Kai da yaro wa ya fi kirki?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Abu ne da yawancin mutane suka yarda cewa kananan yara suna da son kansu sosai, amma kamar yadda Caroline Williams ta gano, a yawancin lokaci yara sun ma fi manya kirki.

Caroline Williams

A lokacin bikin kirsimeti na shekara ta 2014, na dauki dan karamin dana zuwa wurin wasannin kwaikwayo.

Sunan wasan da aka yi a lokacin Antarctica, kuma wasa ne domin yara 'yan shekara hudu zuwa bakwai, kuma a wurin babban mutum wasa ne na kamar mafarki.

'Yan wasan sun rika warwatsa fararen takardu a matsayin kamar dusar kankara, suka barbazu a dandalin wasan gaba daya.

Bayan wannan kuma sai a can gaba 'yan wasan suka yi shiga kamar ta manyan kifaye (seal),suka rika birgima a cikin takardun nan da ke zaman kamar dusar kankara, sanye da gashin baki na bogi, suna yi wa junansu haushi (wannan duka kamar yadda irin manya-manyan kifayen nan ne da a ke kira 'seal' su ke yi a bkin teku).

Idan na dauki wannan kamar wani abu bako da ban saba gani ba, to hakan ba ma komai ba ne idan aka kwatanta da abin da ya faru bayan wasan.

Lokacin da 'yan wasan suka bar dandalin, iyayen yara suka fara tattara 'yan jakunkuna da rigunan kwat na 'ya'yan nasu, sai wata mata dauke da wata 'yar akwati ta bullo ta je bayan dandalin wasan kusan ba tare da kowa ma ya lura da ita ba.

Ba tare da ta kalli kowa ko ta ce wa kowa komai ba ta ajiye akwatin a kasa ta koma baya.

Kafin ka ce me, sai dukkanin yaran da su ke wannan babban daki, suka rika tururuwa suna ta kwashe fararen takardun nan (da aka yi amfani da su a matsayin dusar kankara), suna sa su a cikin akwatin.

Ba fa wanda ya ce wa yaran su yi hakan. Ba wata magana da yaran su ke yi a tsakaninsu ko musun wa zai dauki wannan ko wancan. Haka kawai suka yi wannan abu.

Sai iyayen yaran suka rika kallon junansu cike da mamaki, ba su san abin da ya sa yaran yin hakan ba. Abin kamar an tsafe su.

To me ya ke faruwa? Matar da ta kawo akwatin ta yi wa yaran wani siddabaru ne? Wani yaro ne daya ya fara yi sauran suka ga kamar wani abin nishadi ne su ma suka bi shi suna yi? Ko kuma za ta iya yuwuwa yara na da tausayi ne da son yin taimako?

PIC 1

Bayani na karshe na maganar ko yara suna da son taimako, kusan shi ne abu na krshe da za a iya tunnin dangantawa da lamarin, domin kananan yara ba kasafai aka san su da rashin son-kai ba (sun fi kishin kansu), sannan kuma, akalla ni dai a gidana tsaftace wuri abu ne da yara ke yi a bisa dole, idan an tilasta musu.

Amma kuma a wurin masanin tunanin dan adam (tun daga tushe), Felix Warneken, na jami'ar Harvard, bayanin na karshe shi ne tabbas zai iya zama dalilin abin da ya sa yaran suka yi hakan (wato tausayi).

Masanin wanda ya ke nazarin dabi'ar taimako a rayuwar yara daga 'yan wata 14 zuwa 'yan shekara biyar, ya yi amanna cewa kananan yara suna da tausayi da taimako matukar matakin yadda duk dan adam zai iya kaiwa.

Malamin ya ce, ''akwai tunanin da a ke yi cewa ana ganin sai mun koya wa yara yadda za su rika nuna tausayi da taimakon wasu, saboda suna da son kansu da frko, amma kuma yanzu bincike ya nuna labarin ya fi hak sarkakiya,''

A gaskiya ma dai nazarin dabi'ar yara ka iya koya mana abubuwa da yawa a game da kirki da tausayin da dan adam ya ke da.

Taimakon juna;

Taimako shi ne babban bangaren abin da masana tunanin dan adam ke kira kaunar zamantakewa, wadda ke samar da dankon zumunta.

Wannan dabi'a (taimako) a wurin manya ta tattaru ne a jikin halayya ta gari da kuma al'adu masu kyau na al'ummma, wanda hakan ya sa abu ne mai wuya a iya amsa tambayar cewa ko lalle taimako abu ne na rashin nuna son-kai zalla.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wannan ne dalilin da ya sa Warneken ya ke son nazarin dabi'ar a tsakanin kananan yara, bisa yarda da cewa idan ka same su tun suna kanana a lokacin al'umma ba ta sauya su ba.

