Yadda gumi ke bayyana halin da muke ciki

Hakkin mallakar hoto Getty

Muna sane da cewa gumi na fita daga jikinmu ne lokacin da muka ji zafi, ko tashin hankali ko wulakanta. Ba a san cewa jibin da ke fito mana na nuni ne da irin damuwar da muke ciki ba.

Ga bayanin nazarin Jason G Goldman

A shekarar 1934, wani likitan Birtaniya, mai suna BA McSwiney ya yi jawabi a gaban abokan aikinsa, wajen taron kungiyar likitoci ta Biritaniya, inda ya nuna takaicinsa ganin yadda mafi yawan mutane ba su damu da sinadaran da ke kunshe a cikin guminsu ba.

Maimakon haka ma sun fi mayar da hankali game da yanayin da zufa ke fita daga fata, ta sa jiki ya sanyaya kansa.

Sai dai McSwiney na sane da cewa akwai wasu al'amura tattare da gumi fiye da yadda yake sanya jiki ya sanyaya idan ya bi iska.

A wani yanayi,ta yiwu a lura da cewa a kan yi asarar sinadaran da ke damfare a cikin jini, ta hanyar yin zufa da yawa akai-akai.

A iya cewa wasu muhimman abubuwa na fita daga jiki sanadiyyar fitar guminmu. Amma wane irin abu ne muke asara, mai amfani ne ko maras amfani ne?

Wasu sinadaran da ke cikin guminmu ta yiwu babu bukatar zubar da su. Dauki misalin sinadarin Kuloraid (chloride).

Wannan sinadari yana gauraya da na sodiyom ( sodium), su samar da gishiri, wanda yake da muhimmanci wajen daidaita karfin ruwan sinadaran kwayoyin halittarmu ta yadda wani ba zai rinjaya ba ya cutar da jikinmu.

Harwayau dai gishin ne kuma yake daidaita shige da ficen yawan ruwan cikin kwayoyin halittarmu.

Sannan kuma gishirin ne dai ya ke mika sako tsakanin jijiyoyin jikinmu.

Daidai ne idan sinadarin kulorin (chlorine) ya fita daga jiki, lokacin da muke zufa amma fa akwai wasu lokutan da mutum zai iya zubar da sinadarin da yawa.

Dauki misalin lokacin da kake aiki na tsawon sa'o'i a wuri mai zafi. Mafi yawanmu mun san cewa shan ruwa na taimaka wa jiki ya kasance da ruwa.

To amma fa idan ya kasance kana zufa da yawa kuma kana shan ruwa da yawa, to yanzu ne fa alamar gubar ruwa za ta bayyana a jikinka.

A wannan yanayi jikinka ba zai iya maye gurbin sinadarin kuloraid (chloride) da jikin yake rasawa ta zufa da sauri ba.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Zufarka na dauke da 'yan sinadaran karafuna (zinc da magnesium)

Wani sinadarin da shi ma yake gauraye a zufa shi ne Yuriya (Urea) , wanda daga shi ne aka samu sunan fitsari na Ingilishi ''urine''.

An yi kiyasin akalla tsakanin miligiram 0.24 da 1.12 na sinadarin yana narkewa a cikin wani dan kalilan na yawan gumi.

Duk da ana jin cewa ba shi da yawa, amma idan aka yi la'akari da cewa mutum kan yi zufa ta wani adadi a kullum (kimanin rubi uku na santimita 600 zuwa 700) a kowace rana, gumi ne sanadin zubar kashi bakwai cikin 100 na sinadarin yuriya.

Sannan akwai sinadaran amoniya (ammonia) da nau'ukan abinci mai gina jiki da sukari da kanwa da burbushin nau'ukan karafa iri-iri. Wasu daga cikin wadannan sinadaran karafa zufa ce ke taimaka wa wajen fitar da su daga cikin jiki

Ba dukkanin abubuwan da ke fita daga jikinmu ta zufa ba ne za a ce suna da yanayi na guba.

