Nawa za ka biya a kara maka shekara daya a rayuwa?

Hakkin mallakar hoto Getty

Dukkannin mu muna fafutukar kare kanmu daga mutuwa, to amma a nawa ne za mu ce aikin hakan ya yi mana tsada, ba za mu iya biya ba, mun hakura?

David Robson ya bincika mana.

Rayuwar mutum tana da matukar daraja, wadda kusan a ce wawanci ne a kwatanta ta da darajar wani kudi ko a sanya mata farashi.

Yaya za a iya kwatanta darajar tarin wasu kudade tsaba ko takardu ko gwala-gwalai da rayuwar shekara daya a duniya? Ko alama ba za a iya kwatanta darajar rayuwa ba.

To amma duk da wannan matsayi na rayuwa, wannan ita ce tambayar da masu kula da harkar lafiya a ko'ina suke yi.

Ba su da isassun kudaden da za su kashe a kan marassa lafiya da wadanda ke fama da cutar mutuwa.

Kuma duk lokacin da aka bullo da wani sabon magani, sai su auna su ga zabin da za su yi;

Shin 'yan watanni ko shekarun da maras lafiyar da zai mutu zai kara samu idan aka ba shi wannan magani sun kai darajar kudin maganin?

Ya cancanta a kashe makudan kudaden domin ya samu karin dan wannan lokaci?

Ra'ayinmu dai zai iya kasancewa, za mu yi duk abin da za mu iya domin tsawaita rayuwar mutanen da muke kauna.

Duk da wannan Dominic Wilkinson, wanda likitan marassa lafiyar da ke cikin tsananin jiyya a jami'ar Oxford ne, a kwanan nan ya rubuta wata kasida mai jan hankali, inda yake ganin shakkun amfanin maganar cewa, mutum zai yi duk abin da zai iya domin tsawaita rayuwar wani nasa da ke fama da rashin lafiyar da ba zai tashi ba.

Ya kuma bukace mu da mu sake duba wannan magana ko matsayi namu, game da nawa za mu iya kashewa domin tsawaita rayuwar wanda muke kaunar.

Bisa wannan matsayi nasa ne BBC ta nemi jin ta bakinsa domin ya fayyace lamarin da kuma neman fahimtar yadda muke kiyasin darajar rayuwa a yanzu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hanyoyin magani na fasaha sun kare mu daga mutuwa daga wasu cutukan da suka kashe kakanninmu, amma suna da tsada

A yanzu dai ana auna darajar maganin masu jinyar da ba ta tashi ba kan abubuwa biyu.

Da farko, tsawon wana lokaci maganin zai kara rayuwar maras lafiyar? Ma'ana wata ko shekara nawa zai kara a raye, sannan kuma ya ingancin lafiyar mutumin za ta kasance a wannan lokaci da ya karu?

Ana amfani da wani mizani ne (QALY) wajen auna duka wadannan abubuwa biyu.

Misali, maganin da zai taimaka maka ka samu karin rayuwar shekara daya, a rabin cikakkiyar lafiyarka, zai samu kusan rabin maki daya (0.5), a wannan ma'auni.

Haka kuma maganin da zai kara tsawon rayuwarka da wata shekara dayar, daga matsayin rabin cikakkiyar lafiya zuwa cikakkiyar lafiya shi ma zai samu wannan rabin maki, kamar yadda Wilkinson ya bayyana.

Daga wannan lissafi tsarin kula da lafiya na hukuma (ko inshora) zai auna ya ga ko maganin ya ci kudinsa wato bai yi tsada ba.

Misali, tsarin Biritaniya shi ne na shawarar kashe fan 20,000 zuwa 30,000 na karin lafiyar duk shekara daya a rayuwar mai jiyyar da ba zai warke ba, idan har aka kara matsayin tsarin inda zai shigo da maganar ingancin lafiyar da mai jiyya zai mora a karin lokacin.

Saboda haka maganin da ya kai wannan maki na rabi (0.5) a wannan ma'auni na QALY, za a saye shi ne a kan fan 10,000 zuwa 15,000.

Wannan na nufin kenan tsarin kula da lafiya na Biritaniya zai ki amincewa da wasu magungunan saboda sun yi tsada.

Misali, maganin sankarar nono wanda ake kira Kdycla, yana kara lafiyar mai jiyyar ne da kusan wata shida kawai a kan kudi fam 95,000.

Ko da da karin watanni shidan ingancin lafiyar mai jiyyar zai kai kamar na mai cikakkiyar lafiya, duk da haka kudin maganin ya zarta iyaka sosai.

Wasu masu inshorar tsarin kula da lafiyar za su iya sanya wasu ka'idojin na daban, to amma ko su ma, sai sun auna kudin maganin da kuma amfanin da zai samar, kafin su yarda su biya kudin yi wa maras lafiyar amfani da shi.

Hakkin mallakar hoto Getty

Masu rajin kare lafiyar jama'a na ganin kamata ya yi kamfanonin yin magunguna su rage farashin irin wadannan magunguna, sannan su ma masu tsarin kula da lafiya (inshora) su kara zuba jari wurin samar da magungunan da za su kara tsawon rayuwar masu cutar mutuwa.

A kan wannan muhawara kwanan nan Biritaniya ta duba yuwuwar kara yawan kudin samawa masu cutar mutuwa karin rayuwar duk shekara daya mai inganci zuwa fan 80,000 (dala 120,000).

