Kare yana kama da mai shi - shakka babu

Hakkin mallakar hoto Gerrard Gethings

Kare yana bayyana wani yanayi na yadda muke kula da kaunar kanmu, wanda hakan wata dabi'a ce wadda kuma watakila ma ita take tsara yadda kake soyayya.

Ga binciken na David Robson.

Ka je duk wani dandali za ka ga abin mamaki game da karnuka. Watakila mutumin da za ka gani irin masu sanya tufafi na gayu ne wadanda suka sha bamban da na sauran jama'a, kuma ga shi da gemu, yana rike da buzun karensa (mai gashi buzu-buzu) yana binsa zagwai-zagwai kai ka ce maiaskinsu daya.

Ko ka ga wani matashi dan bana-bakwai yana rike da jibgegen karensa. Ko kuma ma ka ga mai wata mata ce mai motsa jiki tana sassarfa dan karenta irin jinsin karnukan Afghanistan yana bin ta a baya, iska na kada gashinsu.

To me ya sa ne mutane suke zabar karnukan da yawanci suka yi kama da su?

Ko alama amsar wannan tambaya ba shaci fadi ba ce, amsa ce da za ta iya bayyana maka irin tsananin shakuwa da alakar da mutane ke yi da karnukansu.

Abin mamaki kuma shi ne akwai bambanci tsakanin wannan da kuma yadda muke zabar mata ko mazajenmu na aure.

Hakkin mallakar hoto Gerrard Gethings

Micheal Roy na jami'ar California da ke San Diego shi ne masanin tunanin dan adam na farko da ya fara jarraba wannan bincike.

Ya je wasu dandali-dandali ne guda uku inda masu karnuka suka taru, ya dauki hotunan karnukan sannan kuma ya dauki na masu su daban-daban, sanna ya sa wasu mutane daban su hada kowane hoton kare da hoton mutumin da ya yi kama.

Mutanen kusan sun yi nasarar hada kowane kare da mai shi daidai. Tun daga sannan an sake jarraba wannan gwaji sau da yawa.

Duk da cewa kamannin kadan ne to amma ana ganinsa, amma kuma fa ba kowane mai irin insin karen nan mai dukunkunanniyar fuska ba ne (bulldog) za ka ga fuskarsa kamar shi ma kamar wadda aka dukunkuna.

Yawanci ana ganin kamannin ne a tsakanin karnukan da aka hada jinsinsu ( ba na jinsi daya ba), kuma wani lokacin za ka ga kamanni ne na fisha kawai.

Za ka ga mata masu gashi dogo sun fi son karnuka masu dogayen kunnuwa, kuma mutane masu girma ko teba za ka ga sun fi son karnuka masu kiba.

Haka kuma wannan kamanni yana kara bayyana a siffar idanuwa tsakanin kare da mai shi.

A lokacin da aka rufe idanuwan mutanen da na karnukan a hotunan, mutanen sun sha wahalar iya gane kamannin.

Hakkin mallakar hoto Gerrard Gethings

Watakila duka wannan na da dangataka ne da sabo, domin kila kare zai fi kwanta wa mutum a rai idan ya yi kama da wani daga cikin iyalinsa ko danginsa, wanda ya sani kuma yake kauna.

Wasu masana tunanin dan adam kuwa sun yi amanna cewa abu ne da ya samo asali daga yadda muke zabar mutanen da za mu aura, domin kulla kauna da wanda ko wadda kuka yi kama abu ne da ke tabbatar da cewa kwayoyin halittarmu sun dace da juna.

A saboda wannan dabi'ar kenan zai iya kasancewa mun fi son kusan duk abin ya dan yi kama da mu.

A bisa wannan dalili ne za ka ga hatta a fannin mota, mutane sun fi zabar wadda ta fi dacewa da kamanninsu, misali mutumin da yake da mukamuki mai dan fadi ya fi son motar da take da kumatu mai dan girma.

Bisa hakan idan ka duba za ka ga motarsu ta yi kama da karnukansu.

Hakkin mallakar hoto Gerrard Gethings

Wani abu kuma shi ne kaunarmu ba kara ma ba ce, domin ba mutanen da suka yi kama da mu kawai muke so ba, mukan yi la'akari da wadanda suke da halaye kamar mu kuma.

Kamannin halaye kan iya bayar da hanyar hasashen gamsuwar ma'aurata da junansu.

A 'yan shekarun da suka gabata Borbala Turcsan ta jami'ar Eotvos da ke Budapest ta ga ya dace ta yi bincike ko haka abin yake a alakar mutane da karnukansu ma.

Ta ce, '' dangantakar mutum da kare ta musamman ce, ba wai kawai sha'awa ba ce a tsakaninsu, kare kusan da ne, ko aboki ko kuma dan uwa ma, mun dauka cewa dantakar za ta saba da sauran dangantakar.''

Wasu za su iya cewa ta yaya za a iya sanin yanayin halin kare kamar yadda za a iya kwatanta wa da halin mutum, to amma a nan, wadansu nazarce-nazarce da aka yi a baya sun nuna yadda za a iya sanin hakan.

Za a iya fahimta daga kare yake ko ba ya saurara wa baki ko yana da kunya, inda a yawancin lokaci yake zama a bayan kafar mai shi.

Hatta tsarin tambayoyin (big Five questionaire) da ake yi wajen sanin hali da yanayin mutum, akwai irin wannan tsari na tambayoyi na kare, wanda na karen ya danganci dabi'unsa ne kamar lalaci ko saukin kai.

Hakkin mallakar hoto Gerrard Gethings

Turcsan ta gano cewa karnuka da masu su suna da kamaceceniya ta halayya.

Ta ce, ''abin da muka gano ya wuce ma kamannin da ke tsakanin ma'aurata da abokai.''

Ba za a iya bayyana dangantakar daga tsawon lokacin da karen ya yi tare da mai shi ba, saboda haka ba wai karen ya kwaikwayi irin wadannan halaye ba ne daga mai shi ba.

Maimakon haka sai dai a ce wadannan halaye na karen na daga cikin abubuwan da suka ja hankalin mai karen har ya saye shi ko ya mallake shi.

Kuma zaman mutum da karensa yawanci ya fi karko da lokacin da yawancin aure kan kai tsakanin ma'aurata.

Abin mamaki neka yi tunanin yadda wannan dangantaka ta samo asali tun da farko.

Shi dai mutum ya fara amfani da kare ne a gida (daga daji) kusan shekara dubu 30 da ta wuce domin ya taimaka masa a farauta, amma a hanakali sai muka sauya yanayinsu ya zama yadda ya dace ko kama da mu.

Wanda kuma daga haka muka kulla kauna ta kut da kut da shi, wadda har ta zarta yadda iyakar jinsinmu da su take.

A yausun yi kama da mu, suna abu kamar yadda muke yi, kuma ba kamar sauran mutane ba, a ko da yaushe suna damuwa da halin da muke ciki.

Ta hanyoyi da dama su ne wadanda za a iya cewa ke bayyana ainahin irin yanayin mutum.

Ba mamaki daman yadda a yau mutum ya dauke kare a matsayin babban abokinsa

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Dogs look like their owners - it's a scientific fact