Mutum, asali na kirki ne ko na banza?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

A zahirin gaskiya a iya cewa mutane masu kirki ne ko mugaye ne? Wannan tambaya ce da aka dade ana yi a tarihin rayuwar dan adam.

Tsawon dubban shekaru, masana falsafa sun yi muhawara, ko tun ainahi mu mutane halayenmu masu kyau ne amma yanayin zamantakewa a cikin al'umma ya sa muka sauya ko kuma dama tun asali ba mu da kirki al'umma ce ke daidaita mu, mu zama kamar na gari.

Ilimin tunanin dan adam ya gano wasu shedu da ka iya sauya wannan dadaddiya kuma tsohuwar muhawara.

Hanya daya ta binciken ainahin dabi'unmu na asali ita ce ta lura da yadda jarirai ko 'yan kananan yara su ke.

Zuciya ko yanayin 'yan kananan yara (jarirai) babban abin lura ne, ko mudubi na sanin yadda dan adam ya ke ainahinsa daga halitta.

Jarirai mutane ne da kusan babu wani gauraye ko tasiri da al'ada ta yi a kansu.

Misali ba su da abokai da yawa, ba su je makaranta ba sannan kuma ba su karanta kowane littafi ba.

Ba ma sa iya furta bakaken zancensu da kyau ballantana a ce ma suna magana, saboda zuciyarsu tsarkakakka ce matuka, kamar yadda duk wani dan adam zai iya kasance wa maras laifi.

Matsala daya kawai ita ce, rashin yaren da jariran ke ji shi ya sa da wuya ko ma a ce ba ta yadda za a iya sanin ra'ayinsu.

A ka'ida mu kan sa mutane su shiga wani tsari na nazari ko gwaji, mu ba su ka'idoji ko mu yi musu tambayoyi, wadanda dukkanin wadannan hanyoyi na bukatar mutum ya kasance yana da yare ko harshe da zai amsa.

Jarirai za su iya fin dacewa a yi wannan bincike da su, amma kuma ba a san su da bin umarni ba.

To yaya masanin tunanin dan adam mai son sani ko ganin kwakwaf zai yi kenan?

To dadin abin shi ne ba lalle sai ka iya magana ba za ka iya bayyana ra'ayinka.

'Yan kananan yara za su iya kai hannunsu wurin abin da su ke so, kuma sukan dade suna kallon abin da ya ba su mamaki.

An yi amfani da wasu hanyoyi a jami'ar Yale da ke Amurka ta bin wadannan matakai domin duba tunani da zuciyar yara.

Sakamakon da a ke ganin an samu shi ne cewa hatta shi dan karamin mutum (jariri) ya san abin da ya ke daidai da kuma wanda ya ke ba daidai ba.

Bayan wannan kuma yana da tunanin da zai iya karkatar da shi ya zabi alheri a kan sharri.

Ta yaya binciken zai iya nuna haka? Ka dauka kai dan mitsitsin yaro ne. Tun da yanayin sanya hankalinka a kan abu (attention span) gajere ne, hanyar gwajin za ta zama gajera, kuma za ta kunshi abubuwan ban sha'awa, ba kamar yawancin hanyoyin gwaji na tunanin dan adam ba.

A takaice dai kamar irin wasannan ne na 'yar tsana ko wata siffa da a ke ratayewa da zare ana sarrafa motsinta daga sama ko wani wuri daga bayanta.

Yadda aka tsara aikin gwajin shi ne, wuri ne da ke da wani tsauni mai launin kore mai haske, su kuma siffofin abubuwan da aka kirkira an yi su ne da 'yan sanduna, kuma idanuwan da ke ganinsu yana rawa ne.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Su abubuwan (siffofin) da aka yi da 'yan sandunan, alwatika ne (triangle), da murabba'i (square) da kuma kawanya ko da'ira (circle), dukkanninsu kuma kowanne da irin hasken launinsa daban.

Daga nan kuma sai aka shirya wani dan wasa na takaitaccen lokaci, inda daya daga cikin wadannan abubuwa uku da aka yi (misali kawanyar) ke kokarin hawa wannan tsauni ta fadi ta tashi ta ci gaba da kokarin hawa.

Daga nan kuma sai sauran abubuwan biyu su ma suka fara aiki (motsi kamar mutane, idan ba a manta ba mun ce ana motsa su ne da zare ko wani abu ta yadda ba kowa ke ganin yadda ake motsa su ba).