Zufa na fita daga jiki ne ta kafofin kwayoyin halitta biyu. Akwai "Apocrine gland" da ake samu a karkashin hammata da hanci da kan nono da kunnuwa da wasu sassa na al'aura.

Mafi yawan abin da yake sananne, su ne kafar kwayar haitta ta eccrine glands, inda miliyoyin kwayar suke kusan yawancin sassan jikin mutum, kusan a ko'ina suna nan in banda lebe da wurin al'aura.

Idan jiki ya yi zafi, masu amsar zafin na tura shi a matsayin sako da ke kaiwa zuwa ga kwakwalwa.

A can ne kafar hypothalamus, wata kafa da ke dauke da curarrun kwayoyin halitta ke kula da jin yunwa da kishirwa da barci da zafin jiki, sannan ta aike da sako zuwa ga kafofin apocrine da eccrine gland, wadanda daga nan sai su fara turo gumi waje.

Akwai kuma wata kafar ta uku ta kwayoyin halittar na gumi, wadda aka fara ganowa a 1987.

Ana kwayoyin halittar ne a wurin da na apocrine suke kawai, amma saboda masu bincike ba su iya cewa ita ma apocrine ce ko eccrine ba sai suka ba ta suna na gamayya apoeccrine.

Wasu masu binciken suna ganin ai ita ma kwayar ta eccrine ce amma take juyewa a lokacin balagar mutum.

Gumi a matsayin abin sadarwa.

Ba dukkanin abubuwan da suke fita daga jikinmu ba ne suke dauke da cukaden sinadarai.

Kowane mutum ya fara zuwa ne a wani lokaci bayan ya ci wani abu mai barkono, kuma mutane da yawa sun san yadda mutum ke zufa idan ya samu kansa a wani hali kamar na tsoro ko abin kunya ko zafi ko damuwa.

Ba mamaki ashe mutum yake gumi a tafin hannu da na kafarsa da kuma goshinsa a yawancin lokaci idan ya samu kansa a ire-iren wadancan yanayi na baya da muka ambata.

Wannan yana faruwa ne domin wadannan wuraren suna dauke da tarin kafofin kwayoyin halittar gumi na eccrine.

An gano cewa gumin da mutum ya yi saboda wani hali da ya shiga na daga irin abubuwan da muka ambata a sama muhimmin abu ne na sadarwa.

Hasali ma kanshi ko warin da muke ji na zufar ka iya bayyana mana abubuwa da dama kan yadda mutumin ke ji a wannan hali da ya shiga.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wari ko kanshin zufar mutanen da ke wani yanayi na iya tasiri a kan halayyar wasu mutanen

A wani gwaji an tattara samfur na gumin mutane goma yayin da suke kallon wani bidiyo da aka tsara da zai sa su ji tsoro ko damuwa.

Domin ganin gumin bai gurbata da wani sinadari na wani abu daban ba, mutanen sun kaurace wa kayan abinci masu kanshi ko wari da barasa da taba, da kuma dakatar da motsa jikida yawa har tsawon kwana biyu kafin su bayar da gumin.

Daga nan kuma sai aka sa wasu mata 36 da su duba ruwan zufar ko za su ga wata alama ta wata damuwa, inda suke shinshinawa.

Masu nazarin sun gano cewa, idan aka ba wa matan zufar wanda ya ji tsoro, fuskarsu su ma sai ta nuna alamun tsoro.

Kuma idan aka ba su zufar wanda ransa ya baci sai su ma a ga alamar bacin ran a fuskarsa.

Wannan ya nuna wa masu binciken cewa gumi wani abu ne mai sadarwa sosai tsakanin mutane.

Wani muhimmin abu kuma shi ne, yanayin sauyin fuskar da matan suka nuna a lokacin da suka shinshina ruwan gumin ko alama ba shi da wata alaka da yadda matan suke ji da tsananin wari ko kanshi.

Wato kenan za su iya nuna wannan yanayi na bacin rai a fuskar ko da kuwa sun bayyana wani sanfurin na zuwa da cewa kanshinsa na da dadi.

