Intanet ta yaudare ka, kada ma ka dauka ba a sani ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Idan muna amfani da intanet mu kan dauka cewa mu masu ilimi ne sosai

Intanet za ta iya yaudararmu da ilimi, ta sa mu dauki kanmu cewa karanmu ya kai tsaiko ko kuma ma mu dauka cewa mun san kusan komai a fagen ilimi. To amma dadin abin akwai hanyar maganin wannan tunkaho.

Masanin tunanin dan adam Tom Stafford na dauke da bayani.

Intanet ta yi fice wajen samar da mutanen da ke ji cewa su ai sun san komai.

Masu bayyana ra'ayi a kan wata kasida da masu bayar da bayanai ta shafukan intanet, hatta 'yan makarantarku ta da, wadanda ke Facebook, dukkaninsu kusan suna tunkaho da cewa sun san yadda duniya ke gudana.

Kuma suna zakwadi da azarbabin sanar da kowa da kuma duk wanda zai saurare su.

To a yanzu dai wani sabon bincike ya nuna cewa samun hanyar kaiwa ga bayanai na duniya kadai zai iya sa mu rika ci-da-zuci da girman kai.

Sai dai kuma dadin abin shi ne, binciken ya bayyana hanyoyin da za a iya bi domin magance wannan matsala ta ci-da-zuci da tunkaho.

A takaice dai a nan muna duba yadda intanet ta shafi tunaninmu ne game da abin da muka sani.

Idan har ka san cewa kana bugun kirji, to ba ka da gaskiya, amma dai ba ka yi wani kuskure ba wajen kiyasta iliminka.

Idan har da gaske ka yi imani cewa kai kana da ilimi sosai fiye da tsammani, to ka yi kuskure.

Binciken ya nuna cewa daukar da mutum ke yi ta sanin abu, abin mamaki za ta iya kasancewa abu ne da kusan kowa ya ke da shi, kuma wannan kuskure ya bayyana ne ta wasu sabbin hanyoyi a wannan zamani na intanet.

Wani abu game da yawan neman bayanai ko yin bincike ta intanet, wannan kadai yana yaudarar mutum ya dauka ai shi yana da ilimi.

A wata sabuwar kasida da ya wallafa Matt Fisher na jami'ar Yale, ya yi magana a kan wani nau'i na tunani, wanda tsari ne da mu ke dogaro a kan wasu mutane da sauran sassan duniya kamar littattafai da abubuwa, su rika tuna mana abubuwa.

Idan har ka taba barin wani abu a kofa a daren da ya gabata, wanda ka ke bukata domin yin wani aiki washegari to kenan kana amfani da irin wannan tsari ko ilimi.

Daga cikin matsalolin wannan tsari ko tunani shi ne, kasa bambancewa tsakanin ainahin abin da muka sani a kwakwalwarmu da kuma ilimin da muke iya kaiwa gare shi a saukake, wato ilimin da yake a tanade a duniya, ko kuma wanda muka saba da shi kawai ba tare da saninsa sosai ba (intanet).

Za a ji kamar mun fahimci yadda mota ta ke aiki, wanda alhali kuwa mun saba ne da yadda kawai za mu sa ta yi aiki.

Na taka totar ne kawai sai motar ta tafi, na ki yarda in tsaya na gane cewa ban fa san yadda aka yi motar take tafiyar ba.

Fisher da abokan bincikensa suna da sha'awa kan yadda wannan yanayi ya ke mu'amulla da zamanin nan na intanet.

Sun tambayi mutane su bayar da amsa ga tambayoyi na ainahi kamar, ''me ya sa a ke da bambancin lokaci (agogo)a wurare''?

Rabin mutanen da aka yi wa tambayar an ba su damar su duba amsa a intanet, rabi kuma ba a ba su wannan dama ba.

A gaba kuma sai aka tambayi dukkanin mutanen irin kwarin gwiwar da suke da shi na bayyana amsar wasu jerin tambayoyi na gaba.

Tambayoyin daban su ke, amma su ma na abu ne na zahiri, kamar ''me ya sa gajimaren dare ya ke da dumi?'' ko kuma ''Ya a ke yin misali bammi?''.

