa, saboda haka shagon da abin ya shafa kawai zai sheda wa.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu kanti suna son fasahar da za ta hana mutanen da aka san barayi ne shiga kantinsu tun kafin su shiga.

Shagunan da suke amfani da wannan fasaha ta gane fuska sai sun samu hanyar shiga rumbun adana bayanan barayin kanti da aka sani, wanda galibi ake yi da hadin gwiwar hukumar 'yan sandan yankin.

Shaguna da yawa a yanzu suna zabar tsarin fasahar da ya kunshi bayanan jama'a, insa sama da kashi daya bisa uku suka bayyana cewa a kwanan nan sun yi amfani da tsarin tsaron na gane fuskar barayi.

Suna amfani da ita ne ta wani bangare domin su kare kayansu, a wani bangaren kuma su san yawan zuwan mutane shagunan da kuma sanin wanda yake zuwa kantin.

Wannan fasaha ta gane fuska da na'urorin daukar hoto na zamani na bukatar shago ya kashe kudi sosai wajen samunsu in ji Rowen, kuma shagunan yawanci suna duba wasu karin hanyoyin na amfani da fasahar, ta yadda za su fi cin moriyarsu.

Bayan gano musu barayi, shagunan suna iya yin amfani da fasahar, wajen sanin mutumin da ya fi yi musu ciniki ko zuwa shagon sosai, su ga rukunin da za su sa shi a masu yi musu ciniki ko wane sashe mutum ya fi zuwa a kantin.

A wani bincike da muka gudanar a shekarun baya, kusan rabin kantunan da muka gana da su sun goyi bayan amfani da fasahar gane fuskar kuma kashi bakwai cikin dari ne kawai suke ganin tana yi musu kutse a abin da ya shafi sirrinsu.

Wannan shi ya taso da wata maganar, ta cewa, to ko ya kamata a kara yin abin da zai sa masu sayayya su san da fasahar da ke lura da su, wadda za ta iya bibiyarsu a lokacin da suke sayayya?

Lee na ganin wannan kari ne kawai na na'urar daukar hoto ta tsaro ta CCTV, wadda muka saba da ita daman a rayuwarmu ta yau da kullum.

Ya ce, ''idan aka yi amfani da ita ta hanyar da ta kamata domin kare su da kasuwancinsu, ina ganin hakan ba wata matsala.''

Amma ya kara da cewa mutane za su lamunta da ita ne kawai idan aikinta bai wuce ''gona da iri ba''.

Tana shiga sirrin mutane da yawa?

Sirrin mutane zai cigaba da zama muhimmin abin damuwa wurin amfani da ita. A watan Satumba na wannan shekara, hukumar kula da harkokin cikin cika ta Biritaniya ta wallafa wani rahoto, wanda a cikinsa take kara karfafa gwiwa kan yadda ya kamata a rika sanya ido da kula da bayanan jama'a, wanda ya hada da irin abin da fasahar gane fuskar za ta rika nazari.

Saboda irin wannan damuwar da ake nunawa, wasu sabbin kantuna sun yi kokarin gano hanyar kansu ta sanya ido ko bin diddigin masu musu sayayya, ba tare da sun dauki hotunansu ba, kamar na fuska.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barayin kanti sun fi satar kananan kayan aiki saboda sun fi saukin sayarwa

Netra, wanda yake a Massachusetts a Amurka, ya yi nazarin hoton bidiyon tsaro na wani kanti, inda ya fitar da wasu abubuwa a jikin kayan da kuma mai sayen kayan, wadanda za su taimaka wajen sanin abin da ya faru bayan wani abu ya faru misali bayan an yi sata ko an kai hari da sauransu.

''Muna zakulo wasu abubuwa ne a hoton bidiyon, ta yadda ba za mu keta haddin sirrin mutum ba,'' in ji Shashi Kant.

Manhajar kamfanin Netra tana gane abubuwa ne kamar launin kayan mutum da tsawon gashinsa da kuma ko yana dauke da irin jakar nan da ake goyawa a baya ko kuma jakar hannu.

''A yawancin lokaci akwai abubuwan da za a iya tantance tsakanin mutum da abin da ba mutum ba. Ba mutane ne kawai ba ake daukar hoton, hatta abin da suke dauke da shi, misali jakar da ake goye da ita ko 'yar kurar da ake zuba kaya ake turawa a cikin kanti. Dukkanin wadannan abubuwa suna da muhimmanci a hoto,'' ya ce.

