Yadda dabbobi su ke yi wa kansu magani

Hakkin mallakar hoto science phoyo library

Tun da dadewa dabbobi sun kirkiro dabarun kare kansu daga cutuka da rashin lafiya tun kafin mu samo hanyoyin yi wa kanmu magani. Me dabbobin su ke yi?

Ga nazarin Jason G Goldman

Dare da rana a kullum mutane na cikin yaki da cutuka. Muna harba wa kwayoyin cuta na bakteriya (bacteria) makamai masu linzami da jefa wa kwayoyin bairus (virus) gurneti-gurneti.

Muna sakin bama-bamai na magungunan kashe kwayoyin cuta na sabulai da sinadaran tsaftace hannu kusan a kan duk wani abu da za mu iya.

Yaki tsakanin mutane da kwayoyin cuta abu ne da ke da asali tun a zamanin da, kuma abu ne da ke da tsanani a kan wanzuwar halitta kamar yadda wasu dabbobi suka dogara a kan cinye wasu su rayu, da fari da yunwa.

Sauran halittu ma na fuskantar irin wannan barazana, kuma wannan shi ne ya ke tuna mana irin illar da kwayoyin cuta suke yi wa duniya a kullum.

Halittu iri daban-daban na ruwa da na tudu na fama da matsaloli da barazana daga kwayoyin cuta iri-iri.

Jemagu da birai, hatta mutane ma na cikin barazana daga kwayar cutar Ebola da ta nimoniya wadda ke kama huhu da sauran cutuka.

Idan muka duba wannan za mu fahimci cewa lalle dabbobi suna da hanyoyin da suka kirkiro na kare kansu daga cutuka da rashin lafiya iri-iri, tun kafin dan adam ya san zai hadiyi kwayar magani. To wadanne hanyoyin magani da jiyya ne dabbobin suka kirkiro?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan kifin (salmon) idan ya kasance kusa da kusa ya kan yi saurin yada kwarkwatar ruwa ga dan uwansa

Kanana nau'in kifin da a ke kira salmon ya kan nemi agaji idan yana fuskantar barazanar wata cuta.

A shekara ta 2007 ne irin wannan kifi, ya gamu da annobar wata cuta (ta kwarkwatar teku) wadda ke haddasa karancin jini da kuma kisa, daga wasu nau'in kifin irinsa da a ke kiwo a gonaki a kasar Chile, bayan da aka zuba kifayen a cikin teku suka hadu.

Wannan kifi da sauran nau'in kifaye da suka gamu da wannan annoba sai suka hada kai da sauran kananan kifaye su ka rika cinye musu wannan kwarkwata da ke jikinsu.

A teku da wuraren da a ke kiwon kifaye, an dade da sanin wasu kifayen (corkwing wrasse, ballan wrasse, cuckoo wrasse, goldsinny, rock cook)wadanda ke tsaftace wuri daga kwayoyin cutuka, ta hanyar cinye halittun da ke haifar da cutuka.

Su wadannan kifaye masu tsafatce wuri sukan cinye kwayoyin cutar a matsayin abinci, su kuma sauran kifaye da ke wurin wadanda kwayoyin cutar a da suka addaba sai su samu lafiya.

A shekarun 1990, cibiyar nazarin harkokin kiwon kifi ta kasar Norway ta gano cewa kwaya daya kawai na wani daga cikin nau'in kifayen da ke cinye kwayoyin cuta da a ke kira 'wrasse' a Ingilishi, ya isa kare lafiyar kifin da a ke kira 'salmon' har guda dari daya.

Haka kkuma wani binciken nasu ya gano shi kuma wani kifin mai suna 'goldsinny' guda daya zai iya kare lafiyar salmon 150.

Shi 'goldsinny' guda daya zai iya cinye wannan kwarkwatar teku guda 45 a jikin salmon a cikin minti 90 kawai.

Haka a jinsin 'yan kananan kwari kamar su tururuwa da kiyashi ma akwai hanyoyin da su ke da su na kare tarayyarsu daga cutuka.

