Abincin mutum nawa mai ciki za ta ci?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

A bisa al'ada za ka ji ana cewa mace za ta iya cin abinci mai tarin yawa idan tana da juna-biyu, amma kuma bayanai na nuna akasin bukatar yin hakan.

Claudia Hammond ta yi nazari

Duk matar da ta taba samun juna-biyu za ta gaya maka yadda kawaye ko danginta suke tura mata abinci akai-akai ba kakkautawa, suna ce mata: ''Ki ci fa! Mutum biyu yanzu ki ke ci wa!''

Matan da suka dade suna damuwa kan kibarsu galibi sukan samu kwanciyar hankali a karshe saboda cewa, yanzu hankalinsu ya kwanta ba su da wata fargaba game da abin da su ke ci.

A da dai suna cewa abu ne da aka yarda da shi... To anya kuwa abu ne mai amfani da kyau ga jariri idan kika ci abinci da yawa?

Wannan al'ada ta yarda da cewa cin abinci da yawa na mutum biyu ta samo asali ne daga yadda kusan kashi uku na mata da suke kara kiba ana ganin hakan a likitance kibar ta yi yawa matuka.

Wannan kiba dai ba kawai tana wuyar zubewa ba bayan mace ta haihu, tana ma iya jawo wa mai juna-biyu matsaloli masu tsanani.

Hakan na kara hadarin samun cutar hawan jini da cutar sukari. Za ta ma iya shafar lafiyar jaririn kansa, da har ta iya kaiwa ga yin tiyata a cire dan, ko ma matar ta yi bari.

Hakkin mallakar hoto ianhootonsciencephotolibrary

Farfesa Jane Ogden ta jami'ar Surrey da ke Biritaniya, ta gano cewa wasu matan suna ganin cikin da suke dauke da shi, shi ke nuna musu yawan abincin da za su so su ci.

To idan har abin haka ya ke, akwai hadarin sabawa da cin abincin mutum biyu ga mai ciki, domin zai yi wuya ta iya rage yawan abincin da ta ke ci bayan ta haihu, ko kuma can gaba idan kika fara shayarwa.

Sanya mutane su kiyaye da wata ka'ida wata matsala ce. Mata da yawa suna cewa su kan ji yunwa sosai idan suna dauke da juna-biyu, saboda haka ba abin mamaki ba ne cin abinci mai yawa da su ke yi.

Nazarin da kungiyar likitoci ko masanan abinci ta Amurka ta yi, kan matakan taimaka wa mata su rage teba yayin da su ke dauke da ciki, ta gano cewa wasu matakan sun yi aiki wasu kuwa ba su yi ba.

A kasar Finland mata suna cin 'ya'yan itace da ba a dade da debo su ba sakamakon shawarar, amma kuma ba su rage kiba ba.

A Amurka wasu matakan sun yi amfani, sai dai idan daman mace mai teba ce tun kafin ta samu ciki.

Wadansu nazarce-nazarcen da aka yi a tsakanin al'ummomi (Native American Cree communities) a kasar Canada, sun gano cewa shawara game da irin abincin da mace za ta ci tana da dan tasiri ne kadan ne kawai.

Kuma wani nazari na baya-bayan nan da aka yi na matakai daban-daban ya gano cewa wadanda suka karfafa wa mata gwiwa kan su rika cin abinci mai kyau sun fi tasiri wajen daidaita kibar mata da yanayin lafiyar juna biyunsu fiye da wadanda ke shawartar mata su rika tattaki da motsa jiki sama-sama.

Yawan abincin da za a ci

Ina kuma maganar mace ta ci abincin mutum uku ko ma hudu, idan tana sa ran haihuwar 'yan biyu ko 'yan uku? Lalle ne suna bukatar cin abinci mai yawa sosai? Watakila ba lalle ba ne.

Idan abin da mace ke dauke da shi a cikinta ya fi daya, yanayin aikin jikinta yana karuwa da kashi 10 cikin dari, abin da ke sa jikin sarrafa makamashi ko abincin cikinta da sauri.

Wasu tsare-tsaren cin abinci na shawartar matan da ke sa ran haihuwar 'yan biyu ko 'yan uku su rika cin karin abinci a rana (calory 4,000).

Kusan yawan abin da a ke shawartar sojin Biritaniya da ke aiki a Afghanistan su rika ci.

Amma wannan bai yi la'akari da cewa mata masu ciki za su iya kasancewa sun fi sojojin da ke yaki zama ba sa aikin komai ba.

Wani abin da kuma ya ke da muhimmanci a sani shi ne cewa, matan da ke sa ran haihuwar 'yan biyu ko 'yan uku, wadanda ba su kara kiba yadda ya kamata ba (ba su kara yawan abincin da suke ci ba), za su iya haihuwar jarirai kanana sosai.

Amma duk da cewa ana gaya wa mata (masu juna biyu), wani lokaci su kara yawan abincin da su ke ci sosai, ba a san takamaimai inda maganar ainahin yawan abin ya kamata su ci ta samo asali ba.

Abin damuwar shi ne, nazarin da aka yi a tsanaki a 2011 bai iya gano ko da wani bincike guda daya mai kyau da aka yi wanda ya bambance tsakanin abinci na ka'ida da mata ke ci ba da kuma na musamman mai kara kiba ba.

To kuma idan har ba a san wannan bambancin ba, wanene zai iya cewa ga shawarar da ta ke da kyau?

Saboda haka idan aka kawar da maganar haihuwar jariri fiye da daya, menene karin yawan abincin da ya kamata mace mai ciki ta ci kenan?

A Amurka cibiyar nazarin harkokin likitanci ta bayar da shawarar mace mai ciki ta ci abinci sau uku da dan abin makulashe (snacks) biyu a rana.

Za ka dauka wannan wani abinci ne mai yawa, sai ka duba ka ga yawansa bai taka kara ya karya ba, domin abinci ne da aka saba ci na yau da kullum da kwai biyu kawai (karin calory 340) a rana a watannin tsakiya na cikin.

Sai kuma chakulet (chocolate) guda biyu mai sanya narkewar abinci da sauri da biredin tafarnuwa (karin calory 452) a kashi na uku na watannin juna-biyun.

Saboda haka abu ne mai wuya a ce mai juna-biyu ta rika cin abincin mutum biyu.

Kamar yadda kwararren likitan mata masu juna-biyu na Landan, Patrick O'Brien, ya ce, '' Kina cin abincin mutum daya da dan kari ne kawai.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Should pregnant women eat for two?