Kamfanin Prism shi ma ya kirkiro kusan irin wannan na'urar, wadda take sa na'urar daukar hoto ta zama wata kafa ta tattara bayanai masu muhimmanci, da kuma binciken kwakwaf na hoton bidiyon na'urar daukar hoto ta tsaro ta CCTV na abubuwan da suka faru a kanti, kamar zirga-zirgar mutane ko daukar kaya daga kan kanta.

Shugaban ayyukan kamfanin na Prism Bob Cutt, ya kara bayani da cewa ,''mun yi amfani da tsarin da kusan a ce ya kare sirrin mutane, ba wai lalle mu ce muna bibiya ko sanya ido a kan misali wani mutum ba.

Ya ce manhaja kamar ta Prism tana aiki ne da kyau idan aka yi amfani da wasu na'urorin wadanda daman aka sanya a wuri kamar na'urar fallasa (mai kara).

''Duk wani tsari na irin wannan na'ura yana bukatar tantance hotuna,'' ya kara da cewa Kantuna suna bukatar wani abu da zai tabbatra da cewa mutumin da ya jawo na'urar fallasa ta kantin ta kama kara shi din ne ya taba kayan (da za a sata) ba wani abu ba na daban.

Iyakar aikin na'urar:

Ko na'ura ce mai daukar hoton bayanan mutum ko wasu abubuwan da ba na zahiri ba na mutum, duk da haka kantuna sun dogara ga amfani da na'urar daukar hoto, wadda ke daukar abin da ta gani.

''Kyamara tana da amfaninta a wannan fasaha,'' in ji Cutting.

FaceFirst, wanda ya ce, yana sa kyamara yadda za ta dauki hotuna a kofofin shiga maimakon a layi-layi na cikin kanti, kuma galibi tana bukatar ta tabbatar da fuskar wanda ta dauka ita ce kashi 90 cikin dari kafin ta sa na'urar fallasa ta fara kara, za a iya gyara hakan.

Wurare kamar filin jirgin sama na bukatar na'urar da za ta dauki hoton wuri mai fadi da yawa, in ji Rosenkrantz, inda na'urar za ta yi aiki da zarar abin da ta gani ya dan kusa da wanda take da bayaninsa.

Hakkin mallakar hoto Netra
Image caption Fasahar kamfanin NEtra na mayar da hankali ne kan kayan mutum kamar jakarsa da tufafinsa maimakon fuskarsa

Manhajar fasahar gane fuska na bukatar ganin fuskar mutum sosai da idonsa kafin ta gane mutum.

''Muna bukatar dan bayani,'' in ji Lee na kamfanin Herta Security. Domin mutumin da ya kauce gefen na'urar ko ya batar da kamanninsa ko da dan kadan ne shikenan na'urar ba za ta iya gano shi ba. ''Wannan gazawa ta na'urar in ji Lee.

Amma abin da ake sa rai shi ne a bunkasa aikin fasahar ta yadda za ta kara samun karbuwa a wurin wasu kantunan da wuraren da ake bukatar tsaro.

Yadda wannan fasaha take neman zama ruwan dare, za a taso da abubuwa da dama. Misali, a watan Yuni masu rajin kare sirrin mutane a Amurka sun fice daga taron tattaunawa da ma'aikatar kasuwanci kan yunkurin kirkiro sabbin dokoki na amfani da wata manhajar daukar hoton fuskar mutum.

A watan Nuwamba katafaren kamfanin sayar da kayayyaki na Amurka Walmart, ya bayyana cewa ya jarraba fasahar gane fuska a kantunansa, na tsawon 'yan watanni.

Inda ya gano cewa fasahar tana iya gano mutanen da ke da wasu take-take na sata ko kuma ma wadanda aka san barayi ne, amma kuma ba ta iya gano ma'aikatan da suke satar kayan kantin.

Kantuna za su cigaba da fafutukar samun karin tsaro da mutunta sirrin jama'a da kuma zuba jari sosai wurin samar da fasaha. Sai dai za a dauki lokaci kafin a samu daidaito kan ka'idar aiwatar da wadannan abubuwa.

Kantunan kayan kawa na mata kamar na Rotterdam, suna cike kwarin gwiwa da kyautata zaton cewa a nan gaba barayin irin kayansu a kanti ba za su samu ta yi ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Catching a thief by their face