A wani gwaji da aka yi a shekara ta 2006 ma a jami'ar Rice an ga irin wannan sakamako.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Zufar mai wasan fadowa daga jirgin sama a karon farko na dauke da sinadarai masu karfi na nuna alamun tsoronsa

Kuma a shekara ta 2012 masana tunanin dan adama da likitocin masu tabin hankali ko kwakwalwa a jami'ar jihar New York sun debi gumi daga rigunan wasu mutane 64.

Rabin mutanen da suka bayar da gumin rigunan nasu sun fado cikin iska daga jirgin sama ne a karon farko a rayuwarsu, yayin da sauran rabin kuwa sun rika motsa jiki ne sosai.

Wadanda suka shinshina rigunan mutanen da suka yi wasan fadowa daga jirgin saman an ga alamun sun farga da suka ga fuskokin mutanen da ransu ya baci.

Kuma hatta fuskokin mutanen da ba su nuna wata alama ba da ma wadanda ba za ka iya cewa ga yadda suke ba ma, mutanen sun farga da suka gansu.

Masana tunanin dan adam din sun bayyana hakan a matsayin lura, warin wannan zufa ta masu wasan fadowa daga jirgin saman ya sa mutanen su sanya ido sosai a kan duk wani abu wanda idan ba don sun shinshina zufar ba da ba ma za su lura da shi ba.

Su kuwa wadanda suka shinshina zufar wadanda suka motsa jikin nasu sun farga ne a lokacin da suka ga fuskokin mutanen da ransu ya baci, kamar yadda lamarin zai iya kasancewa a yanayi na yau da kullum.

Wani gwajin kuma da wani masanin tunanin dan adam dan kasar Jamus ya gudanar ya gano cewa zufar mutanen da suka damu, (wadanda suka shiga wani wasa na tafiya a kan igiya da aka daura a can sama) ta sa mata su yanke hukunci mai hadari, bayan sun dauki lokaci suna tattauanawa kan matsayin da za su dauka, a kan wani wasan kwanfuta da aka tsara domin tantance dabi'ar mutum ta kasada.

Babu wani daga cikin duk wadannan nazari da ya nuna cewa mutanen sun san warin wani gumi ya shafi matsayin da suka dauka ko dabi'ar da suka nuna. Amma sun nuna alamun cewa a wani lokaci warin gumi zai iya bayyana yanayin halin da hankalimmu ke ciki (mental state).

Ya kuma nuna cewa muna amfani da bayanin da ke cikin gumin mutane mu kara fahimtar muhallinmu da kyau.

Watakila wanna ba abin mamaki ba ne. Jinsinmu na adam kila ya saba ne da sadarwa ta magana da yare, to amma shi yare ai sabon abu ne a tsarinmu na zamantakewa da mu'amulla da juna (a da babu shi kenan )

Binciken ya nuna ga alama kakanninmu na zamanin da can sun yi amfani da jin kanshi ko wari (hanci) wurin sadarwa, kuma muma muka gaji hakan daga wurinsu.

Hakkin mallakar hoto Getty

Ba shakka mutane sun fi gane yanayin da mutum yake a kwamfuta idan hotunan mutanen wasan ko wani bidiyo da ake nunawa suna gumi.

Kuma ba haka kadai ba, domin kara alamar shi wannan gumi da hoton yake yi a bidiyo kan sa mutane fahimtar tsananin halin da ake so a nuna shi mutumin na bidiyo yake ciki.

Saboda haka gumi ba hanya da ake sanin abu ba ta hanci kadai hatta ta ido ma ana fahimtar abu daga gare shi.

A karshe, gumi ba tsarin sanyaya jiki ba ne kawai, zai iya kasancewa kamar wata na'urar sani ko hasashen yanayin mutum, wadda muke amfani da ita wajen fadakar da abokai da iyalanmu abin da muke ji a birnin zuciyarmu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan What our perspiration reveals about us