Kamar yadda aka sani wadanda ba su jima ba da duba intanet domin samun bayani sun fi kwarin gwiwa na fahimtar sauran tambayoyin.

Sauran binciken da aka biyo baya da shi ya nuna cewa mutanen da suka duba intanet din suna dauka cewa ilimin nasu ne.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Muna jin shucin gizon (rudi) cewa bayanan da mu ke iya samu ta intanet a kanmu su ke (iliminmu ne)

Idan wannan yanayi na jin cewa muna da dama ko iko a kan samun bayani, ya sanya mana ci-da-zuci, za a iya cewa intanet kenan na'ura ce ta mayar da dukkaninmu tamkar ramuka.

To sai dai an dace cewa wani nazari ko bincike, wanda shi ma aka wallafa a wannan shekara (2015) ya kawo 'yar hanyar da ya ke ganin kila za a dan magance matsalar.

Amanda Ferguson ta jami'ar Toronto da abokan aikinta sun gudanar da irin wannan bincike, sai dai nasu a juye suka yi shi.

Sun bukaci mutane (wadanda aka yi gwajin da su) ne su bayar da amsa farko, amma idan ba su san amsar ba to sai su shiga intanet su duba.

A wannan tsarin mutanen da su ke da damar shiga intanet sai suka noke ba sa son su bayar da amsa da farko (saboda ba sa son su ji kunya ba su bayar da amsa daidai ba, tun da har a nan gaba za su iya duba intanet din, su amsa tambayar, kuma da haka jahilicinsu ba zai bayyana ba sosai), ba kamar wadanda ba su da damar shiga intanet din ba.

Saboda haka su wadannan mutanen damar shiga intanet din ta rufe su , maimakon ta sa su nuna cewa su, sun san komai.

Saboda haka sanya mutane a yanayin da za a iya bincikarsu a gaba, yana sa su yi hankali, su natsu a kan irin ikirarin da za su yi game da kansu a can baya.

Abin da na fahimta daga nan shi ne, hanya daya ta yaki da, wanda ke dauka cewa shi ya san komai, idan har kana da karfin yakin, ita ce, ka nuna masa cewa za a bincike shi, ciki da bai a kan ko daidai ya ke ko ba daidai ya ke ba ( bayan ya bayar da amsar).

Ba lalle ba ne hakan ya hana su binciken amsa mai tsawo ba ta intanet din, amma dai hakan zai dan sa su rage zakwadi da ji da kai da tunkaho, kuma zai dakushe jin da su ke yi cewa kawai saboda intanet ta san wasu bayanai, su ma sun sani kenan.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kafin ka kara nuna cewa kai ka san komai a nan gaba, sai ka yi tunani

Ana yawan tambayar cewa ko intanet na sauya yadda muke tunani. Amsar da wannan bincike ya nuna, ita ce intanet na samar da wani sabon makamashi ga yadda mu ke tunani a ko da yaushe.

Hakan zai iya kasancewa sanadin ci-da-zuci a gare mu, idan mun kuskure muka kasa gane iyakar abin da muka sani da kuma abin da ya ke a intanet, wanda za mu iya dubawa mu gani.

Haka kuma zai iya kasancewa sanadi na rashin tabbas idan muna ganin za a bincike mu, ta amfani da intanet din a kan amsar da muka bayar ko ikirarin da muka yi (domin mun san za a gano inda muka dauko amsar da muka bayar).

Yanayi na kasancewar mu iya zuzuta abin da muka sani, da amfani da bayani ko ilimin da ya ke a tanade (a intanet) a matsayin ilimi maimakon ainahin iliminmu na kanmu, da kuma damuwar za a iya kama mu (gane cewa ilimin intanet ne ba namu ba), dukkanin wadannan na nan suna tasiri ko da yaushe a kan yadda mu ke tunani.

Intanet ta samu damar kutsawa cikin ainahin matattarar iliminmu ta halitta, wadda daga wannan matattara ne tarin abubuwa sababbi marassa iyaka ke samo asali (kirkira).

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The web has deluded you, and don't pretend it hasn't