Amma idan dabi'a ce da aka halicci mutum da it, zai kasance tana tare da shi tun daga shekarar farko ta rayuwarsa, da zarar sun kai girman da za su iya taimako.

Malamin ya yi tunanin wannan nazari ne a lokacin yana matashin dalibin da ke karatun digirin digirgir (digiri na uku; dakta), wanda ke cike da zumudi.

Da farko abokan karatunsa wadanda suka fi shi kwarewa suna ganin ma ba wani abin a-zo-a-gani da zai gano a nazarin.

A lokacin ya tuna yadda ya ke tunani, ''ina tunanin cewa idan na jefar da wani abu (bisa kuskure) yaran suka tsinta za su dawo min da shi kuwa?''

Ya ce, ''wasu mutanen suka ce, 'ko alama, yaran ba za su ba ka ba'. Amma duk da haka na jarraba.'' Kuma ka san mai ya faru? Yaran sun taimaka suka dawo min da abin.

Tun daga wannan lokacin ya gano cewa kananan yara tun suna 'yan wata 14 za su taimaki mutumin da ya ke bukatar wani taimako ko ya ke cikin dmuw, ko da kuwa za su dakata da wani abin da su ke yi wanda su ke jin dadi.

A shekara biyu, kuma za su taimaki hatta mutumin da ba su ma san ko yana bukatar wannan taimako ba ma, domin ba su ma ga wani abu da ya fadi daga misali hannunsa ko aljihunsa ba.

Kuma abin mamaki yaran ba sa ma sa ran wani lada da za a ba su, na wannan taimako da su ka yi.

A wani gwaji da aka yi da yara 'yan wata 20, inda aka ba su lada na taimkon da suka yi, hakan bai kara musu wani kuzari ko kwarin gwiwa na sake yin wannan taimako ba, fiye da wadanda ba a ba wa wani lada ba kan taimakon (ko da ya ke da aka karbe ladan hakan ya sa sun rage dabi'ar taimakon).

Wasu nazarce-nazarcen da aka yi kuma sun nuna cewa taimakon juna wata dabi'a ce da aka halicci mutum da ita.

'Yan uwanmu na kusa a halitta, wato birai, suna taimakon junansu ko da ba wani lada da za su samu, abin da ke nuna ga alama wannan dabi'a ta samo asali tun kafin a san yin alheri a cikin al'umma.

Haka kuma a wani nazari da aka yi a wata cibiyar nazarin ilimin sauyin halitta (Max Planck Institute for Evolutionary Anthropology) a Jamus, an gano cewa a lokacin da yaro ya ke shekara biyu, yana da yanayi (tausayi) iri daya, kamar yadda aka auna sauyin da girman kwayar idonsa ke yi, alokacin da suka taimaki wasu mutane kamar a lokacin da su ma aka taimake su.

Wannan na nuna alamar cewa an halicce su ne da wannan dabi'a ta tausayawa da taimakon wasu.

Mugun sauyi;

Duka wannan abin ya jawo tunanin wannan tambayar cewa, to wai me ya ke faruwa da wannan kyakkyawar dabi'a tamu ta taimakon wasu, idan muka girma?

Ganin cewa, manya (iyaye da suka kai 'ya'yansu wurin wasan nan), suna ganin bukatar share wannan dandali da aka barbaza takardu, amma kuma ba wani daga cikinmu da ya yi tunanin yin wannan taimako. Me ya sa?

Da farko dai za a ga kamar yayin da muke girma muna rasa wannan imani da tausayi, amma kuma wani masanin tunanin dan adam Martin Hoffman na jami'ar New York, wanda ya yi shekara sama da 30, yana nazarin tausayi, bai yarda da hakan ba.

Ya ce, ''ba wata sheda da ke nuna cewa manya ba su da tausayi kamar kananan yara.''

Hakkin mallakar hoto Thinstock

Maimakon haka, ga alama a lokacin da muka girma, mukan tsaya ne mu yi nazarin abin da ke faruwa, mu ga abin da ya kamata a yi a game da lamarin.

A karshe za ka ga muna son mu taimaka, muna kawai nazari ne na zabin abubuwan da za mu yi (ko taimakon zai iya haifar mana da illa mu ma da sauransu), kamar yadda Warneken ya nuna, wannan domin amfanin kanmu ne.

Ya ce, ''dukkanin wadannan abubuwa ne na dabarar rayuwa, domin ba abu ne da zai dace ba, a ce ka bayar, ka byar, ka bayar, ko da yaushe.''

Hasalima ba wanda ya ke nuna cewa shi mutum a ko da yaushe ba mai son kansa ba ne. Amfani da damar da ake da ita tabbas na daga halittar t mutum kamar yin taimakon, kamar yadda masanin ya nuna.