Ta wata hanyar, irin wadannan kwari suna rayuwa kamar al'umma daya ne, maimakon su bar kowanne daya a cikinsu ya nema wa kansa lafiya idan ya gamu da wata cuta, domin a tarin nasu suna da wani tsari na kula da lafiya wanda masana suka kira babbar garkuwa (social immunity).

Binne matacce

Idan tururuwa (ko wani kwaro nau'inta; red ant) daya ta mutu, sauran dangi sai su taru gaba daya su dauke gawar daga cikinsu.

Zuwa yanzu ba a san irin kwayoyin cuta na bakteriya da bairus ko fungai (fungi) da su ke fito wa daga jikin gawar ba.

Amma masana ilimin halittu suna ganin kawar da gawar daga cikinsu wata hanya ce ta kare kansu, wadda kwarin su ke yi domin za ta iya kasancewa wadda ta mutun ta kamu da wata kwayar cuta ne, kuma in ban da yanzu ba a gano hakan ba.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Tururuwa na da saurin kamuwa da cuta, amma kuma tana da hanyar maganinta

A farkon shekara ta 2014 mai bincike 'yar kasar Belgium Lise Diez da abokan aikinta sun yi nasarar gano shedar da ta tabbatar da wannan fahimta.

Masu binciken sun tara tururuwa (myrmica rubra) a dakin bincikensu na kimiyya har tsawon kawana 50.

Rabin tarin tururuwa suna da damar dauke gawar duk dan uwansu da ya mutu kamar yadda su ke yi a duk inda su ke.

Rabi kuwa ba su da wannan dama, kamar yadda masu binciken suka tsara wurin da suka tara su.

Daga rana ta takwas, manyan tururuwan (ma'aikata) daga cikin rukunin wadanda aka bari a sake, da za su iya kawar da gawar 'yar uwarsu in ta mutu, za su fi kasancewa a raye fiye da wadanda ba su da wannan dama.

Abin mamaki, su wadanda ba a ba su damar kamar da gawar ba, sai suka yi wata dabara ta rage yawan hadarin kasancewa kusa da gawa, inda suka rika daukar gawawwakin wadanda suka mutu su ke kaiwa su ajiye a kusurwowi, wanda hakan ya rage yawan masu rai da za su rika wucewa kusa da gawarwakin a kan hanya, kuma hakan ya rage musu hadarin kusanta da tsutsar da gawar za ta iya yi.

Wasu daga cikin su wadannan tururuwai da aka hana damar hanyar da za su fitar da gawa daga cikinsu, sun ma yi dabarar binne wasu gwarwakin a cikin wata auduga da suka samu a wurin da su ke.

Dabara ko dabi'un kare dabba daga kamuwa da wasu kwayoyin halitta na cuta, wadanda suka hada da samar da kifin da ke cinye halittun da ke yada cuta, da dabarar boye gawa, kila sun samu ne domin kawar da tasirin cuta a kan mai rai, kamar yadda wasu dabbobin su ke iya sajewa da launin wuri domin kare kansu daga wata muguwar dabbar da ke farautarsu.

A wani nazari da aka gudanar a kan wasu tarin jinsinan manyan dabbobi masu shayarwa (dawakai da jakuna da kanki da barewa da makamantansu) guda 60, a gidan namun daji na San Diego da Safari Park an gano cewa dabbobin suna kokarin tsaftace kansu (sharewa da kade jiki ) duk da cewa suna wurin da wasu kwari masu yada cuta ba za su same su ba.

Ma'ana wannan dabi'a ce da dabbobin su ke yi a matsayin riga-kafi maimakon kawai susa idan jikinsu na musu kaikayi.

Ko da ya ke wannan nazari an yi shi ne a kan wadannan jinsinan dabbobi, amma ana ganin, dabi'ar gyran jikin a tsakanin dabbobi, kama daga damusa da ke lasar jikinta zuwa birai da ke cire kwarkwata da sauran kwari a jikinsu, duk abu ne da ya samo asali daya (riga-kafi da kare kai daga cutuka).

