Me ya sa mu ke son ganin kwakwaf?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Sauyin halitta ya sa mun zama na'urorin da suka fi neman sani da son ganin kwakwaf a duniya, kuma na'urorin (mutane) suna bukatar neman sanin kwakwaf ya zama abin da ke zaburar da su.

Ga nazarin Tom Stafford

Ba na son in ba ka kunya, amma ko wane irin buri ko fata ka ke da shi, na tabbata karanta wannan kasida ba zai ciyar da wannan buri naka gaba ba.

Ba zai hana ka jin yunwa ba. Ba zai ba ka wani bayani da kila zai ceci rayuwarka ba. Ba kuma lalle idan kai namiji ba ne ya kara maka farin jini a wurin mata, in kuma mace ce ba na jin zai sa maza su kara sonki ba.

Amma kuma duk da haka, idan da zan ce zan koya maka wani darasi mai dimbin amfani da muhimmanci a game da tunaninka na kuruciya, ina fatan za ka cigaba da karantawa, ba domin komai ba sai don ka kara sanin abubuwa.

To menene a kwakwalwarka da zai rika angiza ka ka ji lalle kai kana son jin wannan bayani, ma'ana sai ka ji kwakwaf?

Mu mutane hali da kuma dabi'armu ce son jin kwakwaf, kuma yawancin lokaci ba a kan wani abu ba ne face, 'yan kanana-kananan abubuwa ne game da rayuwarmu mu ke zakuwa mu ji komai.

Wannan son ji da ganin kwakwaf shi ya karkatar da mu mu ke mayar da hankalinmu kan yin abubuwan da ba su da amfani kamar karanta labaran da suka shafi mutanen da ba za mu taba hadu da su ba, da koyon ilimin abubuwan da ba za mu taba amfani da su ba, ko ziyarar bincike da duba wuraren da ba za mu kara taba komawa ba.

Mu kawai muna son sanin amsoshi kan abubuwa ko da kuwa a zahiri sanin wannan ilimi ba shi da wani amfani.

Idan muka duba wannan abu ta fannin sauyin halitta za mu ga wani abu ne kawai da ya fi karfin sanin mutum.

Muna danganta sauyin halitta da tsarin rayuwa na gafiya tsira da na bakinki ko kuma kowa ta shi ta fishshe shi, wanda ke taimaka wa jigon rayuwa ta yau da kullum da kuma hayayyafa.

To tun da haka abin ya ke me ya sa mu ke bata lokaci mai tarin yawa. Da ba tsarin sauyin halitta sai ya zabi halittar da ta fi mayar da hankanlinta wuri guda ba (maimakon mutum da ke kame-kame)?

Wasan yara;

Tushen wannan dabi'a tamu ta daban ta son sanin kwakwaf za a iya cewa ya samo asali ne daga wani yanayi na bunkasar jikin dan adam, inda jikin babban mutum ya ke kasancewa da wasu alamu na kin girma, ya zama kamar na yaro matashi.

Bisa wannan fahimta mutum jinsi ne da ke kamar yaro ba kamar sauran dabbobi masu haihuwa da shayar da 'ya'yansu nono ba.

Rashin gashi a jiki kamar sauran dabbobi masu shayarwar, na daya daga cikin wannan alama ta zahiri.

Girman kwakwalwar mutum idan aka kwatanta da girman jikinsa wannan ma na daga ciki alamu.

Haka kuma wannan dabi'a tamu ta son sanin kwakwaf kan abubuwa, wadda ke tare da mu duk tsawon rayuwarmu da kuma son wasanmu alamu ne na dabi'a na wannan yanayi na rashin bunkasa ko girman jikin mutum( ya cigaba da zama kamar yaro matashi) duk da ya girma.

Wannan yanayi na rashin bunkasa ko girman mutum kamar yadda ya kamata, wata gajeruwar hanya ce da sauyin halitta ya biyo.

Wannan kuwa hanya ce dda ke kawo tarin sauye-sauye a lokaci daya, maimakon zabarsu daya bayan daya.

Wannan tsari ko hanya da sauyin halitta (evolution) ya dauka na sanyawa mu zama halitta

da ta fi kusanci da matasa ya sa mun zama masu rauni ba kamar danginmu birai ba.

