Shin dabbobi na jima'i don jin dadi kawai?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ba dan adam ba ne kadai ya san dadi da amfanin sumba

Mun dauka cewa mu kadai ne halittar da ke jin dadin jima'i, to amma kamar yadda Jason G Goldman ya gano saduwar da wasu dabbobi ke yi ta sauya yadda mu ke kallon lamarin.

Jima'i an fada mana cewa, jin dadi ne. Amma kuma duk da haka kila idan ka bincika littattafai da rubuce-rubuce na kimiyya ba za ka yi tunanin hakan ba.

Hakan ya kasance ne kuwa ba domin komai ba, illa cewa yawancin bayanan kimiyya game da jima'i sun dogara ne a kan bayanan zuwa ko samun halitta, maimakon yanayin da hankali da kuma jiki ke shiga a daidai lokacin saduwar.

Mu ambata cewa muna jima'i ne domin yana taimaka mana mu hayayyafa don dorewa da wanzuwar jinsinmu na dan adam gaskiya ne, ba wata shakka a kan hakan.

Sai dai mun bar dan wannan takaitaccen shaukin dadin da mu ke shiga, wanda ke tattare da wannan saduwa ta hakika, wato dai kamar a ce ne an yi tuya an manta da albasa.

Abin da mu ke ta hankoron sani dai shi ne, ko mu kadai ne jinsin halittar da ke jin dadin jima'i.

Tambayar ko sauran dabbobi wadanda ba mutane ba, su ma suna jin dadin jima'i, tamabaya ce dadaddiya mai muhimmanci a kimiyyance.

A shekara 10 zuwa 15 da ta gabata ana samun tarin shedar da ke nuna cewa dabbobi suna jin dadi da ke mamaye jiki baki daya.

Wanda duk ya ke yi wa kyanwa shafa ya san da haka.

A shekara ta 2001 misali, masana tunanin dan adam Jeffrey Burgdorf da Jaak Panskepp, sun gano cewa berayen dakin bincike na kimiyya suna jin dadi a dan yi musu cakulkuli, inda har sukan yi 'yar wata kara ko dariya amma wadda kunnen mutum ba zai ji ba.

Kuma har ma za a fahimci cewa suna son a yi musu hakan domin su ji wannan dadi.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Mun san cewa dabbobi kamar kyanwa su kan samu jin dadi da ke mamaye jiki baki daya, to amma suna jin hakan ta jima'i?

To amma wannan ya hada da jin dadin jima'i? Wata hanya ta sanin wannan ita ce, ta yin nazari kan saduwar da ba za ta kai ga samun ciki ba, misali, tsakanin maza biyu ko fiye da haka ko tsakanin mata, inda daya ko sama da da haka bai balaga ba.

Ko kuma nazarin jima'in dabbobin da ba a lokacinsu na haihuwa su ke ba.

Misali, nau'in biran da a ke kira Bonobos da Ingilishi, an san su da saduwa tsakanin jinsi daya, da kuma alaka ta saduwa tsakanin baligansu da mazan da ba su balaga ba sosai ko matasa.

To amma ba nau'in wannan birin ne kadai ba ya ke jin dadin jima'in da ba na daukar ciki ba, saboda wani jinsin birin (capuchin) shi ma yana wannan saduwa.

A tsakanin dukkanin wadannan nau'uka na birai guda biyu, masana halayyar dabbobi Joseph Manson, da Susan Perry, da Amy Parish, sun gano cewa matan su kan yi jima'i da yawa ko da kuwa a lokaci ne da ba za su taba daukar ciki ba.

Misali lokacin da su ke shayarwa bayan sun haihu ko kuma lokacin da su ka riga suka yi ciki.

Haka kuma saduwa tsakanin baligan wadannan birai da wadanda ba su balaga ba, abu ne da ke faruwa sosai kamar jima'i tsakanin baligai.

Idan dabbobi suna yawan saduwa a lokacin da ba na daukar ciki ba, wannan zai iya tabbatar da cewa, suna yin hakan ne domin jin dadi.

Zakanya za ta iya saduwa kusan sau 100 a rana a cikin kusan mako daya, da zaki fiye da daya, idan mahaifarta ta bude (tana shirin daukar ciki).

Duk da cewa mani daya ne kawai zai sa ta dauki ciki, hakan bai hana ta wannan jima'i da yawa ba. Ko watakila hakan na nufin tana jin dadin saduwar ne?

Haka ita ma damisa, nau'ukanta da a ke kira ''cougar'' da ''leopard'' da Ingilishi, su ma suna irin wannan jima'i.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu bincike sun dade suna nazarin yadda birai ke dabi'unsu daban-daban

Wata hanyar da kuma za ka iya sanin ko dabbobi suna jin dadin jima'i, ita ce ta ko suna yin inzali.

Wannan musamman ma a kan mata, domin ciki na iya shiga ba lalle sai mace ta yi inzali ba.

Wasu masu bincike 'yan kasar Japan, Alfonso Troisi da Monica Carosi sun shafe sa'o'i 238 suna kallon wasu birai, inda suka ga saduwa 240 tsakanin maza da mata.

A jima'i kashi daya bisa uku na wannan adadi, sun ga abin da su ka kira gamsuwar tamatar (inzali), ''inda matar ta kan juyo kanta ta kalli namijin da ke saduwa da ita, ta mika hannunta daya ta kankame shi''.