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Wasu dabi'un dabbobi na kula da jiki sun yi kama da namu. Wadannan biran suna wanka ne a wata koramar ruwan zafi a Japan

Mai binciken magungunan dabbobi Benjamin Hart, a 1988, ya rubuta (Neuroscience and Biobehavioral Reviews) cewa, ''a nazari da binciken dabbobin da su ke rayuwa a kusan wurin bincike na kimiyya mai tsafta da sauran wurare da aka killace, kuma a ke musu riga-kafin cutuka da magani idan suna rashin lafiya, abu ne mai sauki a manta cewa, su fa dabbobi suna rayuwa ne a cikin tarin wasu kwayoyin halittun masu yada cutuka tun kafin samun kariya ta dan adam.''

Maganar tsafta

Mu mutane muna da hanyoyi da yawa na gado na kariya daga cutuka.

Ta hanyar duba kwayoyin halitta masu yada cuta a cikin kwayoyin kashi a jikin kasusuwan mutanen da a ke ganowa a tsoffin kaburbura a Masar, da sauran wuraren tarihi na karkashin kasa, da hada irinsu da kwayoyin halittu masu yada cuta da aka san suna kama dan adam da sauran birai, mai bincike na jami'ar Cambridge Piers Mitchell, ya iya gano wasu halittu masu yada cuta kamar tsutsotsin ciki (ta hanji da ta koda da ta madaciya).

Wadanda dukkanninsu kusan muna da hanyoyinmu na gado ko na halitta (a ciki) na yadda mu ke maganinsu, domin mutum yana tare da su miliyoyin shekaru ko ma fiye da haka.

Saboda haka ne jikinmu ya fi iya tunkarar yaki da cutukan da wadannan tsutsotsin ciki ke yadawa fiye yaki da halittu masu yada cutuka, na waje, wadanda a baya bayan nan muka gamu da su. Kamar yadda masana ke gani.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Miliyoyin shekaru mutum na yaki da cutukan tsutsar ciki, abin da ya sa har cikinsa ya iya maganinsu

Saboda haka me ya ke faruwa kenan, idan muka yi amfani da duk wani makami na yaki (tsafta) da kwayoyin cuta, kama daga magunguna da sabulu mai magani da sauran kayan tsafta?

Zuwa wani dan lokaci, fasaha da kirkirar mutum sun ba mu damar yin galaba a gogayyar mallakar makamai da mu ke yi a kan 'yan mitsimitsin kwayoyin halittar masu yada cuta, wadanda su ke sanya mana rashin lafiya.

Yanzu tun da mun samu wannan kariya ta dan adam, za mu ga kamar muna tsaftace kanmu sosai.

To amma kuma ta hakan za mu iya kawar da (kashe) kwayoyin halittun da su ke da amfani ga lafiyarmu a yayin yaki da masu cutarwar.

Sai dai akwai hanyoyi da za a iya cewa marassa dadin gwaji da a ke jarrabawa domin kawar da wannan matsala.

Gwaje-gwajen farko sun nuna za a iya maganin wasu cutuka na kan-jiki da sauransu ta hanyar hadiyar wasu tsutsotsi masu cutarwa.

Ko kuma ta hanyar mayar wa mutum wasu kwayoyin da ke cikin kashi, wadanda ke da amfani ga jiki.

Duk da cewa muna ganin mutane suna samun galaba a wannan yaki da kwayoyi masu yada cuta, dole ne mu kwana da sanin cewa su ma fa wadannan halittu (bacteria, virus, fungi) kwararrun halittu ne masu dabara, wadanda tuni suka kirkiro hanyoyin kare kansu daga dabarunmu.

Wannan ne ma ya sa za ka ga muna ta kokarin kirkiro sabbin dabaru na zamani domin fuskantar barazanarsu.

To amma wata babbar tambaya a nan ita ce; ko akwai wata dabi'ar tsaftace jiki da za mu iya koya daga sauran dabbobi, wadda za ta taimake mu yin nasara a wannan yaki da cutuka?

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan, How animals deal with infection