Can baya a shekarun 1970, masana tunanin dan adam Bibb Latane da John Darley sun auna wannan tsari na yanke hukuncin abin yi ( ka taimaka ko kada ka taimaka).

Masanan sun bayyana wani yanayi ko mataki da ke sa a hadakar baki, yawan mutanen da ke ciki na rage damar samun taimakonsu.

Kamar yadda Bibb da Darley suka nuna, muna bin matakai biyar ne na yanke shawara, ko mu taimaka ko kuma kada mu taimaka.

Da farko muna gano cewa mutum yana bukatar taimako, sai mu gano cewa abu ne na gaggawa, sannan mu ji cewa muna da alhakin taimakawa, a karshe mu duba abin da za mu yi. To daga nan ne kawai za mu yi taimakon. Idan akwai mutanen da za su iya taimakawa da yawa, sai mutum ya ji ba lalle wannan nauyi ya hau kansa ba.

''Kananan yar su ba sa bin wadannan matakai guda biyar na tunani,'' in ji Warneken. ''Su suna ganin matsalar ne kawai, sai su tashi su taimaka.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wani bincike na kwanan nan da Maria Plotner (Max Planck Institute for Evolutionary Anthropology), ta yi ya nuna cewa yara suna fara shiga wannan yanayi na nazari kan bukatar taimkon yayin da suka kai shekara biyar.

Yawancin yaran da ke wurin wannan wasa a wannan rana 'yan shekra biyar ne ko sama d haka, kuma a bisa nazari za a iya cewa da za su iya gamuwa da illar kin bin wadannan matakai

To amma me ya hana su bin matakan? Ni a tunanina ina ji kamar wannan mata da ta zo ta ajiye akwati ta shashantar ko dauke hankalinsu da wani siddabaru na tafiya da tunani ne.

Yara musamman wadanda ba su kai munzalin shiga makaranta ba, ana ganin an fi dauke hankalinsu da wasu dabaru ( ba lalle da magana ba), ba kamar babban mutum ba, saboda haka watakila, nuna alamar cewa su tsaftace wannan dandali (kwashe takardun) kadai, ya isa sa su wannan aiki.

Koma dai menene ya sa yaran nan suka yi wannan abu na taimako ta hanyar mayar da su kamar rakumi da akala, ga alama abu ne da za a iya yi wa wasu yaran da dama, masu irin shekarunsu.

Dan wasn fim James Stenhouse ya tuna yadda irin wannan abin ya taba faruwa, in da wata yarinya 'yar shekara biyu ta dakatar da wani wasan kwaikwayo mai daukar hankali, domin taimakawa a magance wata matsala (taimako).

A wasan fim din James, ya jefa wa budurwarsa ta wasan bokiti ne na kwallon wasan tennis ta tebur cikin damuwa da bacin rai, sannan ya zauna kasa ya rike kansa.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

A tsawon shekara hudu a duk lokacin da a ke yin wannan wasan kwaikwayo, 'yan kallon sai di kawai su zura ido suna kallon kwallon na ta zuba daga bokitin kawai.

Wata rana sai wannan 'yar yarinya ta ga ya kamata ta taimaka masa (dan fim din) kwashe kwallon, ta mayar bokitin. Daga nan sai kawai sauran 'yan kallon wasan su ma suka bi ta suna dauke kwallon, suna mayarwa cikin bokitin.

Tun daga wannan rana kusan a ko wane lokaci a ke wasan sai 'yan kallo su taimaka idan aka zo wannan wuri.

Dan wasan fim James Stenhouse ya ce, akalla ba wai da niyya ba ne, muka ki sauya yadda mu ke wannan wasan tun lokacin da yarinyar ta taimaka ba.

Ya ce, ''dan karamin sauyi ne kawai wanda ba ma za mu iya ganinsa ba, amma dai masu kallon wasan za su iya ji.''

Ya kara da cewa, ''muna sa ran su yi shi yanzu, kuma haka din suna yin shi kusan a yawancin lokaci.''

A zahiri dalilan da ke tilasta yara da manya su yi abin alheri ga juna suna da sarkakiya da wuyar fahimta, kuma har yanzu ba a fahimce su gaba daya.

Ko ma menene ya ke tasiri a zauren wasan kwaikwayo (ya ke sa yara da sauran mutane yin abu na taimako kamar an fada musu su yi), abin da muka sani shi ne, su dai yara an halicce su da dabi'a ta son taimako da alheri ta dan wani lokaci kafin su girma.

Saboda haka idan abu ya taso na yin alheri ko taimako, kila zai fi dacewa ka yi koyi da mafi kankantar mutumin (karamin yaro) da ke dakin da ku ke ciki.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Are you nicer than a child?