Duk da cewa abu ne da ba zai yiwu ba, ka iya tambayar biranyar yadda ta ke ji, a hankalinka za ka iya kwatanta abin da ta ke ji ko yi, daidai da abin da matar dan adam ke ji a lokacin da za ta yi inzali, akalla ta wasu hanyoyi.

Haka shi ma jima'i ta baki abu ne da ke wakana a tsakanin wasu dabbobi sosai, kamar birai da kuraye da awakai da tumakai.

Ita ma damisa (cheetah) da zakanya su kan shafa tare da lasar mazakutar mazansu a matsayin wasansu na shirin saduwa.

Haka shi ma jemage akwai nau'insa da ya ke wannan dabi'a tsakanin mace da namiji, wadda ke sa su dade a lokacin saduwa, abin da kuma ke iya sa matar ta samu ciki.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ana ganin wasan saduwa ta baki kan kara yanayin samun ciki a jima'in wasu jemagu

Za a iya cewa misalin da ke bayyana wannan lamari a nan shi ne na wani nazari da aka yi a kan wata dabba da ake kira ''bear'' da Ingilishi, nazarin da aka wallafa a farkon shekarar 2014 a mujallar abubuwan da suka shafi rayuwar dabbobin dawa ta ''Zoo Biology''.

Nazarin a kan wasu mazajen wannan dabba ce guda biyu da aka kama, inda masu bincike a Crotia, suka rika nazari da lura da dabi'un wadannan dabbobi da ke tsare har tsawon sa'o'i 116, wadanda suka hada da jima'i ta baki da su ke yi.

Masu binciken karkashin jagorancin Agnieska Sergiel, ta makarantar nazarin kula da dabbobin daji ta Poland, suna zargin dabbobin (maza) biyu sun dauki wannan dabi'a ta jima'i ta baki ne sakamakon rashin samun damar dabi'ar tsotson nono tun suna kanana.

Saboda an kawo su wannan wuri ne suna kanana, tun kafin uwayensu su yaye su.

Wannan dabi'a ta bi su har lokacin da su ka wuce munzalin masu shan nono, watakila saboda suna jin dadi tare da samun gamsuwa daga gare ta.

A yawancin lokaci masu bincike su kan dogara ne a kan tsarin wanzuwar halitta su yi bayanin wannan dabi'a ta dabbobi.

Su ki yarda tsarin juyewar dabi'ar dabba zuwa ta dan adam ya ja su.

Kamar yadda masanin halayyar dabbobi Jonathan Belcombe ya wallafa a mujallar dabi'un dabbobi ta ''Applied Animal Behaviour Science'', cewa, '' rashin dadin ciwo yana taimakawa wajen sa dabba ta bar wata dabi'a da a ke iya dauka maras kyau ce, wadda ke iya kaiwa ga hadarin mutuwa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Ko sha'awar da dabbobi da mutane ke da ita ta jarraba abinci iri-iri na da alaka da sha'awarsu ta gwada duk sabon abin da ba su sani ba?

Duk da haka Belcombe yana ganin bai kamata ba masana kimiyya su rika kallon dabi'a ta hanyar juyi ko samuwar halitta ba (evolution).

Masanin ya ci gaba da bayanin cewa beraye sun fi zabar abincin da ba su sani ba, a kan wanda suka sani, bayan an yi kwana uku ana ba su abinci iri daya.

Bayani mai sauki a kan wannan dabi'a shi ne cewa, ana ganin, dabi'ar berayen ta sabo ce, saboda abinci iri-iri zai ba su damar samun kayan gina jiki daban-daban.

Ko kuma saboda hakan zai sa kada su dogara a kan takaitacciyar hanyar samun abinci (abinci daya).

To amma za a iya cewa wata 'yar gajeruwar fahimta ce kawai, idan aka ce berayen sun gaji da abinci daya ne kawai, saboda haka suna son jarraba wani abu sabo ne? Domin su dan kara samun wani dandano?

Dukkanin wadannan bayani biyu za su iya kasancewa gaskiya, ya danganta ne ga ko ka dauki abin da fadi ko kuma ba ka fadada ba.

Haka ita ma dabi'a ta jima'i (da wata dabba ta ke yi) za ta iya kasancewa mai dadi gaba dayanta, duk da cewa ta samo asali ne tun daga matakin samuwar halitta ko dabba.

Dalili a nan shi ne, saboda yaduwa (haihuwa) tana da muhimmanci sosai, domin dorewar jinsin halitta, shi ya sa tsarin samuwar halitta (evolution) ya sanya jin dadin da dabbobi, (dan adam da wadanda ba dan adam ba), za su bukaci ta ( saduwa ko jima'i), ko da kuwa ba sa son samun ciki ko kuma ma ba za a samu juna biyun ba idan an yi jima'in.

Belcombe ya ce, bukatar neman wannan dadi, ''gamayya ce ta ilhama ko baiwa da ke tattare da halitta, a hannu daya, da kuma matukar bukata ta samun wani lada ko dadi ko amfani a daya hannun.''

To idan haka ne, a bayyane ta ke kenan, dalilin da ya sa wannan shauki mai tsananin dadi (na jima'i) ya zamanto ba ga mu 'yan adam kadai ya tsaya ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Do animals have sex for pleasure?