To amma hakan shi kuma ya ba mu yanayi na son sanin kwakwaf kamar yadda yara su ke, da yadda mu ke iya koyon abubuwa da kuma kaunar zamantakewa tare da juna.

Kuma mafi muhimmancin amfanin wannan matsala ta rashin bunkasar jiki ( neoteny), shi ne yadda mu ke iya koyon ilimi a duk tsawon rayuwarmu, wannan ba shakka ya taimaka mana.

Wannan tsawaita rayuwa ta matashi da tsarin ke yi wa jinsin mutum, na nufin za mu iya samun abubuwa da yawa daga muhallinmu, abin da ya hada da al'adarmu ta gaba daya.

Hatta idan mun girma, mu kan iya koyon wasu sabbin abubuwa da sabbin hanyoyin tunani, wanda hakan ke ba mu damar sauya tsarin rayuwarmu ya dace da wani sabon yanayi na daban.

A duniyar basira ta na'urori masana ilimin kwamfuta sun duba yadda a ke samun dabi'a idan suka samu jagoranci na hanyoyi daban-daban na koyo.

Sakamako mai muhimmanci a nan shi ne hatta hanyoyin da suka fi duk wasu hanyoyi na koyo, su kan kasa idan ba a kara musu kwarin gwiwa kan su dan kar neman ilimi.

Ba tare da samun wani dan abu da zai karkatar musu da hankali daga abin da ya kamata su kasance suna yi, su kansu wadannan hanyoyin koyo su kan kafe su kasa ci gaba, su dogara a kan abubuwan da suka saba ko da yaushe, ba wani sauyi.

Masana fasahar kwamfuta sun fahimci amfanin da ke tattare da bunkasa wadannan hanyoyin koyon abubuwa, wanda shi ne ladan jarraba wani abu sabo daga wanda ka saba da shi.

Ta wannan su kansu hanyoyin koyon daga lokaci zuwa lokaci su kan kauce daga hanyoyin da suka saba bi su jarraba wasu.

Wannan kasada ta jarraba wani sabon abu da su ke dan yi na sa su rasa wata dama, amma kuma a can gaba su kan ga amfanin da ke tattare da kasadar, domin suna samun karin ilimi game da abin da za su iya yi a gaba, ko da ba abin da zai amfane su ba ne nan take.

Illar sauyin halittar kwakwalwarmu a fili ta ke. Neman sanin kwakwaf shi ne ribar bincike wanda halitta ke tattare da shi.

Mun sauya a tsarin yadda rayuwarmu ta ke ta yadda za mu kaucewa hanyar da muka saba bi, domin jarraba wasu sabbin abubuwa, hankalinmu ya dauke kuma gaba daya ma mu ga kamar muna bata lokaci ne.

Kila muna bata lokacin ne yau, amma hanyoyin koyon da ke kwakwalwarmu sun san cewa abin da muka koya bisa katari a yau zai zama mai amfani a wurinmu gobe.

Ba shakka zai fi dacewa idn mun san abin da mu ke bukatar mu sani, kuma mu mayar da hankali a kan abin kawai.

To amma dadin shi ne, a duniyar da ta kunshi abubuwa iri daban-daban masu sarkakiya, abu ne da ba zai yuwu ba, ka san abin da zai iya kasancewa mai amfani a gaba.

Ba shakka zai fi kyau idan mun san abin da muke bukatar sani, kuma mu mayar da hankalinmu a kai sai dakuma a wannan duniya da muke ciki mai cike da abubuwa iri-iri abu ne mai wuya ka san abin da zai zamar maka mai amfani a gaba.

Hakan ma dai shi ne ya fi dacewa, domin in ba don haka ba, to da mun zama wata halitta mai hadarin gaske, wadda ke cikin wata damuwa ta rashin sabbin abubuwan yi.

Halittar da ba za ta taba so ta bace ko rasa hanya ba, kuma ba za ta taba jarraba abubuwa ta ga me zai faru ba.

Ko kuma kawai ta rinka yin abu domin ba wani abu da za ta yi, in ba wannan din ba.

Sauyin halitta ya zamar da mu na'urorin da suka fi neman sani da son ganin kwakwaf a duniya, kuma wadannan na'urorin neman sanin suna bukatar kyakkyawan tsarin neman sanin kwakwaf wanda zai taimaka mana cin moriyar wannan dama ta koyo.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why are we so curious?