Daya cikinsu yana kokarin taimaka wa wannan da'ira ta hau tsaunin, dayan kuwa ya shiga gabanta yana dawo da ita, wato ya hana ta hawa.

To a nan dai wani abin ban sha'awa a fannin tunanin dan adam tuni yana faruwa daga bayanin da nayi na wannan gwagwarmaya da taimako da kuma hana taimakon, tsakanin abubuwan uku, kuma kowanne dan adam ya iya fassara abin da labarin ya kunsa.

Su wadannan abubuwa uku da ake motsawa (kamar rakumi da akala) siffofi ne kawai. Ba sa magana kamar mutum ko nuna wani yanayi na damuwa kamar yadda mutum ke yi idan wani abu ya same shi.

Suna dai motsi ne kawai, amma kuma duk da haka kowa ya san manufar motsin da su ke yi ( daya na son hawa tsauni, daya na taimakonsa ya hau, daya kuma ya hana hawan), da kuma halin kowannensu.

Za ka iya cewa wannan nazari na zuciya ko halayyar abubuwan, hatta a wurin jarirai ko yara 'yan kanana, na nuna cewa wani yanayi ne na mutum ya yarda da yadda zuciyar wasu ta ke, na daga halayyarsu da ta bayyana.

Zakuwa ko sa rai

Abin da ya faru a gaba kuma zai nuna mana karin ilimi game da yanayin dan adam. Bayan wasan sai aka ba wa 'yan kananan yaran damar su je wurin abubuwan biyu, wanda ya yi taimakon a hau tsaunin ko kuma wanda ya hana hawan.

Abin da ya faru shi ne 'yan yaran sun fi karkata zuwa wurin mai taimakon. Wannan ya nuna wa yaran cewa shi mai taimakon yana da kirki, yayin da shi kuwa mai hana hawan ba shi da kirki.

Masu binciken sun yi amfani da maimaicin gwajin wajen tabbatar da sakamakonsa cewa gaskiya ne, haka abin ya ke.

'Yan kananan yaran sun kuma kalli wasa na biyu, wanda shi kuwa a nan, wannan siffa mai kokarin hawa tsauni ta ke da damar zuwa wurin wadda ta hana ta hawa tsaunin ko kuma mai kokarin taimakonta ta hau (domin nuna godiya).

Lokacin da 'yan yaran suka dauka na kallon dukkanin nunin abubuwan da suka faru biyu, ya nuna yadda suke tunanin abin da zai iya faruwa ko zai kasance.

Da mai kokarin hawa tsaunin ta tafi wurin abin da ya kare, ya hana ta hawa tsaunin sai yaran su ka zura ido suka dade suna kallo fiye da idan ta tafi wajen siffar da ta taimake ta ta hau.

Wannan ya nuna cewa yaran sun yi mamaki kenan yadda mai kokarin hawa tsaunin ta tafi wurin wanda ya hana ta hawa.

Zuwa wurin mai taimakon shi ne abin da ya kamata, kuma shi ne abin da yaran suke tsammani ya faru.

Saboda haka tafiya wurin wanda ya hana taimako abin mamaki ne, kamar yadda ni da kai za mu yi mamaki, mu ga yadda wani zai je ya rungumi mutumin da ya hana shi cigaba a rayuwa.

Yadda za mu fahimci wannan sakamako, shi ne idan 'yan kananan yara, da ba a jirkita musu kwakwalwa da wata al'ada ba, su ke tsammanin yadda ya kamata mutane su yi abin da ya dace.

Ba kawai sun fassara motsin da wadannan abubuwa su ke yi ba a matsayin wani abu na kwarin gwiwa ko kokari ba kadai, sun ma nuna cewa sun fi kaunar taimakon kara karfin gwiwa maimakon wanda zai hana cigaba.

Wannan ba wai ya kawo karshen muhawara a kan hali ko yanayin dan adam ba kenan.

Mutumin da ke da ja a kan wannan lamarin zai ce ai wannan ba wani abu ba ne illa kawai ya nuna cewa 'yan kananan yara suna da wannan ra'ayi ne kawai kuma ana tsammanin a ga sauran mutane ma sun bi ra'ayin.

Akalla, ko ba komai wannan ya nuna can a cikin zuciyar dan adam tun yana dan karaminsa akwai damar fahimtar yadda duniya ta ke a fannin kwarin gwiwa, da kuma son abin da ya ke na alheri a kan mai cutarwa.

Wannan kuwa shi ne harsashin da rayuwa mai kyau, ta sanin ya kamata, ta dan adam ta ginu a kai.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na Are we naturally good or bad?