Wilkinson ya ce gaba daya wannan abu ne da za a iya fahimta, kuma yawanci likita ne da maras lafiyar za su cimma matsaya a kan lamarin.

Ya ce, ''a matsayinmu na likitoci da muke kula da marassa lafiya, a ka'ida mu ne za mu kare matsayin mai jiyyar.

Mu tsaya kai da fata cewa lalle maganin yana da tsada amma kuma aikina na farko shi ne taimaka wa wanda nake yi wa magani.''

To amma inda matsalar take shi ne, wannan kudin za a dauke shi ne daga wasu ayyukan na kula da lafiya.

Kamar kula da lafiyar masu tabin hankali ko fannin kula da nakasassu, wanda wannan matakai ne da suke na kula da lafiyar mutanen da ke kusan farko ko tsakiyar wa'adin rayuwarsu, maimakon su wadancan da suke bakin mutuwa.

Shin ya cancanta a ce an kyale jin dadin wani domin a nema wa wani wanda yake karshen rayuwarsa karin wasu 'yan watanni na rayuwa?

Idan kana duba wannan magana, domin sanin matsayin da za ka dauka, to ya kamata ka yi la'akari da ra'ayin jama'a.

Kuma ko da ya ke za ka dauka cewa mutane da dama za su biya duk kudin da za su iya domin samun karin 'yan wasu shekaru na rayuwa, wani bincike da aka yi kwanan nan ya nuna cewa ba dukkanin mutane ne suke bayar da muhimmanci sosai ga tsawon rayuwa kawai ba.

Ma'ana wasu mutanen ba su damu da tsawon rayuwa ba, domin yawanta kawai.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wilkinson ya yi nuni ga wani cikakken binciken ra'ayin jama'a 40,000 da aka yi a Biritaniya, inda yawancin mutanen suke ganin bai dace ba a kashe kudi sosai, a kan marassa lafiyar da ke fama da cutar mutuwa, maimakon wadanda suke da wata rashin lafiya, wadanda ke da sauran rayuwa a gabansu.

Watakila abin da zai fi ban mamaki a nan shi ne, sakamakon wani bincike da aka yi a Singapore, inda aka tambayi tsofaffi amma masu lafiya, da sauran 'yan kasa da kuma wadanda suke fama da cutar sankara da ba za su warke ba.

Wilkinson ya ce, ''abin mamakin shi ne, mutanen sun ce, za su iya biyan makudan kudade domin a rika ba su kulawar rage radadin cutar a gidajensu, maimakon su sayi wani magani da zai tsawaita rayuwarsu.''

Yawancin mutanen da aka tambaya za su biya fan 5,000 (dala 7,500) domin yi musu maganin da zai kara kwanakinsu da kusan shekara daya.

Amma kuma suka ce za su iya biyan kusan linki biyun wannan kudi wato fan 10,000 (dala 15,000), domin a kula da su da kyau, ta yadda za su mutu a gidansu, maimakon asibiti.

''Ga alama wannan ya bude wani sabon babi na tunani a game da yanke wani hukunci mai wuya,'' in ji Wilkinson.

Hakkin mallakar hoto Getty

A bayyane take wadannan nazarce-nazarce ba su ne amsar karshe ta wannan lamari ba.

Abu ne mai wuya a san cewa ko wannan shi ne ra'ayin sauran mutane a sauran wurare, wadanda kuma suke da wasu matsalolin na jiyya.

Akwai kuma maganar yadda za a yi amfani da ma'aunin duba tasirin maganin da za a yi wa mutum, bisa gaskiya, ba tare da sanya wani ra'ayi ba.

Amma Wilkinson yana ganin duk wani abu da za a yi shi ne, ya kasance akalla, mun duba muhimmancin ingancin karin rayuwar da za a samawa maras lafiyar, wanda ke fama da cutar mutuwa, kafin kashe makudan kudade wurin neman tsawaita wa'adinsa.

''Ko da ya ke abu ne na zahiri sanin yadda ake son saya wa mai cutar da ke jiran mutuwa magani mai tsada, amma ba na jin wannan shi ne ra'ayin dukkanin mutane, ko kuma ma na marassa lafiyar, in ji likitan, wanda ya kara da cewa, ''ba na kuma jin wannan shi ne abin da ya kamata a ka'idar aiki.''

Yayin da al'umma ke tsufa, harkar kula da lafiya kuma ke kara ci gaba da bunkasa da kara tsada, wadannan batutuwa za su ci gaba da damun jama'a.

Fitaccen likitan nan na Amurka Atul Guwande da dadewa, ya dora ayar tambaya kan maganar kara tsawon rayuwa, maimakon kara dadin 'yan shekarun da muke da su.

Ezekiel Emanuel tsohon darakta a hukumar kula da lafiya ta Amurka, National Institutes of Health, ya taba cewa, zai ki duk wani shiri na tsawaita rayuwarsa idan ya kai shekara 75, maimakon ya shiga wani yanayi na tsananta yi masa magani akai akai ya yi 'yan sauran shekarun da suka rage masa.

Kadan ne daga cikinmu za su iya daukar wannan mataki mai tsauri, amma abu ne mai muhimmanci ga kowa, ko nawa ne shekarunka, ka yi la'akari da muhimmancin lokacinka a duniya, da kuma abin da za mu yi mu morewa rayuwar sosai.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan How much would you pay to live for an extra year?