Ana iya hasashen jinsin jariri daga girman ciki?

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Akwai hanyoyi da yawa da a wasu al'adun aka yi imani da su wajen hasashen abin da mai juna biyu ke dauke da shi, namiji ko mace.

Hanyoyin sun hada da yanayin girman ciki ko nakuda mai wuya ko lila zobe a kan ciki ( a kulla zobe a zare ana reto da shi a kan ciki).

Dukkanin wadannan hanyoyi ne na hasashen abin da mace mai ciki za ta haifa. Sai dai daya ne tak daga cikinsu yake tabbata.

ClaudiaHammond ta mana nazari a kan wannan al'ada

Idan cikin mai juna biyu ya burtso gaba kamar kwallo (bal), namiji ne. Idan girma ko nauyin abin da ke cikin nata ya kasance a kewayen cikinta ne mace ce. Haka wasu mutanen ke cewa kuma haka suka yadda da shi a bisa al'adarsu.

Kamar yadda kowace uwa za ta gaya ma ba ta san iyakar yawan dangi ko kawayen da suka gaya mata hanyoyin tantance jinsin abin da take dauke da shi yayin da take da juna biyu.

Hatta mutanen da ba mai juna biyu ma ba ta sani ba sukan tsayar da ita a hanya, su ce mata ga jinsin abin da za ta haifa bisa la'akari da yanayin girma ko siffar cikinta.

To sai dai kuma abin fa ba haka yake da sauki ba kamar yadda ake dauka.

Abubuwa biyu ne ke jawo yanayin girma ko siffar juna biyun mace. Na farko shi ne girman jaririn da ke cikin nata.

Gaskiya ne yawanci jariri namiji ya fi mace girma a lokacin haihuwa, wanda hakan zai iya sa cikin ya dan fi girma idan namiji take dauke da shi.

Amma kuma wannan dan bambancin nauyi ko girman ba lalle ba ne ya sauya siffar girman cikin.

Na biyu kuma shi ne wurin da dan jaririn yake zaune a cikin uwa. Idan bayansa yana fuskantar gaban uwar ne, sai ya sa cikin ya burtso waje.

Idan kuma fuskarsa na kallon gaban mahaifiyar ne, to sai cikinta ya zama kamar shafaffe.

Kuma wannan yanayi na zaman jaririn a cikin uwa ba ya dogara ba ne ga jinsinsa, na namiji ko mace ba, saboda haka shaci-fadi ne ko kuma al'mara a ce yanayin girman ciki na nuna cewa namiji ne ko mace mai ciki take dauke da shi.

Dadaddiyar al'ada.

To idan ba za ka iya hasashen jinsin abin da mai juna biyu take dauke da shi ba, daga alamar siffar girman cikinta, to ina maganar sauran maganganu na al'ada kuma?

Lila zobe (na ma'aurata) a saman cikin mai juna biyu domin ganin inda zai rika reto a jikin zare, wannan ma ba zai nuna jinsin abin da ke cikin ba, saboda jaririn da ke ciki ai ba ta yadda zai san da wani abu da ke reto daga waje.

Haka kuma ba ta yadda za a ce irin abincin da uwa take sha'awa na iya nuna jinsin abin da take dauke da shi a cikinta.

To amma ya maganar cewa uwa ta fi laulayi da safe idan mace take dauke da ita?

Yadda aka dauki abin shi ne, idan uwa tana dauke da mace ne, to sai ya kasance tana samun linki biyu na sinadarin kwayoyin halitta na mace, wannan kuma sai ya sa ta rika rashin lafiya. Wannan ma dai al'mara ce.

Magana ce kawai, domin yawancin laulayin safe na faruwa ne a lokacin makonni 12 na farko, yayin da dantayi yake karami kuma a wannan lokacin kwayoyin halitta na jinsin mace ko namiji 'yan kadan ne.

Hanyoyin sanin jinsin abin da mai juna biyu take dauke da shi, sun hada da daukar hoton asibiti na cikin uwa da gwajin ruwan da ke cikin mahaifa a mako na 15 zuwa 20 ko kuma gwajin kwayoyin halittar da aka debo daga cibiyar jariri.

Hanyoyi biyu na gaba da muka ambata, ana amfani da su ne domin tantance jinsin idan akwai wata matsala da ta shafi jinsi a tattare da dantayin.

Hanya daya da aka fi amfani da ita, ita ce ta daukar hoton asibiti na cikin, amma kuma yawancin asibitoci suna da tsari na kin gaya wa iyaye jinsin jaririnsu.

Amma kuma akwai wata hanya daya da za ka iya sanin jinsin jariri, amma kuma sai kusan a lokacin da aski ya zo gaba goshi.

Wannan hanya ita ce, cewa a tsawon shekaru da dama ungozomomi sukan yi barkwancin cewa idan nakuda ta dauki dogon lokaci kuma ''ta zo da tsanani, to lalle namiji ne ba shakka''.

Akwai alamun gaskiya a wannan magana, domin wani bincike da aka yi a Ireland wanda aka wallafa a mujallar harkokin lafiya ta Biritaniya (British Medical Journal), ya yi nazarin haihuwa dubu takwas a wani asibiti a Dublin tsakanin 1997 da 2000.

Masu nazarin sun gano cewa yawanci idan haihuwa ta jariri namiji ce ta fi dadewa, kuma ta kan zo da matsaloli da ka iya sa a yi tiyata wajen fitar da jariri (CS).

To nan gaba idan mace ta samu kanta cikin nakuda mai tsawo da tsanani, to watakila, watakila fa na kara nanatawa, namiji za ta haifa.

A fa tuna cewa wannan bincike ne da ya nuna yawanci haka abin yake kasancewa amma ba lalle haka yake a ko da yaushe ba, kuma akwai haife-haifen da aka yi na jarirai mata da su ma suka kasance da irin wadannan matsaloli.

Kuma da zarar nakudar ta zo karshe za ku san jinsin jaririnku.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Can you predict a baby's sex from the size of the bump?